Uncategorized

MATAR UBA 25

” Those that mean since when we are in school?”

“Yeah”Nan ta Koro mishi halin da suke ciki  tun daga ranar da sukayi graduation party har zuwa yanzu.

Yace “What about the girl with you?”

Nan Shima ta fada Masa sanadiyar haduwar su da Kuma matsayin ta a wurin Hashim.

Hakuri ya bata ya bukaci da ta taso ta su shiga office d’insa bata musa ba ta rufa mishi baya.

Ruwan sanyi irin na gora ta Ciro ya mika mata tayi saurin karb’a ta Bud’e Saida ta Sha kusan rabi ta sauke Goran shi ko Ammar kallon ya yake cike da tausayi “You’re hungry right?”

Kai ta d’aga Masa alamun eh, “what will you like to eat?”

“Noodles will be okay”

“Alright”

Telephone ya dauka yayi magana dasu da yaren su na indiyanci,bayan ya gama ya sauke wayar ya ajiye,a hankali yake jaan ta da Hira tun bata kulashi ta har ta Fara bihe mishi,sun cikin hirar a ka shigo da abincin.

Wurin Zama na musamman Wanda akayi don cin abinci a office d’in ajiye Mata akayi,tashi tayi a nitse ta nufi inda abincin yake tana ganin abincin tun Kan ta Fara ci yawunta ya tsinke, ganin irin kallon da Ammar ke mata hakan ya sanya ta nitsu ta fara cin abincin,sai da taci Mai isarta Kan ta tashi daga kan abincin,ta Sanar Masa da zata duba Asiyah, tare suka fita.

Hashim na zaune akan gurer dake gefen gadon da Asiyah ke kwance sai faman gyangyad’i yake, Sallamar da sukayi ne yasa ya Bud’e idanunsa ya d’aura su akan Badiyya,ganin Ammar na biye da ita yayi saurin kauda kansa.

Ammar Kan ta Asiya ya nufa Yana duba idonta da aka rufe da bandaji da jini akai Hashim yace “When will you remove the bandage?”

“After three days” 

“Alright”

” Please can I talk to you for a moment?”

” Are you talking to me?” Hashim ke wannan Tambayar

” Yeah you” sai ya fice Hashim ya bi bayan sa.

Office din Ammar suka nufa bayan sun zauna,ammar ya Fara bashi hakuri kana ya Kara Masa bayani akan abinda ya gani Shirin Hashim yayi Yana kallon sa har ya gama sannan yace “Okay I believe you”

“Thanks does that mean you’re going to marry Diyya right?”

” Nooo I can’t marry her”

” But….but why?”

“cos I don’t love her”

” No hash is a lie, you’re lying you Love her,and you’ll forever love her”

“Hmm no I don’t the only girl in my heart is Asiyah”

” The girl you bring here?”

” Yeah”

” But hash you can marry two wives or more,you can marry them both, after all you’re rich you can take care of them all.”

“You’re right but I don’t have interest of marrying two wives”

“Is okay I won’t force you since you are not interested”

“hmm….  But Ammar……. You can marry her you know”

“hahaha are you kidding me I can’t marry the woman I don’t love and am already married to the woman I love, and we have two children”

“Wow that’s very fast,stay blessed”

Mikewa yayi had’e da Mika Masa hannu yace “Thanks” Hashim ya amsa da “You’re welcome”

Badiyya da tun d’azun ta lab’e tana jin dukkanin abinda suke cewa, tayi saurin barin gun ta koma d’akin da Asiyah take.

Kalaman sa ne suke yawo a zuciyar ta “The only girl in my heart is Asiyah”

Hakan yasa ta fashe da kuka “Aunty kukan me kike?”

Muryar Asiyah ne ya sa ta yin shiru.

“Aunty na san sabida Ya Hashim kike kuka ko?”

“A….a a ba…baa shi bane kawaii dai bana Jin dad’i ne”

“Hmmm haba aunty na zauna dake tsawon watanni nasan Wace ce ke,ke jarumar mace ce, Amma na lura weekness d’in ki Hashim ne, kina matukar son sa fiye da tunanin me tunani,Amma aunty me yasa Baki Sanar dani cewar kunyi soyayya a baya ba?”

Cikin muryar kuka Tace “Sabida baida amfani, ke yake so yanzu ba ni ba like he said am his past and you’re his present,so it’s not a big deal”

” No ba haka bane Hashim Yana sonki, har kuka yayi d’azu bayan haka maganganun sa sun nuna cewar haryanzu Yana Jin haushin Dr Ammar in da ace baya sonki da zuwan yanzu da ya manta da ke Amma Bai Manta dake ba”

“Hmm Asiyah Kennan ya jikin naki hope ba Kya Jin komai?”

“Bana Jin komai,meyasa Kika canza zancen?”

” Sabida bana bukatar hakan,Kinga da ace muna da Kayan aiki ni zan Miki aikin a nija Amma Sabida rashin Kayan aiki masu Karfi shiyasa na Bari aka kawo ki Nan”

“Amma aunty kina ganin zan sake gani?”

“Eh da yardan Allah, Ammar na da kokari sosai Abokina ne,Kuma ta tabbatar Mana da cewar aikin nakin is a success,Nan da kwana uku za a cire Miki bandejin”

Murmushi tayi Tace ” Nagode sosai aunty ba don ke ba da ban San halin da nake ciki ba yanzu”

” Shhhsh,  karki Ce haka,Allah baya barin wani don wani ki daina fad’in haka kinji”

“Insha Allah bazan sake ba”

“Asiyah kin San mene ne burukana a yanzu?”

“A’a sai kin fada”

“A baya baban burina shine na Zama likitan Ido,sannan na Aurin na mijin da yake Sona nake son sa,Allah ya cika min burina na farko Amma na biyun Sam ya fita a Raina,tun sanda na had’u dake nake burin naga kin samu lafiya dake nake kwana nake tashi sai yau Allah ya cika min wannan burin nawa abinda ya rage shine a Kama wannan Mara imanin Baraka da yarta”

“Ni kaina na kosa na samu lafiya sanida na dauki fansar mahaifana da kanwata da ta kashe”

” Insha Allah ni zan cika Miki wannan burin naki” Hashim ke wannar maganar zagayawa yayi ya rike hannun ta “Banji kin ambaci maganar auren mu ba ko dai kin fasa be?”

Murmushi kawaii tayi batace Masa komai ba ita a ganin ta cin fuska ne yake yiwa Diyya hakan yasa ta zare hannun ta a nashi a hankali.

Babu Wanda ya sake cewa komai sun d’auki tsawon mintuna ashirin Kan yace “Ni zan koma masauki,akwai wani abunda kuke so ne na kawo muku?” Yana maganar idonsa akan Diyya.

Kawar da kanta tayi yace “Diyya magana nake kinyi shiru, babu abunda kuke bukata?”

Murya na rawa Tace “Wanka”

Zaro Ido yayi ya kalle yace “Wanka zan kawo Miki?”

“Ina nufin Wanka nake son yi”

“Oh okay,but idan muka tafi wa zai kular min da my queen?”

Asiyah tayi saurin fad’in “Kar ka damu akwai nurse ai zata kula dani,yanzun ma nace Mata yunwa nake ji zata kawo min abinci,Amma asibitin Nan yayi daga cewa ina jin yunwa sai a ce za a kawo min”

Dariya Hashim yayi yace ” Malama kud’in mu zaki ci duk Yana cikin hospital bills so ba kyauta zasu Baki ba”

” Oh to sai yanzu na fahimta”

Shafa kanta yayi yace “You look more beautiful when you smile queen”

Ya Maida kallon sa ga Diyya yace

“Muje ko?” 

Kai kawaii ta d’aga masa, ta fice, ganin ta fita ya manna wa Asiyah kiss an goshi yace “Sai mun dawo”

“Take care.”

Tarar da ita yayi tana tsaye a katafaren gate na asibitin sai da ya tare taxi yace “Muje ko?”

Ko kallon sa batayi ba ta shige motar, d’aga kafad’a yayi “Kinyi a banza” Yan aiyana hakana a ransa.

Bayan sun Isa hotel din da suka sauka, ta shige d’akin su Shima ya shige nasa, Diyya Kai da gwiwa ta had’a Banda kuka babu abinda take yi sai kuka ta dad’e a Haka na ta tashi ta shiga ban d’aki ta d’auro alwala dake tayi sallar azahar a asibiti, sallar la’asar kawaii tayi akan sallayar baccin wahala yayi awun gaba da ita, ganin bata fito ba hakan yasa ya nufo d’akin su ya dad’e Yana kwankwasa kofan Amma shiru hakan ya sa ya tura kofan ya shiga.

Ganin ta dukun kune sai sharar baccin ta take yace “lallai ma wato Nan baccin ta ma take hankali kwance ni Kuma na tsaya Zaman jiranta” hannu yasa zai tada ta sai kuma ya fasa “maybe baccin take bukata zan tafi kawaii idan ta tashi ta same ni a chan, ficewar sa yayi ya ja kofar.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button