Uncategorized

MATAR UBA 20

Murmushin takaici yayi yace “Ni kaina abun na bani mamaki Faisal,Amma ya zanyi Ina son Asiyah Ina so na San a wani hali take ciki Dole nayi yadda take so”

” Kasan mene ne, hashim? Duk yanda za’a yi ka nuna Mata ita d’in kake so kayi ka nuna Mata baka son Asiyah,Dole game zamu buga kamar yadda take so”

” Kamar ya Kenan fa ban fahimce ba”

” Abin nufi zaka tura gidan su,ayi komai da komai, Kan ranar auren Kai ma ka nuna Mata in dai Bata fad’a maka inda Asiya take ba zaka fasa by then Bata da option Dole ta fad’a maka sabida kaga a wannan lokacin lokaci ya kure Mata sun gayyaci Yan uwa da abokanan arziqi babu yadda zatayi Dole ta fad’a maka idan ka tabbatar da hakan ka ganta sai ka fasa”

Murmushi Hashim yayi Wanda shi kansa ya manta ranar da yayi yace ” hakan za’a yi Abokina nagode sosai”

” Kar ka damu yanzu ka tashi Muje masallaci Naga Ana Kiran sallah daga Nan sai mu wuce gidan nasu.”

Hakan kuwa akayi suna idar da sallan Kai tsaye suka wuce gidan su Safiyya horn sukayi aka bud’e musu gate dake ta sanar da sabon Mai gadin da zuwan su, tana Jin horn ta tashi jiki na rawa da niyar zata fita.

A tsawace Baraka Tace “And where are you going to?”

Murmushi tayi Tace “Mummy bako nayi”

Cikin rashin fahimta Tace “bako? Daga Ina?”

Murmushi tayi Tace “Mummy kiyi hakuri idan na dawo zan fad’a Miki komai.” Tana Kai Nan ta fita da sauri.

Baraka na kiranta Amma Bata juya ba bare ta ji me zata ce, kad’a Kai kawaii tayi ta cigaba da mugun Shirin ta.

Faisal yace “Kirata Mana”

“To ai bani da number ta”

“Kamarya baka da number ta dame kukayi waya?”

” Uhmn hiding number tayi”

Kama Baki Faisal yayi yace ” Lallai yarinyar Nan ta wuce tunani na,Allah ya kyauta.”

Ya amsa da “ameen, Bari na aiki Mai gadin ya Mata magana kawai” har ya sauke kafa d’aya sai ya hango ta ya waiga ya kalli Faisal yace “gata chan ma tana zuwa”

Da sallama ta Kara so inda suke, da Murmushi d’auke a fuskarta ganin su biyu ne sai taji wani iri,Tace ” Sannun ku da zuwa”

A tare suka amsa da “yauwa sannu” 

“bismillah ku Zo mu Shiga ciki”

Babu wanda yace Mata komai,kawaii fita sukayi suka bi bayanta, Faisal murya kasa kasa yace “Mutumina yarinyar Nan fa karshe ne gun kyau wallahi ta had’u”

Hararar da Hashim ya Masa ne yasa yayi saurin Kay da kansa.

Maganar da yayi ya sauka Akan kunnen Safiyya Aiko tana jin hakan ta canza tafiya sai yauki take,a parlor da ake saukan bakin ta ajiye su, Yar aikin gida tasa ta kawo musu drinks, Faisal ya sa hannu ya d’auki exotic ya Fara Sha,gyaran murya hashim yayi yace “Abokina kaga gimbiyar tawa ko?”

Murmushi Faisal yayi Yana kokarin had’iye exotic da ya cika bakinsa da shi don dama shi masoyin exotic ne, sai da ya had’iye yace “Na ganta Abokina tabarakallah Masha Allah,sannu Amaryar mu.”

Safiyya wani irin dadi taji rufw fuska tayi da hannu biyu Tace “yauwa sannu abokin mu,da fatan kana lafiya?”

“Lafiya lau,ya gida yasu hajiya?”

” Suna lafiya Lau”

” Masha Allahu.”

Hashim gyara zaman sa yayi yace ” My princess gani nazo,ya ake ciki?”

Cikin muryar shagwab’a Tace ” So nake cikin satin Nan kazo neman aure na”

Murmushi yayi yace “shine kawaii?”

Ta d’aga Kai alamun “eh”

Murmushi irin na Zaki Raina Kanki yayi yace “Consider ita My Sofiyat”

“Wow Amma naji dad’in sunan Nan”

” Dan Allah dagaske kike?”

” Eh dagaske nake har cikin Raina naji shi”

” To in ko Haka ne yanzu Kika Fara Jin dad’i don yanzu na Fara kirin ki da sunaye masu dad’i”

Murmushi tayi tace “Nagode sosai,Allah ya bar mu tare”

Ya amsa da Amin Amma a iya baki ya tsaya.

ASIBITI

“Asiyah inaso ki kwantar da hankalin ki ki saurare ni,Kuma ki fahimce Ni kinji?” Dr Badiyya ke maganar Nan cike da tausayin Asiya, Asiyah ta amsa da “Toh Aunty Ina sauraron ki”

“Baba Mai gadi Yana Asibitin Nan”

Tashi tayi ta zauna tana Murmushi Tace ” Baba ya dawo Alhamdulillah, ina yake?”

Nan ta fad’a Mata tun ranar da aka kwantar dashi Bai tashi ba,bare ma aji ya samu aunty Rukayya ko Bai same ta ba.

Kuka ta Shiga tana fad’in “Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un, Ya Allah me nayi me nayi da chanchanci irin wannan laifin, Allah na tuba ka yafe min”

Dr Badiyya rungumarta tayi Tace ” Ki daina fad’in haka Zaki yi sabo Allah ya na gwada bayin sa ne Wanda take so,ki d’auki wannan a matsayin kaddarar rayuwar ki,insha Allah komai zai wuce Allah ya Baki ikon cin jarrabawar nan, kiyi hakuri Asiyah Dole ki bar asibitin nan don na tabbata zasu Kore ki yanzun ma nice ma roka aka barki Kuma private hospital ne”

Fashewa tayi da kuka Tace ” Na Shiga uku Ni yanzu Ina zan je,idan na koma gidan mu kashe Ni zasuyi”

“Ki daina kuka Asiya baza ki Koma gidan Nan ba, nayiwa Mahaifina maganar ki,Kuma ya amince ki dawo gidan mu da Zama kamun a samu mafita”

Godiya ta Mata sosai,da yamma suka wuce gidan su Dr Badiyya,Amma kamun Nan sai da ta biya d’akin da baba Mai gadi yake,gidan nasu Ba wani babba bane Kuma ba masu kud’i bane ba kawai dai sun da rufin asirine dai dai gwargwado.

“Nayi farin ciki sosai Nana hakan da kikayi ya tabbatar min da cewar kin tuba ne dagaske,idan shaid’aniyar Jan ta Kuma zuwa gidan nan ki sanar Dani nasan matakin da zan d’auka a kanta”

Ta amsa da to,kashe mata Ido yayi yace “Ya to mu haura sama na Baki sako” ya haura sama abunsa

Murmushi tayi dake ta gane abinda gogan nata ke nufi sai ta mara Masa baya,Niko da na leka Naga abinda yaso yafi karfin idona na jawo musu kofar nayi gaba.

Hira suka Sha sosai kamar dama tun chan Yana Sona ta,karfe Tara saura suka you Sallama suka wuce, Faisal yace “Abokina ban San haka kake ba Ashe zaka iya yaudara jibi yadda ka sake kamar dagaske kana sonta”

Murmushi yayi yace ” Toh idan ban yi hakan ba bazan samu abinda nake so ba, I’ll do whatever it takes to make Asiyah mine,sabida Ina sonta Ina Kuma kaunara ta”

“Allah ya tabbatar Mana da Alhairi yanzu ya maganar turowan?”

“ai yanzu ba anjima ba muna Isa zan sanarwa hajiya ta Kar a b’ata lokaci gurin wannan abun”

“Hakane ka dai bi hankali yarinyar Nan abin tsoro ce”

” Toh insha Allah,zan kiyaye” gidan su Faisal suka biye ya ajiye shi kama ya wuce gidan su,Yana zuwa ya samu hajiya na parlor tana kallon film,a gefen ta ya zauna,bayan ya gaishe ta bai sake cewa komai ba,kallon sa tayi Tace “Son Dan Allah ka fad’a min me yake damin ka,idan baka fad’a min matsalar ka ba wa zaka fad’awa?”

Riko hannun ta yayi yasa shi a cikin nata Yana d’an Wasa dashi yace “Mom,aure nake so”

‘dan zaro Ido tayi Tace “Aure son a Yanzu?”

“Eh Kuma so nake a cikin satin Nan aje a nema min auren”

Zare hannun ta tayi tace ” bazaiyu ba Hashim,kasan kana son aure Kuma kaki karb’an aiki? Yanzu Haka company ya daina tafiya yanda ya kamata ka sani mahifin ka ya tura ka kasar waje kayi karatu be don ka rike kamfanin bayan ransa ba zaman kashe wando ba daga Nan zuwa chan ba,idan kaga kayi aure to ka Zama cikakken mutum ne akasin haka Kuma to wallahi ba da yawuna ba.”

Tana Kai nan ta bar gun ta barshi bakina bud’e Yana mamakin yanda ta d’auki maganar da zafi haka,Kiran Faisal yayi ya Sanar Masa Yanda sukayi da mom, Faisal yace “ai kaji Kuma Ana wata sai ga wata, Kai ma Hashim baka Jin shawara nasha fad’a maka ka koma company ka karb’i aikin Nan Amma ka bar bare akai yanzu wa gari ya waya?”

” Faisal na Kira ka ne ka ne don ka kwantar min da hankali ba ka kara min tashin hankali ba”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button