Uncategorized

SALON SO BOOK 1 PAGE5-6

 ????????????????????????????????????????            ???? SALON SO ????

????????????????????????????????????????

    BOOK ONE ????

Story & written by

Mommyn fareesa

 Masu buk’atar siyan paid books nawa serious sumin mgn ta 08100084251

Dedicate to all my commenters????????????????

   ????️5&6

*wacece anty amarya*?

 samira shine cikakken sunanta”iyayenta duk suna anan kaduna”bazawarace datayi 15 yrs tana zawarci”tafito dg gidan mijinta da yara 2″

      samira batada tarbiyya ko kad’an,akwaita dason abin duniya da yawace yawace”anan wata rana taga alh mukhtar anyi fira dashi agidan TV”taji tana mugun son ta auresa kodan tadama itada yaranta”aikuwa taje tadinga yawo bata nan bata nan”saida tabawa maza kusan3 kanta sannan tasamu ganinsa”bayan tashafa turaren da boka yabata”yace idan har yashak’a mgn ta k’are zai sota ya aureta..

Hakan kuwa yafaru”acikin sati 2 gaba d’aya dangin samira sun canza”musammun yaranta da uwarta”

dukda wasu sun kawo zugarta agun alh mukhtar “amma asirin data masa yasaka be yarda ba”

“Aymaan saurayine d’an kimanin shekara 24″zakiyya nada 19 yrs”dg aymaan har zakiyyar kowa barikin sa yakeyi…

Wannan kenan

mr Aliyu kuwa ya k’udurta aransa muddin zakiyya da aymaan agidan zasu zauna bazai lamunci rashin tarbiya da iskanciba”tsab zaiyiwa daddy mgn kokuwa yad’auki imaan subar masa gidansa”

da wannan tunanin ya saka key ya bud’e k’ofar parlourn sa”yakalli dining table”yahango abincin da imaan ta jera”

murmushi yakubce masa”afili yace”.my sweet baby kenan”Allah yasa girkin yyi dad’i to”

fatana Allah yabaki mijin k’warai yarik’e ki amana”ba kowa  zan iya bawa aurenki ba imaan”yafad’a yana rufe k’ofar yawuce bed room d’in sa”

kayan jikin sa yarage yad’aura towel iya k’ugunsa ya wuce bathroom….

Ahankali yashigo cikin parlourn yana sanye da suit farare k’al”yanata zuba k’amshi”yaja kujera yazauna”

Dambun shinkafa ne dayaji coslow”ga miyan kifi ga zob’o drink”sai farfesun kayan ciki”kasancewar imaan tasan yanason kayan ciki sosai….yanata murmushi yazuba komai”kafin yyi bisimillah anutse yafara cin abincin…bbu laifi girkin yamasa dad’i sosai”

saida yyi kat”kafin yagoge bakinsa da tissue da hannayensa”

Fitowa yyi dg sashensu”zakiyya na zaune kan kujera tana zubawa masu aiki masifa da mulki”kallo basu isheshiba yarab’a su ya wuce….

  ****************

yasmeen nabarin gurin ta wuce anguwar kawo”cike da fargaba da damuwa”sbd batasan meye zata sanarwa umman taba akan aiken data mata”

Tana shiga gidansu tun asoro” tafara jin kukan Ahmed”tasan kukan yunwa yakeyi”

sallama tayi”matar dasuke haya da ummanta ta amsa mata”d’akin umman su ta nufa”

tana k’okarin d’aga labulen d’akin”taji muryar umma nacewa” indai kin yaba da tarbiyyarsa ni wlh banida damuwa”sbd nasan baba me kuka bazaki cucemuba”kinsan rayuwa ta canza”wlh bana k’wadayi”gara mutuncin y’ata akan nasamu wani abu”ni ko aikin na shekara 1 tamasa”abinda tasamu nakama wata sana’a”har Allah yabata miji tayi aure”

Baba me kuka tace”.wlh salame”nayaba da mutuncin yaron nan “najima agidan su ina aiki kusan shekara 20″d’an arzik’i ne”Inda kamar ma ace matar ubansace tace”.na nemo masa mai aiki”gsky bazan miki mgn ba”sannan kuma na yaba da tarbiyar y’ar ki”kuma ina tausaya muku halin dakuke ciki”musammun sbd yaron nan Ahmed dakeda sicler”ajiyar zuciya yasmeen tasaki tana yin sallama ta shigo cikin d’akin”gaisheda baba me kuka tayi”umma tace”.yaya ake ciki?umma wlh kiyi hak’uri matar nan tace”.batason aikin nan tasallameki….shikenan babu komai yasmeen”gama aiki har gida baba me kuka tasarmiki”insha Allah baza muyi nadama ba”

Baba me kuka tace”.insha Allah”yanzun ma zanje nasanar masa yafidda rana kifara zuwa”

Aikin dazaki masa shine” share share da goge goge”kizo tun 8 nasafe”sai 10 yake tafiya office”amma nasanar masa kina islamiya k’arfe 4″gaban yasmeen na fad’uwa ta amsa dato”sbd itadai harga Allah”komai wahalar aiki zatayi”indai za’a sami kud’in dazasu siyi abinci akuma siyawa Ahmed magani”

saidai ayadda ta fahimta kamar namiji zata yiwa aikin”

Umma nak’ok’arin mgn Ahmed yashigo cikin d’akin yana kukan yunwa”

baba me kuka takamashi ta zaunar agefenta”ta fito da 500 cikin albashinta 10k da aka bata ayau tace”.asiya mishi wani abu”umma tace” haba baba me kuka”gsky bazamu amsar miki kud’i ba kibarsu dan Allah”salame ba rok’ona kuka yiba”kibar mishi dan Allah indai na isa”bbu kyau maida hannun kyauta baya”godiya sosai umma ta mata”kafin baba me kuka tace”.insha Allah yadda mukayi da safe zanzo nasanar miki insha Allah”godiya sosai umma tayiwa baba me kuka sukayi sallama ta fice”

yasmeen na kallon Ahmed tace”.tokai kawo kud’in nan”asiyo garin kwaki da k’uli k’uli tunda munada sauran mai”

Umma tace kisiyo sabilin wanki da klin amusu wanki”asma’u ta jido mana ruwa d’azun”dato yasmeen ta amsa ta amshi kud’in ta fita…..

Wacece yasmeen?

Bilkisu Abdallahi shine cikakken sunanta”(ana kiranta yasmeen sbd sunan mahaifiyar babanta)yasmeen yarinya ce y’ar kimanin shekara 19_20″wankan tarwad’ace ita”itaba doguwaba bakuma gajeraba”tanada k’ira me kyau”musammun kirjinta”tanada beauty point”ga round face”tanada wushirya ,da idan tayi dariya take bayyana atsakkiyar hak’oranta”yasmeen nada ilimin adini sosai”awannan year d’in ta kammala NCE d’inta”mahaifin bilkisu da ummanta y’an asalin garin nan ne”shekarar mahaifinta 7 da rasuwa”su 3 ne agun iyayensu”yasmeen ,sai Asma y’ar 12 yrs”sai auta Ahmed 8 yrs”wanda keda ciwon sicler”yaron nashan wahala sosai idan ciwon yatashi”sannan ba k’ananun kud’ad’e ake cazarsuba akan magani…hakan yasa baffa d’ahiru”( yayan mahaifinta)gaba d’aya yyi baya dasu bai taimaka musu”dama shine mai d’an k’arfi adangin ubansu”gashi mahaifiyar ubansu ta tarasu itama”sannan yabuk’aci ya auri umma”amma tak’i yarda…umma keta wahala da fad’i tashi akansu”kwata kwata shekarun umma basu wuce 38 amma idan kaganta zaka yi zaton y’ar 30 yrs sbd tanada kyan jiki”tayi k’osai,tayi markad’e “duk akan yaranta”amma lokaci guda ciwon Ahmed yacinye komai harda gidan dasuke zaune”hakan yasa suka kama haya”sbd itama danginta talakawane”

Lokacin da yasmeen ta cika 18 yrs”kyawunta yagama bayyana”atime d’in kuma baba d’ahiru yazo har gida yasanarwa umma data kammala karatun ta zai hadata aure da d’an sa sanusi”yaron da beda tarbiyya da kamun kai”sai sace sace da shaye shaye….umma ta nuna masa hakan bazai tab’a faruwa ba…

      shikuma yanuna mata yana akan bakansa”ga sanusi yayita zuwa yanayiwa yasmeen maganganun banza”hakan yasa suka tashi dg unguwar mu’azu suka koma kawo….ayanzun haka basusan anguwar dasu yasmeen suka komaba….

yasmeen yarinya ce nutsatstsiya”bata son raini da wulak’anci”kuma bata raina kowa”hakan yasa bata cika yawon k’awaye ba”k’awayenta 2 data shak’u dasu”rukky da teema”samari da yawa nacewa suna sonta amma bata kulasu”batafi wata 5 da kammala karatuntaba”mahaifiyarsu nayin aikatau awani gida”kasancewar Ahmed ciwonsa yatashi”kusan kwana 10 bata jeba”kuma gidan akwai samari maza marasa tarbiyya “hakan yasa tak’i ta tura y’arta”

       Baba me kuka mak’otansune suna gaisawar mutunci da umma”kuma tasan halin dasuke ciki”hakan yasa mr Aliyu namata mgn taga bbu wacce ta dace irin yasmeen”sbd hankalinta da nutsuwarta..

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button