Al-Ajab

Malamin Addinin Kirista ya yi lalata da mata biyu ‘yan gida daya

Malamin Addinin Kirista ya yi lalata da yara mata 2 yan gida daya

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, ta tabbatar da cafke malamin coci mai shekaru 30, Joseph Ogundeji, wanda ake zarginsa da aikata lakata da wasu ‘yan mata biyu yan gida daya a Ajuwon da ke karamar hukumar Ifo a jihar.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Talata a Ota, Ogun.

 

Abimbola ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan karbar korafi daga wajen mahaifin yaran biyu da ya kai a hedikwatar ysn sanda ta Ajuwon, inda ya ce ya gano cewa daya daga cikin ‘ya’yansa mai shekara 16 tana dauke da juna biyu.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button