MATAR UBA 14

Murmushi yayi Kan yace “Ko dai zargin matar ka kake”
“Eh to kusan hakan dai, sabida abin yayi yawa gaskiya”
” Maybe tana chat da qawayen ta ne”
” Kawaye har ukun dare? Kai bazaiyu ba”
“yanzu abinda za’a yi na iya tracking zamu ga dukkanin abinda take yi zan duba maka,Amma fa kamin alkawarin duk abinda muka gani baza ka sake ta ba, sabida bana so na Zama sanadiyar mutuwar auren ka”
” Na amince”
” To Shikenan insha Allah Zan duba maka”
“To na gode Abokina.”
Cikin dare ya yi tracking yaga irin chat d’in da Nana takeyi, hankalin sa yayi mugun Tashi, sabida bai tab’a ganin shaid’aniyar mace irin ta ba, yanzu ya rasa abinda zaicewa Abokin nasa shin ya fad’a Masa ne ko Kuma don babu Wanda zai ga irin wannan kazantar ya cigaba da Zama da ita, don ko shine yaga hakan bazai Bari ba.
*NEXT DAY*
Abban Yesmin ne ya shigo d’akin Abokin nasa, “Abokina ya akayi kasan jiya kasa bacci nayi shin ka duba min ne ko Kuma,wallahi da abin na kwan a raina.”
Kallon sa kawai yayi kana ya kau da Kai yace
“Na duba”
“Uhmnn ina sauraron ka”
“Yaushe rabon ka da zuwa gida?”
“Eh to na Kai watanni shida ban je ba”
Murmushin takaici yayi yace ” Ko kad’an ban ga laifin Nana ba Kaine ka cutar da matar ka lalata Mata Rayuwa”
” Kamarya Kenan ban fahimce ka ba?”
Gyara Zama yayi Kan yace ” Ka saurareni da kunnen basira”
Yace “Kai nake sauraro”
????????????????????????????????
Kakakara Kaka,yau akeyinta, fansa yakuje ganin zata kasance shin Kuna ganin idan ya rufa Mata asiri yayi dai dai,ko Kuma ya fad’a Masa don Kar ya cutar da Abokin Sa?
Ina jiran amsoshi da comments d’inku
*MILHAAT CE YAR TERAWA*
PLEASE COMMENT AND SHARE
[ad_2]