MATAR UBA 24

Karfe takwas na yamma Badiyya ta riko hannun Asiyah suka fice daga asibitin, napep suka shiga tunda suka shiga babu Wanda ya sake magana, Asiyah Jin shirun tayi yawa tace “Aunty kina lafiya kuwa?”
“Lafiya lau,me Kika gani?”
“Ji nayi kinyi shiru kamar ba ke ba”
Murmushi tayi tace “Bakomai gajiya ce kawai tayi min yawa Baki ga yau ko Zama banyi munyi Hira ba?”
Tace “Hakane”
Federal low-cost suka nufa,suna Isa gida ta sallami mai napep suka shige gida, Momy suka Tarar a parlor bayan sun gaisheta ta musu sannu da zuwa suka shige d’aki, Badiyya ban d’aki ta fad’a tayi wanka kana ta riko hannun Asiyah har zata cire Mata Kaya,cike da Jin kunya Tace “Aunty zan iya wankan,kawai ki kunna min shower” Murmushi tayi,tayi yanda tace ba tare da Tace Mata komai ba,
Bayan ta fito suka koma parlor suka ci abinci, Badiyya abincin kawaii take ci bata Jin dadin sa, Momy da ta lura da alamu tana cikin damuwa bayan sun gama ta kirata d’akin ta,cikin kuka ta Sanar da ita dalilin da yasa Hashim ya fasa auren ta kana ta fad’a Mata matsayin Asiyah a gunta, Momy nasiha ta mata sosai Mai shiga jiki sannan ta jawo hankalin ta Akan Kar ta kuskura son zuciya yasa ta ki Asiya tace “Naga alama yau sai wani shashshareta kike yi,to wallahi kul Kar naji Kar na gani” wayarta ne ta Fara ringing, sunan Hashim ta gani Momy ta d’an leka tace “Ki d’ga mana”
Ji nayi Tace “To”
Momy tace “Ya akayi me yace?” Ganin yanda Badiyya ta b’ata Rai.
“cewa yayi na fito da Asiya”
“To Tashi kuje,ki saki ranki karki bari ya gane abinda ke ranki”
Tashi tayi ta fice, suna fita suka tarar Yana harabar gidan Murmushin takaici ci tayi tuno sanda yake zuwa gunta Hira tayi,a wannan tunanin suka karasa inda yake bayan sun gaisa yace “Maganar tafiyar mu India ne, na Mana passport”
Cikin rashin fahimta Tace ” Bangane ka Muku passport ba?kai dawa?”
” Ni da ke,da Asiyah,you know how caring I am idan ina son Abu”
Kai ta d’aga alamun eh,yace ” Asiyah ta,ya naji kinyi shiru ba magana ne?”
Murmushi kawaii tayi Tace ” Kawaii ina farin cikine da Jin dad’in yanda Kyle damuwa da lafiya ta, sannan naji dad’i da duk mu ukun zamuje”
Murmushi yayi yace “kin chanchanci fiye da haka My princess”
Wani irin kallo Badiyya tayi masa, murmushin gefen Baki yayi don yasan baza taji dadin hakan ba,a zuciyar sa yace “Ke ma kiji inda Dadi wani abun ma sai ta warke”
A fili Kuma yace ” Ni zan koma,karfe Bakwai na safe flight din mu zai Tashi zan Zo na d’auke ku karfe shida”
Kai kawaii ta d’aga Masa ta shige motar sa,leko wa yayi yace “Dan Allah ki Kularmin da My princess” key ya Danna ya fice.
Badiyya takaicin duniya ce ta ishe ta ta rasa yanda zatayi, rike hannunta tayi ta jaa ta suka shige gida.
Khamal ya d’auki aniyar d’aukar fansar abinda akayi was Sadeeq da ‘ya ‘yan sa,hakan yasa ya koma bakin aikin don samun Karin Hutu yayi sa’a ya samu hutun sati uku, bai d’au lokaci ba ya dawo garin gombe.
Hashim na barin gidan su Badiyya gun Safiyya yayi ya Sanar Mata da cewar zaiyi tafiya har Na tsawon sati biyu Rai a b’ace Tace “wallahi baka Isa ba,a satin da za’a yi bikin zaka dawo?”
Ransa yayi mugun ‘baci a ransa yace “yarinyar Nan ta samu kanta Amma Bakomai zanyi maganin ki” kirkirarren Murmushi yayi riko hannunta yayi yace “Am sorry gimbiya ta kin San bana son ‘bacin ranki tafiyar Nan fa dazanyi saudi zanje na had’o miki Kayan lefe kin San Kina da daraja a guna baxaiyu ace kina gimbiyar Hashim ace a sa Miki Kayan Nigeria a lefen ki ba” Yana maganar hade da daga Mata gira.
Murmushi tayi Tace “Hakane,gaskiya kana pampering Dina dayawa Hashim”
“Hmm to ai ke kadaice,wannan kad’an ne acikin abubuwan da na tsara Miki”
Murmushi tayi ta rufe fuska Tace “Dan Allah dagaske”
Yace “Eh dagaske nake wani abun ma sai na dawo zaki Sha mamaki irin Wanda Baki tabayin irinsa ba”
“Toh Allah ya dawo min da Kai lafiya har kasa naji na kosa da dawo war ka”
“Karki damu soon” mikewa yayi tace ” to ni Zan koma,kinsan flight dina karfe shida ne ya kamata na kwanta da wuri ko?”
Mikewa ita ma tayi Tace ” Hakane my prince,Allah ya tsare ya dawo min da Kai lafiya”
Ya amsa da “Ameen”
” And please before ka tafi call me”
” Dole na ai,da ba don Zan makara ba da sai na biyo na ganki Kan na tafi”
” Allah sarki Kar ka damu,Kiran ka kad’ai ta wadatar Dani”
” Alright,good night” Yana Mai waving hannun sa,itama tayi waving d’insa,inda yayi parking motar sa ya nufa ya Danna mata key, yayi ficewar sa.
Asiya farin cikin da take ciki bazai misaltu ba,alwala tayi ta Fara jero nafila,a yayin da Badiyya ke ji Kamar ta shake Mata wuya ta kashe ta kawaii ko zata huce takaicin dake daminta,ganin zaman da take bazai amfana mata komai ba,ta fada ban d’aki tayi alwala, fitowar ta yayi dai dai da lokacin da Asiya ke kokarin lalabu gadon d’akin,da alama kwanciya zata yi,kallon ta ta tsayi yi har ta kwanta,Yar karamar tsaki tayi ta shimfid’a prayer mat ta Fara jero nafilfili, bayan ta idar ne ta Fara jero addu’o’i “Ya Allah ina rokon ka,idan Hashim Alhairi ne a gareni ka tabbatar da Alhairi a tsakani na dashi,idan Kuma ba Alhairi bane ka musanya min da mafificin Alhairi,Ya Allah ka bawa baiwar ka Asiya lafiya ka sa tafiyar da zamuyi shine karshen wahalar ta adduniya” ta shafa a fuskar ta mamakine ya kamata da ganin hawaye a hannun ta a lokaci guda Kuma taji sanyi a zuciyar ta, a bayyane Tace “Alhamdulillah.”
Mikewa tayi ta cire hijab din dake jikinta, ta yi shigarta ta bacci ta kwanta bayan tayi addu’a.
WASHE GARI
………Tun karfe 4 Badiyya ta tashi ta shiga shirta musu kaya da duk wani abun da zasu bukata,sai da ta dauki kusan awa daya Kan ta gama had’awa a gaggauce ta fada ban d’aki tayi wanka kana ta d’aura da alwala,fitar ta kwe da wuya ta hango a Asiya zaune a bakin gado, Tace “Ahh Asiya har kin tashi?”
Cikin muryar bacci Tace “Eh Aunty”
“Okay good,maza tashi kije kiyi wanka na had’a Miki ruwa nasan Hash na hanya”
Cikin rashin fahimta asiya Tace ” Hash?”
“Emm emm eh hash,ba sunan shi hashim ba?”
“Eh!!!”
” Yauwa to ai duk wani Hashim,Akan Kira shi da hash”
” Oh na gane,Amma aunty sunan da dad’i”
Murmushi tayi Tace “Hakane”
FLASH BACK
“Kinga Badiyya bana so kina kirana da sunan Nan,me wani hashimu kamar wani tsoho?” Magana yake Wanda yake nuna cewar dagaske yake baya son sunan.
Yar karamar dariya tayi Tace “To Hashim Kam ai hashimu ne ko?”
‘bata Rai yayi ya mike da niyar barin gun,da sauri ta shiga gaban sa “haba Mana My Kai baka San wasa bane?”
Kau da Kai yayi,Yana kallon gefen hade da sa hannayen sa duka biyu aljihu, hada hannayen ta tayi wuri guda alamun am sorry tace “Please am sorry My,na daina baxan sake ba”
“Ba wannin nan,sau nawa kike fad’in hakan Kuma ki sake?”
” Naji naji a baya ne wannan but yanzu am serious sabida bana son bacin ranka”
” Kin tabbata baza ki sake ba?”
“Eh wallahi dagaske nake”
“Uhmm” kawaii yace zagayowa tayi ta inda yake fuskanta,idanuwa ta acikin Nasa tace “Please My” idanun ta fal da hawaye.
Murmushi yayi ya sa hannu ya shafo fuskanta yace “is okay,ya wuce”
Hannun sa ta rike Tace “Thank you My,but Zan iya sa maka wani sunan?”
‘dan ‘bata fuska yayi yace “A’a bana so”
“Ranka shidad’e meyasa kake saurin Yanke hukunci ka tsaya ka ji sunan tukunna Mana”