MATAR UBA 36

Asiyah acikin Yan kwanaki ta murmure tayi kyau kamar ba ita ba,ba tsangwama ba duka ba zagi, Lokaci zuwa lokaci suna zuwa gidan Aunty Rukayya, Yesmin kuwa dad’i take ji sosai sabida ba ita kad’ai bace a gidan, makaranta kawaii ke Raba su da Safiyya da Asiyah, Khamal na ganin Hakan ya sasu Suma a makaranta, Asiya ta girma yanzu don ratar dake tsakanin Asiyah da Safiyya ya Kai kimanin shekaru 5, hakan ne yasa aka sata a SS 3 Safiyya Kuma da Yesmin a SS 2.
Tun ranar labaraba suke event, friends day,fulani day,sai bridal shower,sai yau da ta kasance Saturday aka d’aura auren Diyya da Hashim Akan sadaki naira dubu hamsin,bayan an d’aura akayi bud’an Kai a gidan su Amarya, a lokacin abmar hall na tashe a garin Gombe, Nan suka Kama don yin dinner, Asiyah, Safiyya da Yesmin Shiri suke don zuwa wurin dinner.
Faysal ne yaje d’aukan su, Farees kuma yana tare da ango, Basu d’au lokaci mai tsawo ba suka isa akan high table suka zauna, Hashim ga Amaryar sa nan a gefen sa amma hankalin sa na Kan Asiyah, fili aka Bud’e wa ango da Amarya suka nuna farin cikin su yayin da Yan uwa da abokan arziki suke musu liki, su Fadeelah sune kirjin biki ita a Lallai auren kaninta ne.
Kiran wayar da akayi wa farees ne ya sa shi fita, Bai dad’e ba ya dawo ciki da saurin gaske kana ganin sa kasan hankalin sa a tashe, magana yayi wa Hashim a kunne a zabure ya mike,hatta Diyya da ta ji abinda yace ta Mike tana ambaton Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un, Faysal,Hashim da Farees sukayi waje da gudu, su Asiyah suka nufo Diyya suna tambayar ta, ji nayi Asiyah ta fashe da kuka naso Jin maganar da sukayi Amma karar kid’an ya hanani ji, sai gani nayi Amarya ta fice da sauri Suma duk suka bi bayan.
Mc yace “To Allah Yasa lafiya,tunda Wanda ake taron don su sun watse ina ganin ai gara mu tashi muma,kashe kid’an akayi sai surutai kake ji kowa na fad’an Albarkacin bakin sa.
Sunyi sa’a su Hashim Basu tafi ba,babu Wanda ya tsaya magana suka lodo a mota, kasantuwar motar Jeep CE shiyasa ya d’auke su, hashim ke jaan motar, a guje ya fizgi motar suka bar haraban hall d’in.
????????????????????????????????
Wa ya Kira Farees?
Me aka ce Masa?
Meya tsoratar dasu haka?
Kuma ina zasu je?
Milhat ce kad’ai ke da amsar wannan tambayoyin,ku kasance tare dani don Jin amsoshin tambayoyin Nan.
Milhat ce
Yar Terawa
Please comment and share
[ad_2]