
Jidda na zaune daga ƙasa can gefe daga ƙasa,Ummie tayi-tayi ta hau saman kujera taƙiya.
Girgiza kai tayi alaman aa,kafin tace,”aa Ummie so ɗaya mukaje”.
Ummie ɗaukan wayarta tayi dake gefe,don rabon Aliyu da gidan watou fushi yake da ita daga mai faɗa.
Lalubo number shi tayi ta buga masa kira,ringing biyu ya ɗaga,bata amsa sallaman da yake mata illa cewa datayi kazo gida yanzun nan ina son ganin ka.
Bata jira mai zaice ba ta datse wayar.
Ajiyan zuciya Aliyu ya sauke mai nauyi,gaban shi na faɗi, yana tunanin mai kuma yayi.
Gama haɗa takaddun dake gaban shi yayi yasa laptop ɗinshi acikin breif case ɗin shi ya kulle ya kwashi wayar shi da key ɗin motor shi ya fito yana rataye breif case ɗin a kafaɗan shi.
Biyawa yayi gidan abinci yasaya yanufi asbiti yakai ma Abba yasamu jikin nasa saide ace alhamdulillah.
Gaisawa sukai Abba yana ta shi masa albarka yana amsawa cikin jin daɗi.
“Ali,ina ƙanwar Jidda kace mata ina kewar tA”.
Faɗan Abba dake zaune tsakiyan gado ya jingina da bango.
Wani nauyi da kunya Aliyu yaji ya rufe shi,yakamata ko ya kawo JIDDA gidan ma bai samu zuwa ba sabida abubuwa yayi mai yawa.
Murmushi yayi a zahiri yace,”Abba suna gaisheka ifa da Ummie da Cutie,yau ma Ummie tace zan kawo su”.
Yagaya masa haka ne don bai sanmai zaice mata.
Allah sarki Maa’u ina amsa faɗan Abba.
Murmushi yayi Aliyu yamiƙe yai masa sallama yace zasu zo anjima.
Kai tsaye gidan Ummie ya nufa ,a falo ya iske su suna kallo a tashan zeeworld.
Bayan yayi sallama sun amsa,ya gaida Ummie,Cutie ta gaida shi kafin Jidda ta gaida shi,ya amsa cikin kulawa.
Zama yayi agefe Cutie yana riƙo hannun ta,amma hankalin shi yana wajan Jidda yana wani satan kallon ta.
Ummie kula da tayi da haka yasa ta tawani haɗa rai tace,”Jidda ,Cutie ku tashi ku shiga ciki mangariba ta ƙarato”.
Bako musu tatashi jikinta asanyaye ta matso inda suke zaune ta sa hannu zata Cutie na zare hannun ta jikin Aliyu ta miƙa ma Jidda hannun ta.
Riƙe mata hannu tayi suka nufi hanyar bedroom ɗin su.
Zazzare ido Aliyu yaketayi kamar yayi ƙarya.
“Sannu Aliyu nikake fushi dani,don nayi ma faɗa”.
Faɗan Ummie da take kallon sa.
Murmushi yayi ya kwanto kan kafaɗan ta cikin shagwaɓa yace,”Ummie ba haka bane,ayyuka suka min yawa,wa ƴanda kwana biyu banyi ba a office,wallahi kuna raina”.
Ƙwafa tayi kafin tace,”ni ɗaga ni karka karya ni ,ƴarka ta haumin jiki kaima kazo duk so kuke ku karya ni”.
Murmushi yayi tare da ƙara shigewa cikin jikin ta yana ƙyalƙyale dariya.
Ran ƙwashi ta buga masa akai,da sauri ya saketa yana sosa inda ta buga masa ran ƙwashin.
“Wani asbiti Ibrahim yake?.
Ta tambaye shi tana kafe shi da ido.
“Ummie Uduth yake fa”.
“Shine baka ji zaka iya gayamin ba?.
“Ummie dama zan kaiku anjima ku shirya”.
“Tou Allah yakai mu,kaima Allah yama albarka”.
In banda wulaƙanci taya bayan shekara goma da kuka kawo tsiyan auran ku zaku dawo kuce abaku abinku,gaskiya bazai saɓu ba bindiga a ruwa……..!
MORE COMMENT
MORE TYPING
typing????️
????JEEDDATOU????
NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI
JIDDATOU
MALLAKIN:- (THE CAT LOVER????????)
(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo
WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE
SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU
PAGE81&85
BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM
_????In banda wulaƙanci taya bayan shekara goma da kuka kawo tsiyan auran ku zaku dawo kuce abaku abinku,gaskiya bazai saɓu ba bindiga a ruwa”.
Faɗan Zarah da take tsaye tana ta girgiza-girgize kamar bishiyan ceɗiya,tana wani fusgo masifa,masifa na fisgenta,kunga matan nan masu kamar goran bobo masifa a jinin su take.
“Mtsewww ku at ciki,da hankalin mu baza mu ɗauka gurɓatacce fura musa a cikin muba,don haka mun baku sati ɗaya kudawo mana da dukiyan auren ɗanmu”.
Faɗan wata mace siririya doguwa,itama cike da masifa take maganan.
“Ladi wallah bazamu dawo dasu ba,aure babu fashi,in kunga ko baayi auran nan ba sai bayan raina”.
“Tou matsiyaciya da ranki ko zaki ga mun rusa shi,ina zamu ɗau ƴar iska lalatatta mukai zuri’an mu,zuri’an muko ba lalatacce baragurbin ƙwai”.
“Ladi kika ƙara cema ƴata ƴar iska sai nayi ƙasa-ƙasa dake,ai ko ubanta bai isa ya hanata ba,don shima da gindinta ya ganta”.
“Ahhh Zarah dama nasan da ɗaurin gindin ki take aikata duk wata tsiya kwararo-kwararo,don haka baza’a kwaso ƙanjamau a ƙa-ƙaba mana ba”.
“La’ilafi ƙafa dubu,mai bakin karnuka,baa ce ɗanku keda ƙanjamau ba da suke zuwa hausa,duk ƴaƴan arna sun gama lalata dasu sai ƴata da ko sokoto bata taɓa zuwa,kenan illela bata sanshi ba,duk iskancin ta iyakan ta ƙauyen nan da gida fura,da ɗanboka,da su lakoda da iddirawa,da sagera”.
“Wallahi Zarah kinyi asaran rayuwar ki,kinzo duniya a banza haka zaki koma a banza keda ƴaƴanki,jakar gidan ki tafiki hankali da tunani,kina uwa amma kina alfahari kina gaya ma duniya ƴarki na yawon iskanci?.
Faɗan Larai maƙwafciyan su,da tun ɗazun tana sauraran hayaniyan dake faruwa,duk maƙwafta suna ji,amma ba wanda zayi magana ko yabada haƙuri gudun cin mutuncin Zarah.
Sheƙeƙe Zara ta kalleta tawani taɓa baki tafa hannu tayi tace,”tou maziga maƙwan gara masu zuwa lahira daƙoƙan dambu,munafukai kunan ku na gidan mutane kuna sauraran abinda ke wakana,ina ruwanki Larai,munafuka,kowa da guntun kashin shi a gindin shi amma ya take ya rinƙa hango na wani”.
“Gaskiya ko inzaki mutu sai na faɗa miki donni bani tsoronki bani munafurci”.
“Ki riƙe gaskiyan ki annami-miya,banso”.
“Dama bance kiso ba,matsitaciya mahaukaciya jakar da kike kiwo tafiki tinani”.
Nan fa faɗa ya koma kan Larai,sukai ta zuba ruwan masifa,su Ladi ƴan kallo suka koma,da ƙyar surukan Larai suka jata zuwa gida,don abin nanema yakai ga dambe.
Ladi ko wucewa sukai ita da Sabuwa suna jaddada ma Zarah zasu dawo tanemo musu duk abinda ya kawo da abinda yakashe mata.
Zarah wuni tayi tana zage-zage ranan a ƙauyen,daga ƙarshe shirya wa tayi ta nufi gidan aminiyarta Abu,don neman mafita da shawara.
Kamar yanda Aliyu yace ko bayan mangariba nayi ya,duk sun shirya,yanadawo wa sallah ya ya iske su afalo shi suke jira,dukkan su suna sanye cikin shigar abaya,don Aliyu abaya yasayo ma Jidda don yana matuƙar son abaya,duk yawanci in zai sai ma Abeeda kaya abaya yake saya mata,kafin yasai mata atamfa yana jimawa ko leshi,amma duk wani sabon style na abaya sai yasayo mata shi,yana son mace ƴargayu,amma kashe gayun Abeeda yayi yawa bata iya tsinana ma kanfa komi sai gantali,ɗan gajeran tsaki yaja a ƙasan zuciyar shi,a zahiri kuwa murmushi ya sake yana ɗaga Cutie sama da take sanye cikin blue abaya yayi matuƙar mata kyau Ummie ko nata baka ce tayafa gyalan akai,Jidda ko nata yellow ce duk da rashin wayewa da iya kwalliya ta ɗanyi kyau,itama gyalen tayafa akai.
Cutie ƙyal-ƙyalewa tayi da dariya tace,”Dady nafara gilma kar ka yaddani”.
Dariya Aliyu ya sake yana dungurinta a goshi yace,”ina girman yake?