Uncategorized

MATAR UBA 26

“Oh Hashim duk wannan abubuwan dake faruwa Amma baka sanar Dani ba sai yanzu? Dama da Badiyya kuka yi tafiyar?”

“Eh da ita mukayi,sabida itace take kula da ita, Am sorry Mom naga Sam Baki kaunar yarinyar ne shiysa”

“A’a Hashim ba Haka bane kawaii dai naga yanda duk baka damu da kanka bane sai ita shiysa Kuma kasan bani da wani buri da ya wuce ka koma Kan aikin Mahaifin ka”

” Insha Allah Mom satin Nan zan Fara zuwa aiki”

” Aiko da na ji dad’i, yarinyar Nan Badiyya Yar Albarka ce duk irin Soyayyar da take maka kishi bai hanata kula da Asiyah ba”

“Hmmm mom Diyyata Kenan”

” Dan Allah rufe min baki wai Diyyata kamanta irin rashin mutuncin da kq shuka Mata ne, yarinyar Nan taxo gidan Nan don Kai yafi a irga”

“To Mom ai komai ya wuce yanzu ko,mun dai daita”

“Masha Allah,nafi kowa farin ciki,na tabbata da Mahaifin ka na raye ba karamin dad’in had’in Nan zaiyi ba,duk da ka bajire Masa a baya”

“Oh nikam na shiga uku”

“Tara ka shiga ba uku” dariya kawaii yake mikewa yayi yace “Ni zan fita”

“Ina Kuma zaka je,da Daren nan?”

“Hira zanje”

“Lallai Son Amma baka duba time ba ko?”

Agogon hannun sa ya duba “Inna lillahi wa Inna ilaihirraji’un”

“ya da salati Haka?”

“Mom karfe Sha biyu saura fa, gaskiya banji dad’i ba”

“Oh da Kai tunda ka cika Mara kunya gidan su Diyya zaka je da way zakayi Hira a cikin su?”

“Duk su biyun”

Mom yarfa hannu ta shigayi tana salati “A ina aka tab’a yin Haka Hira da Yan Mata biyu?”

“Ni Zan Fara mom”

Hab’ar ta ta rike Baki a Bud’e take kallon sa, dariya kawaii yayi yace “Ni zan kwanta sai da safe” ya haura d’akin sa Yana dariya.

“Oh Ni yasu,wani abu sai wannan zamani ko a littafin ban tab’a ji anyi haka ba,Amma da sauki tunda da amincewar su” tana Kai Nan itama ta haura d’akin ta.

Asiyah da Diyya sunyi ta zuba Ido don ganin Hashim Amma Shiru kaje ji, Diyya ta Kira layin sa yafi sau biyar bai d’aga ba, a Lokacin Yana parlor da mummy ya bar wayar a d’akin sa.

Yana ganin missed call d’in yabi baya ya Kira har sau uku ba a d’aga ba sai ya Kuma Kira har ya kusa yankewa a ka ‘daga cikin muryar bacci Tace “Hello!!!”

Ajiyar zuciya yayi yace “You can’t imagine how much I missed this voice”

Murmushi kawai tayi ya d’aura da fad’in “Am so sorry Diyya for not giving you the chance to explain yourself to me”

“Is okay kasan komai mukaddarine daga Allah, idan da a Lokacin Nan mukayi aure na tabbata baza ka had’u da Asiyah ba, Asiyah kaddarar kace ko ince kaddarar muce,gaba ki d’aya”

“Hakane, ke d’in ta dabance Queen, Nagode sosai da kike kula da kanwarki”

“Ban bukatar godiyar ka nayi ne don Allah sannan Asiyah yarinya ce Mai hankali manya,tun farkon Haduwar mu da ita naji ta shiga Raina,da Kuma nasan itace farin cikin ka sai na kud’iri a niyar kyautata Mata Sabida Ina son abunda kake so King”

“Kin San yanda nayi missing sunar Nan da ga bakin ki kuwa?”

“hmm a a sai ka fad’a”

” Ke dai Bari don bazai kwatantu ba”

” To Shikenan rankashidad’e na bari”

” kanwar taki tayi bacci ne?”

“Eh tayi bacci”

” Okay kema ya kamata ki Samu ki kwanta ko?”

“Har ka gaji da Jin murya ta?” Cikin muryar Shagwab’a take maganar, wani yaaarrr yaji a jikin sa Nan da Nan yaji wani irin shauqi ya kamashi.

“am sorry queen, nasan kin gaji sosai Kuma gobe nake so mu Fara processing yanda za a kama Baraka”

” Kamar kasan abinda ke cikin zuciya ta,gobe insha Allah Zamuje gidan Abban Yesmin”

“Allah ya kaimu to ku d’auke Ni driver Mana nazo Ni na Kai ki”

“Hahaha to Shikenan, an gama”

“idan Kun shirya goben sai Ku kirani”

“Toh Insha Allah”

“ki shafa min Kan karamar Queen”

Hannu tasa akan Asiyah tace “Na shafa maka”

” Toh saura na My Queen” tasa hannu a kanta ta shafa Tace “Done”

“Thanks Love,good night,ki kula min da Kanki kinji?”

“insha Allah, please do same”

“I’ll bye”

A tare suka katse wayar.

Murmushi kawai take tana Jin wani irin dad’i, Asiyah ma Murmushi take yi don tun Fara wayar su har suka gama tana Jin su,Amma tayi kamar bata ji ba. (oh ni Milhaat ina ganin ikon Allah ,ni kam bazan iya irin wannan Soyayyar ba).

WASHE GARI

……….. “Safiya Ni sa’ar kice ina magana kina Maida min magana?”

“Mummy me na Miki Kuma ,Wai ke meyasa kike son takurawa rayuwatane ke Baki da aikin yi sai masifa haba”

Tashi tayi ta wanka mata maruka biyu masu zafi Tace “Idan Kika sake ina magana kinayii sai na datse miki harshe Kuma na kashe ki”

“Mtswww akwai wani abunda Kika kware Akan sane Banda kisa to sai me idan kin kashe ni?”

Ganin tayi kanta tasa gudu tana biye da ita har Saida ta shige d’akin ta ta kulle kofar ta ciki.

A tsawace Tace “Safiya….. Safiya open this door”

“Baza a Bud’e d’in ba”

“safiya ni kike cewa Haka? Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un,wai me ke Shirin faruwane,asirin Nan na kokarin karyewa dani kike zancen yarinya idan kin San wata baki San wata ba”

Ta shige d’akin ta.

Wani Kullin magani ta dauka a cikin Waldrope d’in ta, fridge ta Bud’e ta d’auko yoghurt ta juye Rabin maganin a ciki,ta girgiza da kyau ta Maida ta ajiye, Jakarta ta d’auko ta shige mota tayi ficewar ta.

Safiyya na Jin karar motar ta gane ta fita ne tsaki ta jaaa, ta fito fridge ta nufa ta d’auki wannan yoghurt din da Baraka tasa Abu a ciki, tana Bud’ewa ta kafa Kai ta shanye tass ko bismillah batayi ba,wani irin bacci ne taji ya kamata,har ta Fara haurawa Kan stairs taji baza ta iya ba ta dawo kan sofa ta kwanta.

????????????????????????????????

Please comment and Share

Milhat ce 

Yar Terawa

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button