Uncategorized

MATAR UBA 25

Hiran su suke Sha sosai da Masoyiyar sa,tun farkon Soyayyar su basu tab’a Hira sama da mintuna talatin ba hakan yasa yake Jin wani irin farin ciki na musamman.

Diyya na tashi daga bacci ta sa hanni ta d’auki wayarta karfe Bakwai saura, tsaki tayi Tace “Me yake yi haka tun dazu Bai min magana ba”

Message ta gani a fuskar wayarta “Na shigo na samu kina bacci shiyasa ban tashe ki ba, idan kin tashi ni na wuce asibiti sai kin zo”

Tsaki kawaii tayi ta shiga bathroom ta watsa ruwa sannan ta shirya ta d’auki Kaya set biyu wa Asiyah tasan Dole zata bukaci wanka.

Taxi ta hau ta wuce asibiti, tana shiga d’akin ta tarar dasu sai dariya suke sai taji ba Dad’i da sallama ta shiga Asiyah ce kad’ai ta amsa Mata sallamar  “Aunty kin tashi? D’axu nake tambayar Ya Hashim inda ya baro min ke yace min Kanki na ciwo kina bacci da fatan kinji sauki ko?”

Kallon shi tayi taga ya kauda Kai “To meyasa ya mata karya?” A ranta ta aiyana hakan a bayyane kuwa tace “Alhamdulillah da sauki stress ne kawaii dama”

“Allah sarki Allah ya sa kaffarane”

“Ameen”

“Ya kamata ki watsa ruwa  tun safe rabon ki da wanka, gashi Kuma nasan bakiyi sallah ba”

Murmushi tayi Tace “Zanyi”

Da taimakon ta suka shiga ban d’aki tayi wanka,duk a ban d’akin tasa kaya sannan suka fito tare.

Zaunar da ita tayi a bakin gado tana shafa mata Mai suna Hira sama sama.

Hashim mamakin diyya yake meyaay take taimakata bayan yasan halin Diyya da muguwar kishi duk da tasan cewar Yana son Asiyah hakan bai Hana ta daina kula da ita ba, Allah ya sa ba da wata manufa take ba..

Kwana a tashi ba wuya a wurin Allah a  yaune za a bud’ewa Asiyah Dr Ammar ne a kanta Saida ya Mata wasu allurai yace Nan da awa d’aya zai Bud’e Amma Kan ya fita yace da ita wane ne take son fara gani idan aka Bud’e Mata ido, ga mamakin su ta ambaci sunan Badiyya, duk sun d’auka Hashim zata ce har ita kanta Diyya tayi mamakin Jin hakan Tace “Amma Asiyah me yasa kikace ni kike son fara gani?”

“Aunty you’re like an angel to me, I just want to see you”

Murmushi kawaii tayi,yayin da Hashim yake mamakin irin shakuwar dake tsakanin Asiyah da Diyya, Ammar fita yayi  awa d’aya na cika ya shigo da nurses guda biyu a biye dashi.

Ba Asiyah kad’ai ba hatta Diyya da Hashim Saida sukaji kirjin su ya soma bugawa.

????????????????????????????????

Please share and comment

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button