Uncategorized

MATAR UBA 23

Ad

_____

 💦💦💦💦💦💦💦💦     *MATAR UBA*

💦💦💦💦💦💦💦💦

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

                 *(MILHAAT)*

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

Ad

NOT EDITED

CHAPTER 23

“What’s wrong with me? What’s wrong me? You’re here kissing this thing and you’re here asking me what am I doing? tell me what you’re doing with him?”

Cikin rashin fahimta Tace ” What? Are you kidding me?”

💦💦💦💦💦💦💦💦

…….”Am I kidding you” magana yake ransa a mugun ‘bace idanunsa sun canza daga Farare zuwa jaa, ran Badiyya yayi matukar ‘baci Rai a d’an ‘bace Tace “Hashim Anya kana cikin hankalin ka kuwa?”

“Ke zan tambaya Badiyya, but is okay…. Is okay” Yana maganar Yana dariya had’e da kuka Yana d’aga kafad’a Yana Kai Nan yayi ficewar sa,duk gun kallon sa a ka tsaya yi, abokin Ammar ne ya d’auki mic yace “Please we are sorry,DJ ka samana kid’a” Nan suka cigaba da shashewar su, Badiyya Kan Ammar ta nufa ganin ya fasa baki sannan  gefen idon  sa  ya  kumbura  hakan ne yasa suka je clinic aka wanke Masa ciwin, banda sorry babu abinda take cewa masa ji take kamar taje ta Rama Masa a fad’in ta baida hujjan dukkan sa.

Hashim kai tsaye d’akin sa ya wuce zama yayi akan one sitter daje d’akin sa, d’an kwanciya yayi Yana kallon saman d’akin hawayene masu zafi suke sauko masa,da zarar ya rufe idanunsa Badiyya yake gani da Ammar, tsaki yayi yace “kin cuce Ni Badiyya,ki rasa Wanda Zaki kula sai Ammar har kiss?” A bayyane yake maganar.

“Hashim Kennan, kana matsala wallahi kishin ka yayi yawa yanzu Dan Allah me amfanin abinda kayi?”

‘dago idanunsa yayi don kallon Wanda yake magana d’an tsaki yayi ya ce “Look Farees baka ga abinda na gani ba ne Dole kace haka” 

“Hakane ni banga abinda ka gani ba….” Zama yayi a bakin gado Jana ya d’aura da fad’in “Babu yanda za a yi idanuna su gane min abinda ka gani,sabida kaga Ni da hankali na” 

Gyara Zama yayi yace “Okay idan na fahimce ka Farees kana nufin mahaukacine Ni bani da hankali ki”

‘yar karamar dariya yayi yace ” Kai kace hakan Ni bance maka mahaukaci ba,Amma me ma difference d’in ka da mahaukacin? Ka tsaya kana ta ihu akan rashin gaskiya,kace min kana da hankali?”

“Farees na roke ka Dan Allah ka kyale Ni naji da abinda yake damina”

Rai a ‘bace ya mike yace “anki a kyale ka Kai Kennan ba hali a fad’a maka gaskiya? Na Sha fad’a maka ba haka ake soyayya ba,Amma baka ji,nifa da idona Naga sanda da buge shi da hannun ta Bata sani ba, shiyasa take hura Masa ido”

A tsawace yace “Kar ka Raina min hankali Mana inga tana kissing d’insa kace min ba Haka ba”

“You see your life kaga shine illan tab’a jikin ta da kake yi,kana kissing d’inta ba Dole kayi zargin ta ba, me bakayi da ita, shaidar da zan maka d’ayane shine nasan bazaka yi Zina da ita ba but nasan babu abinda baka sani ba a jikin ta ba,Kuna ganin hakan waye wane” tsaki Mai tsawo ya jaaa ya fice, sai Kuma ya leko yace “Faisal ya Kiran yace Yana Kiran ka baya shiga idan ka gama haukan naka sai ka Kira shi” ya ja kofar ya rufe Masa yayi tafiyar sa.

Farees cousin brother d’in Faisal ne, hakan yasa Hashim Faisal da Farees suka zama abokai.

Tsaki Hashim yayi ya koma ya zauna Hashim kasa bacci yayi tunda ya zauna Bai tashi ba sai tsaka wa yake da warwara Yana kallon kofar d’akin a ganin sa Badiyya zata Zo ta Bashi hakuri kamar yadda ta Saba,Amma Bata Zo ba,Bai tashi a gun ba sai da lokacin sallah tayi bayan ya idar da sallah yace “Baza ta Zo ta bani hakuri ba Kenan Hmm,ko da yake ma hakurin me zata bani tunda tana son hakan?”

Badiyya ma hakan take ba tayi bacci ba sai kallon wayar ta take ko zai kirata ya Bata hakuri Amma shiru kake a fili Tace “Wato bazai Kiran ba Kenan bayan yasan yayi laifi a tunanin sa zan je na Bashi hakuri ko? To wannan karon Kan karyan ka Tasha Karya” ta cigaba da harkar gaban ta.

Projects d’insu suke kokarin had’awa hakan yasa makarantar busy, Yau kwanaki uku Kenan Badiyya Bata Zo inda yake ba Haka ma Hashim bai nema ta.

Department d’in su Badiyya ya shiga, Badiyya na ganin sa tayi Murmushi a zuciyar ta Tace “Nasan zaka dawo” ga mamakin ta sai taga ya wuce ta Baki a bud’e ta bishi da kallo, Hashim Sarai ya ganta Amma yayi kamar bai ganta ba, inda ya hango Farees ya nufa dake  course d’in badiyya da Farees d’aya.

Farees na ganin sa ya ‘bata Rai, hannu Hashim ya Mika Masa had’e da fad’in “Assalamu Alaikum”

Farees Mika Masa hannu yayi ya amsa chan ciki ba don ya so ba.

Zama Hashim yayi yace “Ina ka shiga ne haka two days ba a ganin ka?”

Farees yace ” Ni d’in kuwa?….. Ina Nan ba a dai neman ba” sai ganin Hashim yayi Farees ya Fara tattara takardun sa, cikin rashin fahimta Hashim yace “A’a Ina kuma zaka?”

“Bacci nake ji zanje na kwanta”

“Bacci Kuma to Muje man” ya tashi da niyar bin sa Farees yayi saurin fad’in “No thanks bakaji bacci nace ma zanyi ba?” Yana Kai Nan Bai tsaya Jin me Hashim zai ce ba ya bar gun. Hashim jikin sa sanyi yayi murmushin takaici yayi yace “To Allah ya kyauta.”

Badiyya na kallon su duk da bata Jin su ta gane akwai matsala, hakan yasa tayi ficewar ta, Hashim Zama yayi Yana kallo a wayar sa duk ji yake baya Jin Dadi,ba Masoyiyar sa Babu abokin sa,tsaki yayi sa wayar a jaka,ya fice.

Ad

_____

1 2 3 4Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button