MATAR UBA 24

‘dan ya tsina fuska yayi yace “Toh ina sauraron ki rankishidad’e”
“Hash!!”
Murmushi yayi yace “Shine sunan?”
” Eh ko baiyi dad’i bane?”
“A a yayi dadi sosai,ai duk wani Abu da zai fito da ga bakin ki mai dadine”
“Hmm Kuma kace baka son Hashimu?”
” Eh nasan kina Kira nane da sunan tunda Kika ji Kaka tana kirana dashi”
” Hmm hakane Allah sarki kaka,Allah ya jikan ta”
” Ameen”
” Toh koma ka zauna” tana nuna masa mazauni da Ido.
Hannun ta cikin nasa suka koma suka zauna, d’an murza hannun ta yake q hankali yace “Diyyata”
“Na am”
“Amma kinsan sunan Nan yamin Dad’i Hash,zanzo a Rika kirana da sunan”
Murmushi tayi Tace ” Am glad you like it”
” Aunty!! Aunty!!, Ko kina sallah ne?” Asiya ke mata wannan Tambayar a d’an razane ta dawo daga duniyar tunanin da ta Lula.
Tace “a a Zan daiyi”
“Amma kina lafiya kuwa aunty,har da nayi wanka,ko wani abun kikeyi?”
” E..ehh,ina had’a Mana kaya ne,ki samu ki shirya ko?”
Ta amsa da “Toh”
Nan ta Fara sallah,Don a lokacin har an idar da sallar asuba,bayan ta idar da ta sanya doguwar Riga fari ne shigen dinki girma,an zuba Masa stones Golding color yayi dam a ajikin ta yayi matukar karb’an ta, takalmi Golding,sannan ta rataya Golding jaka sai zuba kamshi take.
Asiya na idar da sallah da taimakon Badiyya tasa doguwar riga,iri ‘dayene dana Badiyya Amma nata mint green ne,sai stones din fari, takalmin ta fari,duk sunyi matukar kyau, knocking suka ji.
“Badiyya Kun tashi kuwa?”
Muryar Mama suka jiyo, “Eh mun gama”
” Toh maza kizo parlor Abban ki na jiran ki”
” Abba Kuma” a zuciyarta ta ayyana hakan.
” Kina dai jina ko?”
” Eh Mama gani Nan zuwa”
Jakar ta ajiye ta fice,Kai tsaye parlor ta nufa, cikin Ladabi da biyayya ta durkusa ta ce “Abba ina kwana?”
“Lafiya Lau mamana,da fatan Kun tashi lafiya?”
” Lafiya Lau Abba”
Iska Mai zafi ya hura kana yace “Mamana mahaifiyar ki ta,ta fada min duk abubuwan da ke faruwa,game da maganar yaran Nan Hashim da Asiyah” ji tayi kirjinta ya Fara duka uku uku.
Ya d’aura da fad’in “Dan Allah kiyi hakuri ki dauki hakan a matsayin kaddara,karki ce zakiyi fushi ko ki kullaci Asiyah,idan kikayi hakan ladan da Kika samu a baya ta dalilin ta duk Zaki goge shi,Kar ki nuna Mata komai sannan ki cigaba da taimakon ta insha Allah,Zaki ci riba kinji ko?”
” Insha Allah Abba bakomai Kuma zanyi yanda kace”
” Toh Allah ya Miki Albarka”
” Ameen”
” Karfe nawane tafiyar Taku?”
” Karfe shida ne”
Wayarsa ya duba yace “Gashi yanzu karfe biyar da kwata,ya kamata kuna chan”
” Hashim muke jira, Amma bara naje na kira shi naji,ya ake ciki”
” Toh madallah, Allah ya tsare”
Ta amsa da Amin.
Yace ” Tashi kije,Nima Zan shiga d’aki na danyi bacci Kan gari ya waye”
” Toh Abba a tashi lafiya”
Ameen.
Ta shige d’akin su, shigarta yayi dai dai da shigowar Kiran Hashim,da sauri ta d’aga gudun karya Yanke,d’aga ‘dayan ‘bangaren yace “Assalamu Alaiki,da fatan kin tashi lafiya?”
“Lafiya Lau kaifa?”
” Alhamdulillah,da fatan Kun gama Shiri ko?”
” Eh mun gama”
” Okay gani a kofar gidan ku”
Ta amsa da ” Gamu Nan fitowa”
Tare suka katse wayar,Maida kallonta tayi ga Asiya Tace ” Tashi muje ko?”
“Aunty ban San dalilin da yasa nake jin fadiwar gaba ba,gani nake kamar ko da munje bazan samu lafiya ba”
” Karkice haka Asiyah, Insha Allah Zaki warke ina ji a jikina Zaki warke,sabida a India akwai professionals sosai,so Kar ki damu,kiyi ta addu’a kinji,Nima Zan tayaki”
” Toh aunty na gode”
Sallama sukayi wa Mama,sannan ta riko Hannunta suka fice,a tsaye suka same shi,yana hango su yayi saurin nufo su, jakar da ke hannun Badiyya ya karb’a yana mata wani irin kallo Wanda shi kansa bai San yanayi ba, motar suka nufa yayinda shi Kuma yasa Kayan a booth, a baya suka zauna shi Kuma ya zaga gaba ya zauna a gun mai zaman banza, ji tayi ance “barka da Asuba Hajiya Badiyya”
Muryar sa ta dauka Tace “Faisal?”
“Na aaaam”
“Ashe dama kana Nan?”
“Ina Nan Rankishidad’e”
“Ba a ganin ku,shiru shiru haka?”
” Eh wlh kin San abubuwan ne sai a Hankali”
Nan suka shiga hirar yaushe gamo, muryar Faisal da na Badiyya kawaii kake ji a motar, Asiya da Hashim sun Zama tamkar kurame,a haka har suka isa filin jirgi,bayan sunyi Sallama Suma nufi cikin jirgin ko wannen su ya zauna a mazaunin sa,dariyan gefen baki Badiyya tayi ganin yanayin zaman nasu,Hashim ne a gun window,sai Asiyah a tsakiya, ita Kuma tana zaune daga gefenta, bayan sun zauna Hashim ya riko hannun Asiyah, magana ya mata a kunne Wanda ni kaina banji ba, Murmushi kawaii tayi ta kwantar da kanta a kafad’ar sa,Nan jirgin su ya lula sararin samaniya.
Karfe Uku da minti arba’in da shida suka Isa kasar India, masaukin su suka sauka Wanda tun suna Nigeria,Hashim ya shirya komai da komai, d’aki biyu ya Kama musu, Badiyya da Asiyah a d’aki daya,Shima da nasa, d’akin na kallon juna,sai da ya tabba sun samu duk wani abun da suke bukata,kana ya koma d’akinsa. Duk su ukun sun kwana addu’a kasantuwar gobe ne ranar da zata ga likita.
WASHE GARI
……..karfe shida ya musu knocking Badiyya ce ta Bud’e kofar bayan sun gaisa yace “Mun shirya?”
Ta amsa da “Eh”
“Okay Ku fito ina kasa”
” Okay”
Tafiyar sa yayi ita ko ta tsaya kallon saji take soyayyae sa na karuwa a cikin zuciyar ta,ganin yana kokarin juyowa tayi saurin komawa ciki ta turo kofar da Karfi,girgiza kai yayi a bayyane yace “Badiyya.”
A kasa suka same shi Yana zaune,hannun sa rike take da magazine, yana hango su ya ajiye ya mike,yayi gaba suka Mara Masa baya,cab(Taxi) ya tara Saida suka shiga yace ” Powai’s Hiranandani Hospital”
“Okay sir”
Sun d’auki almost 30mints Kan suka Isa, hakkinsa ya bashi, sannan suka shige asibitin.
????????????????????????????????
Please comment and share
[ad_2]