AudiomackLabaraiTechWaka

Yadda Zaku Sauke Waka Daga Audiomack Zuwa Kan Wayar Ku

Ad

_____

Assalamu alaikum barkan ku da kasancewa da shafin LastNg da fatan mun same ku lafiya.

Kamar yadda muka saba kawo muku darusa akan abubuwan ya shafi waya garabasa da kuma yadda zaku magance matsalolin layukan wayoyin ku yau kuma muna tafe muku da yadda zaku sauke waka a Audiomack zuwa kan wayan ku.

Sanin kanku ne duk wanda yake amfani dashi yasan ba a iya sauke waka akan waya saidai ka saurari wakar ta cikin App na Audiomack ba daman ka tura wani kuma dole sai cikin app din zaka iya sauraron wakar.

Yau da yardan Allah zan muku bayani dalla dalla yadda zaku sauke wakar zuwa kan wayar ku yadda zaku turawa abokan ku.

Sau da dama mawaka zasu sako wakokin su amma sai su daura a Audiomack wanda saidai ka saurara ta cikin app din hakan yasa dayawa basu fiye amfani da app din ba.

Da farko ya kasance kanada app na Audiomack idan bakada shi ka sauke shi Audiomack nasan dayawan ku suna amfani sashi idan kuma baka taba amfani dashi ba idan ka sauke zai nuna maka kayi rejista da gmail naka saikayi.

To idan ka bude app din saika je kan wakar da kake son kayi download nasa.

Misali yanzu gashi na bude wakokin Umar M Shareef saina zabi wakar farko.

Ad

Aiku danna wajen Download ku jira ya gama zai nuna muku alamar ✅ ya gama kenan to yanzu kayi download na wakar amma fa baya kan wayar ka idan zaka saurari wakar saidai ka dawo wannan app din amma ta app zaka iya sauraron wakar ba tare da kayi amfani da data ba offline kenan.

Yaya Zaka Dawo Da Wakar Kan Wayar Ka

Abu na farko da muke bukata dan sauke wakar zuwa kan wayar ka shine Es File Explorer idan kana dashi sai kayi amfani dashi idan bakada shi shiga nan ka sauke Es File Explorer bayan ka sauke saika bude sa.

Idan ka bude ka taba inda na nuna da zanen nan.

Saika zabi Internal Storage wato kan waya.

Saika zabi folder me suna Android 

Idan ya bude saika zabi folder me suna Data.

Idan ya bude saika zabi folder me suna Audiomack.

Idan ya bude saika zabi files.

Saika sake zaban folder me suna Audiomack.

Wadan nan da kuke gani sune wakokin da na sauke dama album ne sunkai guda 9.

To zaku ga wakokin kamar files suke to abunda zamuyi yanzu zamuyi rename na wakokin ne sai su dawo waka kaje kan wakar da kake son rename nasa ka danne sa sai kaga ya nuna ma alamar ✅ kq duba kasa inda na nuna da zane an rubuta rename saika danna.

Saiku goge wannan numbobi na ciki ku rubuta sunan wakar sai kusa .mp3 kamar yadda nayi Aisha.mp3 saiku danna ok.

Atake zaku ga sun dawo waka kamar haka kun gansu aisha da kuma farin jini.

Sai kuje ka music player ku nakan waya ku kunna wakar zaku ga yayi.

Idan dame tambaya ya aje mana comment a box na kasa .

               

Ad

_____

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button