
Sai da Jiddatou tashekara biyu da rabi lokacin Aisha ta yayeta,tana yawo ko ina,sai ga Zarah tafara laulayin ciki.
Murna wajan Aisha kamar itace keda cikin,Ibrahim yanuna farin cikin sa,amma ba kamar cikin Jidda ba.
Zarah ko andena sa riga sai ɗaurin ƙirji,tun kafin ciki yafito ake turo ciki,tsurfa kala-kala,kilibi-bi iri-iri,kitifi ba wanda batayi.
Watan ta tara da kwanaki ta haifo ƴarta mace itama mai kama da ita,Ibrahim yayi hidima amma bakamar haihuwar Jidda ba,hakan ya ƙulal da Zarah,a tsakanin ne Aisha ta fara sabon laulayin ciki,ran Zarah yayi matuƙar baƙi.
Tunda Aisha ta ɗau cikin nan yau lafiya gobe ciwo,ba mai kula da ita gashi ƴarta batavda wayon yin abubuwa haka take cijewa ta daure tayi ayukan gida harda na Zarah.
Watarana ciki dare naƙuda ya taso mata,gashi Ibrahim baa ɗakinta yake ba,gashi bata isa ta je ta buga musu ba tasha zagi,tayi matuƙar galaibaita tafita hayyacinta.
Jidda ko baccinta kawai take batasan maike faruwa ba.
Tun Aisha na iya motsi har tazo bata iyawa.
Ko da safe tayi Zarah sai ƙwala mata kira takeyi tajita shiru ban kaɗo ƙofar da zatayi ta iske ta kwance male-male cikin jini ga ɗa yafito babu mai motsi cikin su,ga Jidda nacan na bacci.
Wani mugun ƙara ta sake wanda yai sanadiyan tada Jidda daga bacci a firgice,Ibrahim ya fito daga make wayi ya yarda buta yana tambaya lafiya.
Zarah ko komawa tayi ta zauna daɓas tana kurma ihu,kan kuce mi gida ya cika sa mutane.
Hankalin Ibrahim yayi ƙololuwar tashi,take aka kaita asbiti aka tabbatar musu da rai yayi halin sa.
Dawowa akayi da ita aka kai mata sutura aka kaita gidan ta na gaskiya,bayan share zaman bakwai ƙanwar Aisha taso ta ɗauketa Ibrahim ya hana,haka Ummie taso ta ɗauketa Ibrahim da suke kira da Abba ya hana,alokacin ne suka yanke shawara da ɗan uwan shi Abdullahi da matan shi Ummie na haɗa auran Jidda da Aliyu,basu ko bar garin nan ba saida aka ɗaura aure,bada sanin Zarah ba,daga dangin Aisha sai Abba a ɗan shagon ƙofar gida sukayi cikin sirri .
Ummie taso ta tafi da ita tasata makaranta amma ina Abba ya hana,yace sai in zata tare yasata anan gaba,ai bokoko a wuta ne,miye amfanin bokon mace.
Ahaka suka tafi suka barta,bada son ran Ummie ba,lokacin Aliyu yana india yana karantun shi,bai san wani wainar ake toyawa ba.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya ba daɗi ɓangaran Jidda don tun tana ƙarama ta ke amsan gasashiyar gyaɗa a hannun Zarah ,bayab haihuwar Atiƙa zarah ta ƙara haihuwar Sa’ina.
Ta sangarta su sosai bata son mai zai taɓa su,gashi sun rainata tun suna ƙanana suke zaginta,basa ganin girman kowa.
Jiddatou ko wuni takeyi yawon talla na safe daban na rana daban na yamma daban.
Uƙuban rayuwa ba wanda bata ganshi ba.
Lokacin da takai minzilin girma,ana ta tururuwan nema auran ta,amma zarah ta hana,tace ita da aure sai bayan ranta,rayuwar JIDDATU a tallatan zai ƙare.
Kwatsam aka kira Abba aka sanar dashi mutuwan ɗan uwan shi tunƙwal guda ɗaya,sanadiyar haɗarin motor zuwa kaduna,wajan ɗaurin auran ɗan abokin sa,ya shiga tashin hankali,sosai na rashin ɗan uwan sa,da ƙyar ya dawo hayyacin sa,don Hajiya Asma’u tafishi jarumta da take,haka aka share zaman bakwai,
Lokacin Aliyu har yagama bautan ƙasan sa yasamu aikin bank UBA,kuma sun haɗu da wata yarinya Abeeda ɗiyar ɗan babban kasuwa Manmadu Sharif mai goro,suna soyayya sosai da son junan su kamar su lashe junan su sabida ƙauna.
Ko kaɗan bata son ɓacin ran Aliyu.
Dayazo ma Ummie da buƙatan auran Abeeda,tatuna masa da yana da wani aure fa a ƙauye in ya matanta ya tuna.
Aliyu shafa ma idon shi toka yayi yanuna baisan da wannan labarin ba,kamar sa ace yazauna da ƴar ƙauye,shi yama Abida alƙawarin bazai mata kishiya ba,kuma bai son ɓacin ran ta.
Ummie taji matuƙar baƙin cikin maganan Aliyu,amma ta danne zuciyarta tanuna mai ba komi,taje ta samu Ibrahim a ƙauye,yaji takaici,amma sanin halin ɗan yau yasa ya daure ma zuciyar sa,shiyaje yanemo ma Aliyu auran Abeeda kuma ya amso masa auranta.
Ko sati baayi ba suka fara samun matsala da Abeeda
Abeeda kwalliyan wajene amma bata iya komi ba,bata iya ladabin kula da miji ba,shigo-shigo ba zurfi tayi masa sam bai gane waye ita ba sai bayan aure,satin su uku tafara laulayin ciki,ta tada rashin mutunci sai de acire ita haihuwa ba yanzun ba,bata son ta tsufa da wuri,ga Aliyu nason haihuwa da siɗin goshi ya shawo kanta ta bar ciki,da tatashi haihuwa ko aiki ta sa akayi mata,wai ita batason wahalan naƙuda ta mutu bata gama cin duniyarta da tsinke ba ba,anko ciro mata ƴa mace,in Aliyu farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha,haka Ummie ranan suna taci sunan Ummie watao Nanah Asma’u,Nany aka ɗauka don kula da Nanah wanda Aliyu ke kiranta da Cutie ,bata samun kulawa sam wajan mahaifiya,ko arzikin nono bata samu abata saide tasha madaran yara,Nany ko sabida wulaƙancin Abeeda basa ko daɗewa suke guduwa kawo wasu da haka har Cutie ta girma tayi wayo yakaita school sam bata samun kulawa wajan Abeeda.
Abubuwan Abeeda kullum ƙara yawa yakeyi,Aliyu ganin ta yakeyi kamar mai aljanu wani lokaci,sam bata waiwayen bayanta.
Tun daga lokacin da Aliyu ko yayi aure Abba yasa maka sa damuwa harta kai shi da rasa ɓarin jikin sa,jinin sa kullum hawa yakeyi ,gashi babu mai temakon sa ZARAH ce ta zama mijin inko Jidda batayi talla ba baza suci ita da baban taba saide su zauna da yunwa,ZARAH da ƴaƴanta ba mai zuwa duba Abba Jidda ke hidima dashi
Ƴaƴanta ko ba wanda yanzun ba’a kawo kayan nagani ina son shiba,duk da suna yawo ba ma maza haɗin kai acikin gonaki ba komi bane a wajan su,basa ganin mutuncin kowa harda na uwar tasu,bata isa tasa a ayi ba kuma bata ta hana ba su hanu ba
WANNAN KENAN,ATAƘAICE,A GURGUJE
Ɓangaran Abeeda shirin zuwa katsina biki kawai akeyi.
MORE COMMENTS
MORE TYPING
typing????️
????JEEDDATOU????
NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI
JIDDATOU
MALLAKIN:- (THE CAT LOVER????????)
(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo
WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE
SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU
PAGE76&80
BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM
_????Ɓangaran Abeeda shirin zuwa katsina biki kawai takeyi yayinda Aisha zugata kawai take tana cewa itama zataje.
Bata damu da ta gaya ma Aliyu ba,ko ta kan shi bata bi ,in sun haɗu a get ne zai fita zata shigo ko zai shigo zata fita.
Ɓangaran Abba yana samun kulawa sosai daga wajan likitoci da Aliyu,alhamdulillahi sauƙi na samuwa,jikin shi na motsawa ta dalilin gashin ƙashin da yake samu daga ƙwararrun likitoci.
“Jidda zaki iya gane asbitin da Ibrahim ke kwance?.
Faɗan Ummie da take zaune kan luntsa-ts-tsun kujeru falon ta.
Tana sanye cikin riga da zani mai launin purple da pink ɗinkin dogon riga ta kashe ɗaurin Aisha baban gida,wani abun sai wanda ya gani.
Cutie na zaune gefeta ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana sanye da wando jeans blue da riga yellow an gyara mata gashin kanta.