KISSA KO MAKIRCI 1-END

KISSA KO MAKIRCI Page 41 to 50 (The End)

Harta karasa shigowa falon, bai kuma cewa komai ba sai kllonta da yake yi, yayin da falon ya cika da sautin kukan fauziya, hjy binta zama tayi akan kujera, sai a sannan Mahmud ya iya furta kalman mama, ta daga mai hannu alaman yayi shuru, tace naji komai bana bukatan wani magana, yanzu dai kafin wani bayani ka dawo da matarka, ganin ynda ta daure fuska babu alaman wasa a ciki, yasa yace na dawo da ita, jin haka fauziya dake kukan munafurci ta matsa kusa da hjy binta tana fadin wlh mama nasan nan gaba zai kara saki na, indai akan waccan matar tashi ne, ta nuna salma da gaba daya komai nata ya tsaya cak, sai a sannan hjy binta ta kalli salma, tace mlm ki zauna kin wani tsaya ki kam, salma tayi sauri ta zauna, nan hjy binta ta kalli fauziya dake faman sharara kuka, tace fauziya naji abun daya faru tun daka farko, nayi mamakin da wannan kalman ya fito daka bakin ki, a yau inda bani da wani halaka dake dasai nasa an hukunta ki, domin bazan bari aci zarafin jika naba, ina so daka yau ki sani akan wannan yaron zan iya sabama kowa dan haka ki kiyaye karki kuma aikata wannan kuskuren dan bazan dauka ba, fauziya da mamaki ya cika ta, ta amsa da toh, amma cikin zuciyarta fadi take wlh sai nayi maganinki basai kinga abun da za’a haifa ba, balle ki kirashi jika ba, nan da kwana biyu cikin zai zube sai inga ta tsiya, Hjy binta ta katse mata tunani da fadin saura ke nazo ne in miki kashedi, salma ta dago dakai cikin tsoro tare da fargaban mai zata fad’a, tace naga take takenki bakya son wannan cikin sai yasa kike wasa dashi, wlh kinji na rantse miki indai wani abu ya sami wannan cikin saina sa an hukunta ki, taci gaba da fadin nasa an kawo masu aiki wanda zasu dinga yi muku abinci, saura kuma ki koresu, indai kikai hakan saina saba miki, daka yau zasu fara abinci a gidan nan har sai kin haiyu, in yaso kyayi duk abinda kika ga dama, salma cikin sanyin murya tace nagode mama, hjy binta tace daina godemin badan ke nayi ba, tace ku bamu waje, nan ita da fauziya suka tashi ko wacce tayi dakinta,

Ta kalli Mahmud wanda gaba daya ya shiga cikin wani hali, sai taga kaman ya rame, lokaci daya taji ya bata tausayi ta tashi ta dawo kujeran da yake, ta kira sunanshi, ya amsa cikin taushin murya, tace banji dadin abun da kayi ba, duk da itama bata kyauta ba, bai kamata ka saketa ba, yar uwarka ce, ko kana so ka bata mana zumunci ne? Yayi saurin cewa a’a mama abubuwan fauziya ne sunyi yawa rashin mutuncin yau daban na gobe daban, tace kayi hakuri kaji, bana so in kara jin ka furta kalman saki a bakin ka, kaima gashi yanzu za’a fara maka haiyuwa ko kana so kaima aima naka ne? Yace mama Allah ne shaida na, bana sakin mace ba tare da hujja ba, tace koma miye daka yau bana so, ka kara hakuri akan komai kaji, yace insha Allah, nan suka dan taba fira na d’a da uwa, sannan ta tashi ta wuce, 

Fauziya tana shiga d’aki ta dauki waya ta kira mamanta, tana fad’a mata abunda ya faru, hjy zaliha, tace lallai binta, dole in sake daukan mataki akanta, wato ita idonta ya rufe akan zata sami jika koh, shine har take fad’a miki magana a gaban wannan yar iskan, kar ki damu zan dau mataki, fauziya tace ni yanzu gaba daya ma ya daina zuwa d’aki na, gaba daya ya tare a wajanta, hjy zaliha tace kar ki damu kwanan nan zai dawo wajanki bari cikin ya zube, ai yau saura kwana biyu sati dayan ya cika, kinga in cikin ya zube a nan sai musan yanda za muyi mu xuga binta akan da gangan ta zubar, na tabbata sai tasa an mata wulakanci, daka karshe tasa Mahmud ya saketa, kinga ya dawo naki ke daya sai ynda kika ce, nan fauziya ta saki shewa cikin jin dadi tace kai mama sai yasa nake sonki wlh, hyj zaliha tayi dariya tace zan iya yi miki komai ai dan inga kina farin ciki,. 

Wasa2 har sati dayan ya wuce sati biyu, amma cikin na nan, fauziya ta shiga damuwa sosai kullum salma kaman ana kara mata lafiya, ga wani abun bakin ciki hjy binta tana yawan zuwa duba salma, taga ya take ciki, hjy binta ta sauko akan tsanar da tama salma,suna da gida a zone2 wani katon gida, ta sami labarin gidan ya zama na fauziya, ga wani gidan gonan su inda ake had’a su drinks kala2 dasu kaji kifi da sauransu shima ya zama mallakinta ga wasu gida da take dasu guda biyu, a cikin Abuja, nan ta kira Mahmud ta tambaye shi akan mai zaisa yaba fauziya gida da gidan gona bai fad’a mata ba, nn yace wlh bashi ya bata ba, ta kira fauziya tace ya akai ya zama nata, budan bakinta tace ki tambayi danki mana, abun ya bata mamaki, gashi taji labari wajan mutane da dama akan halayen fauziya na bin malamai nan Hjy binta taji ta fitar mata a rai, tace insha Allah zan kara dagewa da addu’a, tun daka lokacin ta fara sakema salma domin ta gano itace mai son danta tsakani da Allah, 

Fauziya taje wajan boka akan har yanzu cikin bai zube ba, nan yace mata ai cikin bazai taba fita ba, amma abu daya xa’a mata yaron zaizo bada rai ba, yace inta yarda toh, tace ta amince, yace toh duk sati za’a dinga yima aljanu ynka suna shan jini, a kalla zaki dinga kashe million 5 duk sati, tace babu komai indai za’a kashe dan yaxo bada rai ba, ni burina kawai yaron ya mutu tunda ni har yanzu bani da ciki yama daina kulani, boka ya kwashe da dariya domin yaga zai tatseta yace ki tashi kije sai na jiki, ta tashi ta tafi, boka ya kuma kwashewa da dariya tare da fadin mahaukaciya ni na isa in kashe mutum ne, ko in zubar da ciki, nima sa’a ne inna fada abu ya faru, amma wannan banyi sa’a ba, sai ki kawo kudi inta ci.

Salma taja yarinyar matar nan jikinta inda yarinyar take fad’a mata bara xuka zo Abuja, ita da mamanta wanda take dauke da breast cancer sai a sannan salma ta lura inta shiga dakin tana jin wani wari duk saita dauka ciki ne yasa take ji, yarinyar tace babanta ya rasu wajan shekara biyar kenan dangin shi suka cinye dan abun daya bari, ga cuta na damun mamana anyi na hausa abun ya warke ashe ya lafa ne, daka baya ya kuma tashi anyi na hausan yaki yi, dole muka je asibiti akace sai an yanke nonan, ta yarda aka yanke gashi dayan kuma ya kama, wanda wannan karan taki yarda a yanke, sai dai magani da take tasha, gashi bamu damai bamu sai dai muyi bara mu sami na abinci, wata wacce muke bara ta bata shawaran muzo Abuja zamu iya samun wanda zai dauki nauyinta a dubata a babban asibiti hala ta warke, shine abun daya kawo mu Abuja, muna bara duk inda muka ga kango sai mu kwana abun mu, wata rana na sami labarin mijinki akan yana taimaka ma mutane, wata wacce muke bara ta rakani office dinshi nan muka zauna muna ta jira amma shuru bai fito ba, muka wuce wata rana na kuma komawa ni daya a nan naga ya fito zai shiga mota shida masu bashi kulawa, gaba daya saina kasa zuwa wajanshi, haka naita zuwa amma bana iya yi mishi magana daka karshe masu gadin wajan suka ce kar in kuma zuwa, shine bamu sake haduwa ba saida na ganshi asibiti driver dinshi ya bigeni, salma ta tausaya masu sosai, ta dau alkawarin zata sa Mahmud ya taimake su. 

Maryam Obam ????

????????????KISSA KO MAKIRCI????????????

                 NA

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA

(Mrs nura kuriga)

                  85to90

Salma tama Mahmud bayani akan yarinyar da mmnta, shima ya tausaya yace zai sa a kaita asibiti koh Allah zai sa a dace, salma taji dadi tare dayi mai godiya, yayi murmushi yace sai ki fada mata su shirya gobe sai a kaita, nan salma tace toh tare da tashi ya bita da kallo yana murmushi ganin yanda ta tashi tana nishi, ganin yana murmushi yasa ta bishi da ido tare da fadin lafiya? Dariya ya saki mai kara yace babu komai, ta dan bata fuska tace akwai mana ka fadamin plz, tashi yayi yaxo kusa da kunnanta yace I love you, murmushi tayi cikin Jin dadi tace I love you too my dearest husband, sannan ta fita. 

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button