RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 1 to 10

Ad

_____

Alarm ɗin da tasaita ƙarfe 09:00pm. Yatashe ta daga barcin da take yi, a hankali tayaye bargon da tarufe jikin ta har kanta dashi tasoma miƙa tana hamma, ɗakin gaba ɗaya duhu ne don ba’a ganin komi, miƙewa zaune tayi ta jima ahaka har magagin barcin da take yi yasake ta kafin tazuro ƙafafun ta tasauko daga gadon tanufi wajen makunnin ɗakin takunna wuta, haske ne yamamaye gaba ɗaya ɗakin da yatsaru iya tsaruwa, komi na ɗakin Sky Green ne, takowa tayi ta’isa gaban gadon tana sake zama, hannu tasanya tadafe goshin ta na tsawon mintuna 3 kafin tasoma tattare gashin kanta da yake abaje har zuwa kafaɗun ta taɗaure da jelan gashin, miƙewa tayi tasoma cire kayan barcin jikin ta sannan taɗaura towel tashige toilet, tana shiga tasakarwa kanta shower, sai da tadaɗe tana jiƙa ƙanta daga sama har ƙasa kafin tasoma wankan, acikin mintuna 15 tagama taɗauro showel tafito, a gaban dressing mirror tazauna tasoma tsane kanta, sai kuma taɗau handrayer tafara busar da gashin ta, tanayi tana lumshe manyan idanuwanta har sanda tagama tasoma shafa Expensive lotions ɗin ta, bayan ta gama powder kawai tasanya a kyakykyawar face ɗinta tashafa lipstick💄a ƙananun laɓɓan ta, kana tamiƙe tanufi Sif ɗin kayan ta tasoma zaɓo kayan da zata saka, riga ne ja me gajeren hannu tasaka ajikin ta wanda yatsaya mata iya cibiyan ta, sai tasaka dogon wando pencil da yayi matuƙar matseta yafito da halittan ta, Hill shoes tasaka red colour me igiya sannan takoma gaban madubi tasoma tattare gashinta tana sake gyarawa tare da shafa mayuka masu matuƙar saka gashi ƙyalli, sannan tafeshe jikinta da perfomer’s masu ƙamshin daɗi da sanyi, ƙaton Ribom tasaka green colour takama gashin sannan tanufi inda take rataye Wizy Bags ɗin ta taɗauko ɗaya tadawo gaban gadon ta tabuɗe drower takwashi kuɗi masu yawa tazuba a jakan, wayan ta dake ajiye saman drower ɗin taɗauka shima tasaka a jaka kafin taɗau car key tataka tafice, tana fitowa tasauka dawnstair, bata damu da duhun da yamamaye ko ina ba, haka tafice a parlour’n tanufi Compound ɗin gidan, motarta tabuɗe tashiga tafice a gidan da mugun gudu, kasancewar dare yasoma yi motoci sun soma ɗauke ƙafa haka tayi ta tsula gudu kamar zata tashi sama ko tsoro bata ji, wayan ta da yasoma ringing tamiƙa hannu taciro cikin jaka tana peacking call ɗin takara a kunne, kafin tayi magana Ramcy ta riga ta dacewa”Wai Babe kina Ina ne naji ki shiru har yanzu?”.

Cikin siririyan muryan ta me sanyi tace “ga ninan zuwa”.

“Ok sai kin zo”. Cewar Ramcy tana katse kiran

Ajiye wayan kawai tayi taƙara speed, tana tuƙin ne cike da gwaninta har Allah yasa takawo ƙofar gidan su Ramcy ƙawarta, Ramcy dake bakin ƙofar gidan su a tsaye tanufo motan tabuɗe tashige, ita kuma taja sukaci gaba da tafiya, kallon ta Ramcy tayi tana murmushi tace

“Kinyi kyau Babe”.

“Thanks”. Ta’amsa mata ataƙaice

Daga haka basu sake magana ba har suka iso gaban wani kyakkyawan Club, fitowa sukayi cikin motan bayan tayi parcking motan aciki, atare suka jera sukayi cikin Club ɗin

Sosai ciki yacika da mutane maza da mata kowa na harkan gaban shi, an saka music wasu na ta faman cashewa, suna shiga Direct RAUDHA wajen masu rawa tanufa tashige cikin su tasoma kaɗa jiki tana rawa me ban sha’awa, dama abinda ke kawo ta Club kenan RAWA, tana ƙaunar rawa a rayuwan ta, koda tana cikin damuwa ne idan har zataji kiɗa na tashi to fa sai zuciyarta tayi mata sanyi, haka tayi ta cashewa tana rausaya jiki kamar zata karye, dama ba wani auki ne da ita ba, ita kuwa Ramcy ba gwanar rawan bace, zuwa tayi tazauna cikin wasu maza tasoma kora sheesha tana yi tana kaɗa kai

RAUDHA rawa yayi rawa sai zuba ihu take yi tana dariya tana tiƙan rawa, sai da tagaji sosai kafin tayo wajen Ramcy tazauna tana waftan Sheeshan hannun ta tasoma sha tana fesarwa ta hanci ta baki cike da ƙwarewa, mazan wajen duk kallon ta suke yi suna dariya, yayinda ɗaya daga ciki yasoma mata kirari yana faman koɗa mata kai, ita kuwa sai faman bankan sheesha take yi tanayi tana shaƙan Coken, Ramcy tashi tayi tanufi wajen wani saurayi dake can zaune tare da ƴan mata, magana sukayi sannan yamiƙo mata wasu ƙwayoyi da bansan ko menene ba, amsa tayi tanufi wajen Receptionist tayi odan Juice tadawo, kallon ta kawai RAUDHA take yi har tazauna kana tamiƙa mata hannu, ita kuma tabata Cup ɗaya bayan da tasaka mata ƙwayoyin ciki, amsa kawai tayi tasoma korawa tana jin ta asama, zuwa lokacin tasoma kai ƙololuwan bugawa, don daƙyar take iya buɗe kyawawan idanuwanta tana kallon mutane, sai da tashanye gaba ɗaya tasaki Cup ɗin Ramcy tayi saurin tarewa

Lumshe idanu tasoma yi tana buɗewa daƙyar, cikin tsananin maye take cewa “ahh.. ahhm Rammmm.. Rammcyyyy ƙaro min..”

Ad

Bata iya ƙarisa maganar ba ma sai shiru tayi tana ci gaba da zuƙan Sheeshan tana fesarwa ta cikin hancin ta, Ramcy itama da tagama buguwa tashi tayi takoma tasake yin musu odan wani Juice ɗin tadawo, zuba musu ƙwayan tayi suka ci gaba da sha, yayinda su kuma mazan nan sai harkan gaban su suke yi, daga ƙarshe ma tashi sukayi ɗaya bayan ɗaya suna barin wajen, yayinda wasu suka wuce wajen ƴan matan su, wasu kuma sukayi gida don alokacin dare yayi sosai

Ad

_____

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button