MATAR UBA COMPLETE

MATAR UBA 34

Parking space sukayi parking sannan ta fice a motar tace Masa idan kaji kirana ka shigo kawai”

Kai ya d’aga mata had’e da fad’in “To.”

Knocking na kofar ta shigayi tana addu’o’i tana fargaban Shiga gidan, ba dad’ewa aka Bud’e kofar , Baraka na ganin ta cike da mamaki tace “Qawata kece?”

Kirkirerren Murmushi tayi tace “Eh nice”

“Shigo Mana,naji Dad’in ganin ki kuwa”

Tana shiga a parlor suka zauna tace “ke kuwa daga ina kike haka dare dare?”

Yar karamar dariya tayi tace “Wallahi daga gidan mu naje gaida su Mamane”

“Allah sarki ya jikin nata ban samu damar zuwa duba jikin nata ba”

“Eh kin San komai sai Allah yayi,kince  kinji dad’in gani na,akwai wani Labari ne?” 

Dariya tayi sosai Tace “Labari Mai dad’i kuwa kin san yau hakata ta cimma ruwa”

“To me ya Faru?”

“Maganar yarinyar Nan Asiyah” gyara Zama tayi tace “Eh me ya same ta?”

Ba Nana kadai ba har su Hashim,khamal, Yesmin da farees suna son Jin abunda ya same ta.

Dariya ta Kuma yi tace “Ashe haka yarinyar Nan take da dad’i? Na dad’e banji Dad’in irin na yauba”

Zaro Ido tayi tace “Kina nufin kin…..” Kan ta karasa maganar Tace “kin fiye son jan magana ai na fad’a Miki yarinyar ta cika ta ko Inna,musamman kirjinta a yau hankali na ya kwanta na shasu nayi Wasa da su son raina”

“Tohhh Kuma Asiyar bata hanaki ba?”

“Ai bazaiyu ba,sabida ita kanta taji dad’in abun Baki ga yanda ta rikice ba”

“ban Gane ba?”

” Ke matsalata dake wauta, ai ba haka kawaii bane turare na shaka mata,ta bada Kai”

“Oh na fahimta,yanzu tana ina ne?”

“Tana d’aki sai aikin kuka take”

“Allah sarki Baraka is high time ki daina abinda kike d’in Nan ki nitsu ki tuba ki koma ga Allah”

” Mtsww Dan Allah ki daina kawo min irin wannan maganar, yanzu kizo muje in shaka mata turaren Nan ki d’ana ta kiji”

” A a nikam ai na fad’a Miki na daina aikin kazantar nan”

Tab’e Baki tayi tace “Chaan Miki”

Mikewa Nana Tayi tace “Ina daughter na take?”

“Tana d’akin ta ita ma yanzu na gama ligwigwiya ta” 

Rike baki Nana tayi tace “Oh Baraka jarrabar ki ta wuce misali,bari ba shiga Naga Safiyyar”

“okay ni zan Shiga kitchen yunwa nake ji”

Baraka ta nufi kitchen ita Kuma ta haura d’akin Safiyya.

Tana Bud’e kofar Safiyya na ganin ta tayi Murmushi, murmushin ita ma ta Maida mata ta Mata hannu alamun kizo.

‘dakin Asiyah suka shiga Asiyah na Jin motsi a zabure ta tashi ta zauna, Nana tace “Yi hakuri Asiyah mune”

Ajiyar zuciya tayi had’e da mikewa tace “Ina wuni mummy”

Ta amsa da “Lafiya Lau, Babu dogon gaisuwa” ta Maida kallon ta ga Safiyya tace “Hankalin mu ya tashi Hashim yanzu haka suna gidana,Ina fatan babu abinda ta Muku?”

Cikin muryar kuka Safiyya tace “Tayi abunda ta Saba”

“Shikenan Shikenan, safiya ya kamata ki d’auko kwaryar Nan in ba haka ba Wallahi duk baza muji Dad’i ba don na lura tana gab da kamamu”

“Wallahi mummy ina son d’auka Amma idan naje sai naji na kasa,ban San meyasa ba”

“Duk wannan Mai sauki ne kina karanta ayatul qursiyu falaki da nasi da sallatin Annabi Shikenan”

” In ko hakane zanje na d’auko yanzun Nan ki jira ni”

“A a ai gara ki bari in Bata gida”

” Duk ‘daya ina kince Ana d’auka karfinta ya Kare?”

” Eh hakane”

Cikin sauri Safiyya ta fita ta shige d’akin Baraka,Kai tsaye Waldrop d’in ta nufa dake ta San inda yake bata Sha wahalar nema ba”

Tana gani ta yi dukkanin addu’o’in da Nana Tace tayi ga mamakin ta tana sa hannu ta d’auko kwaryan, ba ta tsaya ‘bata lokaci ba ta Maida kayan yanda suke ta fice daga d’akin,tana Shiga d’akin Asiyah Nana na gani Saida ta tsorata Tace “Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un ya Naga kwaryar ta Kara girma?”

“Mummy yanzu ki fita da kwaryan Nan”

“In Kai ina Safiyya fasashi ya kamata kiyi”

” Kar ki damu ki tafi dashi gida Ni zan Zo na fasa shi”

“A a ni hakan bai min ba,ai gara ki fasa shi Yan……”

” Ki taho dashi Nana” muryar khamal taji a ear piece d’in dake makale a kunnen ta.

Ba musu ta karb’a,anyi sa’a ta Zo da jakar hannu irin Mama’s Bag d’in nan,tana karb’a ta sashi a ciki.

Da sauri ta fice a d’akin, Safiyya tabi bayan ta Asiya zata bi bayan su, Safiyya tayi saurin fad’in “Ki zauna in case ko ta ganmu baza ta zargi wani Abu ba”

Kai kawaii ta d’aga ta koma d’akin ta Amma ta makale a bakin kofa tana son ganin fitar Nana.

Nana na Isa parlor tana ganin Baraka batae parlor tayi saurin fita,yayin da Safiyya ta tsaya tana leke Nana na Isa gun Motar Baraka ta fito, kallon Safiyya ta tsaya yi cikin sanyin murya tace “Safiyya leken me kike haka?”

Cikin Rawar murya Tace “Mummy Nana Ce ta fita Tace min in gaya Miki Abban Yesmin Na jiran ta a gida.”

Tab’e baki tayi tace “shine ba sallama Bari na duba ta na gani”

“A a mummy ai ba sai kin bita ba ai ta Riga ta Shiga mota”

Kallon ta kawaii tayi ta sa kai ta fita.

Motar ta nufa Kai tsaye a dai dai Lokacin da Nana da Faisal ke kokarin sa ka kwaryar a cikin Booth na motar, kanta tasa tana leken cikin Booth d’in Tace “Nana me kike sawa a Nan,Kuma meyasa Kika fito ba tare da kin min Sallama ba?”

Nana ta tsorata matuka hatta Faisal kasa magana yayi sai kallon kallo sukeyi wa juna.

????????????????????????????????

Please comment and share

Milhat ce

Yar Terawa

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button