MATAR UBA COMPLETE

MATAR UBA 36

 ????????????????????????????????     *MATAR UBA*

????????????????????????????????

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

                 *(MILHAAT)*

*????MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION????????️*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

CHAPTER 36

Kara Baraka ta saka Mai kara,toshe kunnuwan ta tayi tana ihu daga bisani ta yanke jiki ta Fad’i sumammiya.

????????????????????????????????

……… A hankali take Bud’e idon ta harta Bud’e su duka, a zabure ta tashi ta zauna, kallon d’akin ta farayi bayyane tace ko dai mafarki nake ne?”

Muryar Asiya taji tace “Ba matarki kike ba mummy da gaske ne”

Tana hango Safiyya daga gefe,sai su Khamal,Nana,hashim, Faisal,farees, Yesmin ta dafe kanta tayi cikin kuka tace “Safiyya dake aka had’a Baki aka cuce ni? Meyasa kuka kawo ni asibiti da Kun barni na mutu”

“ai ba don halin ki aka kawo ki Nan ba Ni inda ta nine da an barki kin mutu, sannan Kuma kafarki ta karye Dole mu kawo ki asibiti ko don kiji dad’in zuwa gidan yari”

Kad’a Kai tayi tace “Ni za a Kama a Kai gidan yari? Ni Baraka?”

Sai ta kyalkyale da dariya a d’aura da fad’in “Ai babu Mai kamani duk duniya, Kar kuga don Kun fasa min kwarya Kun gama dani to karyar ku”

Murmushin gefen Baki Safiyya tayi Tace “Ko da kuwa hukuma sunji wannan?” Nan ta Shiga playing records d’in maganar su da Nana Amma duk an cire duk muryar Nana,Baraka hankalin ta yayi mugun tashi Nan da Nan zufa ya keto mata.

Asiyah Tace “Mummy ba wannan ba, idan Kuma suka kalli wanna fa?”

Video Lokacin da ta kashe Anisah ta gani,zaro Ido tayi murya na rawa Tace “Wannan…… Wannan kamarni….A’aa A’a bani b’ace, to Amma ai gashi Nan,Kuma anisa Ce a kwance”

Ta fashe da kuka Tace “A Ina kuka samu Wannan Ashe dama Kun dad’e kuna bibiyata, Innalillahi wa……..”

A tsawace Safiyya tace “Kul karki kuskura ki ambaci kalmar Innalillahi anan ai ba ki San da Allahn ba, tashin hankali Baki gani ba tukunna, Yauwa kikace a ina muka Sami video Nan,da fatan kin gane wachan?”

‘dago kanta tayi tana kallon wacce take nuna mata, Baki a Bud’e take kallon ta tace “Rukayya!!! Ashe dama kina raye, an fa Ce min kin mutu” Dariya tayi Tace “Shege boka Wallahi cemin yayi kin mutu”

Kad’a Kai tayi tace “Ban mutu ba kina ganin don kinyi nasarar kashe min Yar uwata Nima Zaki iya? Na dad’e ina jiran wannan ranar da zanga ki cikin tashin hankali Alhamdulillah Allah ya nuna min ko a yanzu ba mutu ruhina zai huta, Baraka ke azzaluma ce,macuciya, sabida ke ina ji ina gani na bar cibiyata na guji Asiyah a lokacin da take bukata na, Baraka da za a bi zab’i na ba rataye ki zanzo a yi ba zanso ana yanka Naman ki gunduwa gunduwa har Allah ya d’auki ranki”

Fashewa tayi da kuka had’a hannu biyu tayi wuri guda tace “Dan Allah Dan Allah ki yafe min nasan ban chanchanci yafiyar ku ba Amma Dan Allah ki yafe min, Allah ma idan muka masa laifi yana yafe mana”

A tsawace Asiyah tace “Ke har kin Isa kice mu yafe miki? Rayukan da Kika kashe Kuma fa? Zasu dawo ne? Idan har kina so mu yafe miki to ki dawo min da iyaye na da kanwata, Allah ubangiji ya tsinewa duk MATAR UBA da take cutar da ‘ya’yan mijin ta sabida kishi” tana Kai Nan ta fice,Hashim ya rufa mata baya.

A Haka duk suka fita d’aya bayan d’aya daga Mai tsaki sai mai Allah wadai, Nana kuwa yawu ta Tofa mata,duk suka watse suka barta daga ita sai Safiyya dake tsaye a kanta, Murmushi tayi tace “Yauwa Safiyya nasan ko duk duniya zasu juya min baya ke baza ki gujeni ba”

Murmushin gefen Baki tayi tace “Mummy kin tuba Kika ce baza ki sake abunda kikayi ba?”

Murya na rawa tace ” Eh eh Wallahi bazan sake ba,Kar ki juya min baya ki gujeni kamar yadda Asiyah tayi ta Manta irin wahalar da Nasha a kanta”

“Hakane bazan guje ki ba Mummy,zan zauna a tare dake inga yanda Zaki wulakanta, ina so na ga yanda Allah zaiyi dake don Wallahi na tabbata tun anan duniya Allah zai nuna miki matsayin ki a lahira, kece Zina,kece shirka kece kashe muminai duk sabida abun duniya,har kina da bakin cewa kin Sha wahala Akan Aunty Asiyah? tun tasowar ta bata San me ake cewa Jin dad’iin rayuwa ba duk sabida ke,kin kashe mata uwar kin kashe mata uba da Kuma kanwarta, Anisah yar uwata ce, Sadeeq  Kuma Mahaifina  ne,bazan tab’a yafe miki ba Mummy,kisani Ni  zan kashe ki,kuma nasan Allah bazai kamani da laifin komai ba sai ma in samu Ladar na rage mugun iri a doron kasa. ” Tana kai nan tasa kai tayi ficewar ta,baraka na Kiran sunan ta Amma ko ajikin ta.

Asiyah na fita a reception ta zauna ta had’a kai dagwiwa tana kuka, Hashim Zama yayi a gefen ta cikin murya Mai sanyi yace “Queen” ‘dago kanta tayi a hankali ta d’aura su Akan fuskar sa Murmushi ya mata ita ma murmushin tayi yace “Queen kuka? Kukar me kike yi yanzu bayan matsalar ki ta kare?”

Cikin muryar kuka tace “King kasan jiya kasa bacci nayi,jiya ban rintsa ba gani nake zata dawo ta kashe mu, Kuma ganin iyaye na da nayi a kwalban Nan………” Kuka ne ya kwace ta kasa karasa maganar, ta sa kanta a cinyar sa, a hankali ya fara bubbuga mata baya Yana rarrashin ta a haka har su ka fito suka Tarar dasu a Haka.

Khamal yace “Alhamdulillah yanzu dai komai yazo karshe”

Nana tayi saurin fad’in “zaizo  dai ai da sauran Rina a kaba,tunda Baraka na raye Kuma ba a killace ta ba Ni Sam hankali na Bai kwanta da a barta anan ita kad’ai ba gara a nemo masu tsaronta, Baraka ta wuce duk yanda kuke tunani”

Safiyya tace “Ni kaina ban yarda a barta a Nan ita kad’ai ba”

Khamal yace “Mai laifi ce dole a tsare ta yanzu haka akwai wasu polisawa har mutum hud’u suna zuwa”

Rukayya Tace “Nana nagode sosai Allah ya saka”

“A a Rukayya karki gode min nayi abunda ya do nayi ne”

Farees yace “Yauwa ga Nan polisawan ma”

Khamal ne ya nuna musu d’akin da take har yanzu kukan take, girgiza kaie yayi ya fito, Yana fitowa yace “Asiyah ke da Safiyya Zaku dawo gidana da zama sabida hankali na bazai kwanta ba idan kuka zauna a gidan Nan naku ku kad’ai”

Ba musu suka amsa da to, yace “mu  tafi ko?”

Hashim yace “Zan taho da Asiyah zamu Maida Aunty Rukayya gida”

Khamal yace “Okay Kar ku dad’e please, kuna kaita ki dawo gida yawo ba naku bane har sai an yanke wa Baraka hukunci”

Faisal yace “Wannan hakane Allah ya kare mu da kariyar sa”

Duk suka amsa da ameen, Hashim, Asiyah da Rukayya motar hashim suka shiga, Safiyya Kuma ta Shiga motar farees yayin da Faysal Kuma ya d’auki Yesmin, khamal kad’a kai yayi yace “Yaran yanzu ba su da kunya ko kad’an”

Dariya Nana tayi Tace “Kai har ka manta Rawar Kai da rawan jikin da kayie tayi a kaina?”

Shima Dariyar yayi yace “Ina fa,ai bazan manta ba”

Dariya sukayi suka shiga motar su.

Hashim suna Isa gidan Aunty Rukayya ya dawo gidan su Yesmin, bai tsaya ‘bata lokaci ba yace zai tafi,Amma baie tafi ba har sai da ya sanarwa Asiyah cewar yau za a je nema Masa auren Diyya shiysa ma ake ta neman said tun ‘dazu.murmushi kawaii tayi sannan tayi musu fatan Alhairi.

Yana Isa gidan kawun sa,ya tabbatar Masa da cewar an bashi Diyya sannan ansa rana Nan da wata d’aya za a d’aura yayi masa godiya ya tashi ya tafi.

Wasa Wasa yau satin Baraka uku a asibiti, tunda aka kama Baraka komai yake tafiya musu dai dai,tun ranar da suka bar asibitin Babu Wanda ya Kuma komawa sai khamal da ya Zama Dole don tabbas da cewar a tsare ta,Baraka wani irin zazzabi ne ya kamata Wanda shiyasa alkali ta d’aga shari’ar har sai ta samu sauki, yayin da ake ta shirye shiryen Auren Hashim da Badiyya.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button