MATAR UBA 18

Da sauri tabi bayan sa,Dr ya d’aura masifar daga inda ya tsaya.
*Hashim* tunda ya koma yake zaman jiran ganin Kiran ta Amma shiru kake ji,Yana kwance kwasam wurin karfe Tara na dare yaji Karan wayarsa take jikin chaji da saurin gaske ya tashi ganin *Badiyya* ya bayyana a screen d’in wayar sa yayi tsaki ya koma ya kwanta a haka bacci yayi awon gaba dashi.
Wayar hannun ta take kallo Tace “Dan Allah Hashim ka d’aga Kiran Nan I need you” Maida kallonta tayi ga Asiyah dake sharar baccin ta.
Safiya na kwance chat d’in ta take babu abinda ya Sha kanta a fili Tace “Ni zaka rainawa wayo nasan kana Nan kana jiran kirana Ni Kuma ba Kiran ka zanyi ba sai Nan da kwana biyu” da wannan tunanin tayi bacci.
*WASHE GARI*
Da sassafe ta shirya driver ya kaita makaranta don gudun Kar Hashim ya biyo ta, hakan kuwa akayi,tana barin gidan Hashim yazo yayi parking har karfe takwas tayi bai ganta ba hakan yasa ya koma gida.
*ASIBITI*
Dr Badiyya duk kwanan duniya sai to duba Baba Mai gadi don ganin ko ya tashi Jin irin alluran da akayi Masa Tace sai ta sa an kori nurse d’in da tayi hakan.
Badiyya Tace “Asiyah Zaki iya wanka da Kanki? Ko na Miki?”
Kunyar maganar taji Kai kawaii ta d’aga, Badiyya Tace “Zaki iya?”
Ta amsa da “Eh” Murmushi tayi tace baza ki iya ba,Sabi da Baki Saba ba,San Miki Ina so ki saki jikin ki Nima mace ce kamar ki,tunda lalura ce ba matsala Ni zan Rika Miki kinji?”
” Toh Aunty Amma aikin ki fa?”
Murmushi tayi Tace ” Yau Ina break sai gobe” da taimakon Dr Badiyya Asiyah tayi wanka sannan ta d’auko Kaya daka cikin kayan da ta kawo Mata.
????????????????????????????????
PLEASE VOTE AND COMMENT
[ad_2]