MIJIN BABATA NENOVELS

MIJIN BABATA NE

MIJIN BABATA NE COMPLETE

PAGE91&95

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

WANNAN SHAFIN TUKUYCINE GAREKU,:-AUNTY JAMILA ALIYU,MAMAN FARISA,DA MAMAN ABUBAKAR,INA JIN DAƊIN COMMENT ƊINKU SOAO ALLAH YABAR ZUMUNCI DA ƘAUNA????????????

_????Daga ganin Abun watsa-ts-tsa ce kalar Zarah mara mutunci.

Kyaɓe baki Zarah tayi tace,” nifa bana son harkan bokaye nafi gane a watse a rashin mutunci ,ayi tsiya a dai-daita nafi gane wannan yaren”.

“Tsiyata dake fa sakaryace Zarah,ana nuna miki hanya ɓullalla kina bin lungun da bazai ɓulle dake ba,mtsewww,ni tashi kibar min gida tunda bazaki ɗau shawarata ba”.

Abu tai maganan cikin ɓacin rai tana turo kallabi gaba.

Zarah washe jajayen hauru tace,”haba ƙawalliya,na amince gabe daka sammako zanyi inzo mutafi”.

Abu washe itama haƙora tayi tace,ko kefa ƙawalliya,sai an raba shi da har uwar shi,saide tsinannun su zama ƴan kallo,ki tabbata kina da kuɗi sosai don ke zaki min kuɗin mashin”.

“Ai ke daɗina dake son banza,kina da kuɗi kina ɓoye shegen wayo kamar bulbuli”.

Tana magana tana galla ma Abu hararan wasa.

“Ina ruwana ai lalurat ki ta ba nauna ba,in bakiyi ai shikenan”.

“A’a aminiyata zanyi mana”.

Nan sukai ta shirya yanda zasu tafi daga ƙarshe tai ma Zarah rakiya tatafi.


Ɓangaran Abeeda kuwa tun da safe ta tashi tai wanka ta shirya,ta riga ta gama shirya a kwatin ta tsafff duk abubuwan da zata buƙata ta haɗa ta saka,shirya tayi cikin abaya blue tasa takalmi fari,tayafa ,ta kwashe wayoyinta da key ɗin motor ta taja akwati ta fita,ba tare da tinanin komi ba.

Abayan motor tasa akwatin ta kafin tashiga motor ta fice a gidan ta harba motor ta kan titi takama hanyar katsina ba tare da fargaban komi ba.


Zara ko washa gari da sasaafe suka daka sammako,ba sallah ba salati,ba wanke ido balle ɗauraye ƙafa,mashin guda suka hau suka kama hanyar masallata.

Koda suka isa sun iske layi waje suka kama suma kafin azo kansu.


Gudu take tsalawa sosai,kamar na miji,sai da ta isa gusau kafin ta tsaya tasai tsire da drinks taci kafin taci gaba da tafiya tana tsala gudu abinta,tana zuwa funtuwa ta ɗauke hanyar katsina ko tsoro babu atattare da ita.


06:30am Jidda ta tashi Cutie tai mata alwala,tasa mata hijjab tayi sallah,bayan ta idar tai mata wanka ta ta gyara mata suman ta ta shafa masa mai har ƙyalli yake yi kama mata tayi acan ƙasan kai kafin ta shiryata cikin school uniform ɗinta,tasa mata safa da school shoe ɗinta.

Cutie taɓa kanta tayi ta turo baki gaba kamar na ZEE YERO,tace,”Aunty a shushi maza ne zakimin kalan na senior ɗin school ɗin mu”.

Jidda zaro ido tayi tana murmushi tace,” aa kibar shi haka kinfi kyau,minene senior Cutie?.

Ta ƙarashe mata maganan da sigar tambaya.

“Senior manya makarantar mu nake nufi ,zance Dad yasaki makarantan mu”.

Murmushi tayi tana jan hancin Cutie tare suka saka dariya.


Agaggauce yafito yana ɗaura agogo a tsintsiyar hannun shi,yana sanye cikin kaftan yadin mai launin blue,hulan kanshi baƙi haka takalmin ƙafar sa,kafaɗan sa rataye da brief case ɗin sa,sauri yake yaje ya ɗauko Cutie ya aje ta amakaranta don suna da meeting ƙarfe takwas dai-dai,yaga bakwai ta gota

Da mamaki yake kallon parking space ɗin ganin babu motor Abeeda watou bataji maganan sa ba ta fitan kenan tatafi katsina take yaji ranshi ya ɓaci,ƙwafa yayi yashiga motor shi ya fice.

Hon ya buga ,dama haka yakeyi bai shiga in yazo ɗaukan ta gudun ɓata lokaci saide yayi hon ta fito.

Aiko yanayin hone ta ɗau lunching box ɗinta ta fice da gudu,ba tare da ta ɗau jaka ba.

Jidda ɗaukan jakan tayi tabi bayanta,lokacin har yabuɗe mata motor ta shiga,ya ansa lunching box ɗin ya aje a gidan baya,kiss ta manna masa a goshi tana fara’a tace “morning dad”. ataƙaice tayi maganan.

“Morning too,ina school bag ɗinki?.

Yai mata maganan yana kafe ta da ido.

Ɗan zaro ido tayi tana dafe goshi tace,” Dad i forget it,bari inje in ɗauko”.

Bata jira mai zaice ba ta buɗe murfin motor,daidai lokacin Jidda ta ƙaraso.

Komawa tayi ta kwanta jikin kujeran tace,”yauwa nagode Aunty” .

Jidda aje mata jakan tayi akan cinya,ta kai kallon ta kan Aliyu da shima ita yake kallo,idon su sarƙewa yayi ana juna,kallon ƙuda suke ma juna,yayinda wasu kibiyoyi ke fita daga idon junan su yana shiga na ɗaya.

Ƙirjin Jidda matsanan cin bugu yakeyi kamar zai fita da sauri tace,”ina kwana”,cikin sanyin murya.

Da sauri ta juya ta rufe ƙofar motor tabar wajan don jitake ƙirjinta naneman fasowa tafito,bata san miyasa takejin wani yanayi ba da zaran ta ganshi.

Sauke nauyayyan ajiyar zuciya yayi don take jikin sa ya mutu,yima motor key yayi suka fice,jikin sa a sanyaye,tafiya kaɗan ya ajeta a ƙofar school ɗinsu yatafi office,yaso yaje ya duba Abba amma yayi latti ,zai kira Ummie tasa driver yakai musu abinci.


Ta isa cikin garin katsina ƙarfe shaɗaya da ƴan mintoci,takira Na’ima ta hayo abin hawa tazo ta ƙarasa da ita unguwar su,duk ƙawayen su ƴan duniya suna wajan da wanda tasani da wa ƴanda bata sani ba,”Aisha bata ƙaraso bane?.

Abeeda ke tambayar Na’ima

“Eh bata ƙaraso ba,wayoyin ta duk kashe ko online yau banganta ba Allah yasa lafiya”.


Aisha ko da gan-gan ta kashe wayarta don karsu dameta da kira,ta sami matsala da mijinta,don ko labari zuwa biki bata kawo masa ba,don tana mugun tsoran sa da shakkan sa,biki in ba na ƴan uwanta ko dangin ta ba,ƙawaye bakowa yake bari taje bikin shi ba,sai wanda ya gadama zataje, balle bikin ƙanwar ƙawa,har katsina,aibata isa ba.


Su Zarah sunga boka,tun kafin su faɗa mai yakawo su ya zayyana musu,kuɗin aiki ya buƙata su biya su tafi kawai zasu ga aiki ,aiko tabiya suka dawo gida.


Tun Abeeda nasa ran ganin Aisha harta cire rai,sai gwada number ta takeyi akashe daga ƙarshe haƙura tayi,don har anfara shirin zuwa mothers day,shiryawa sukai ,mai makeup tai musu makeup suka tafi duk sunci anko light pink,basu suka dawo ba sai shabiyu saura.

Agida maƙwaftan su suka sami wajan kwana don gidan su Na’ima yacika sosai ba masaka tsinke.

Ƙarfe ɗaya da wani abu unguwan ta karaɗe da harbe-harbe kota ina,hankalin mutanan unguwan yatashi sosai,sun san tabbas anzo ɗaukan wanine,unguwar masu garkuwa da mutane sun addabesu baa wata baazo musu ba,hakan yasa wasu suka tashi,Abeeda ko motsi batayi ƙwaƙwara don tashin hankali iya tashin hankali ta ganshi

Gidan dasu Abeeda suka sauka nan suka fara shiga ko suka taso kan mutanan dake gidan tassssss sai wata mai ciki da sukai sukai ta tashi tace bata iyawa saide su kasheta awajan,bugun tsiya sukai mata suka barta awajan suka fita suka faɗa gidan su Na’ima nan ma ba wanda basu tarkata ba,sai wata tsohuwa,gida biyar suka kwashe mutane,basu sukabar unguwan ba sai asubah,suna bari police na zuwa,Abeeda kuka kawai takeyi………..!

TO HWA KO ƘAƘA OHO????

MORE COMMENTS
MORE TAHIN????
typing????️

~*Lokaci yayi da zaka daina mamaki akan butulcin mutum, kowa zai iya butulce maka, kowa zai iya cin amanarka, kowa zai iya v, labule idan babu shi za kaga komai na ɗaki, murmushi idan babu shi za kaga mummunan kuɗirinshi????????*~

????JEEDDATOU????

NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI
JIDDATOU

MALLAKIN:- (THE CAT LOVER????????)

(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo

WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button