MIJIN BABATA NENOVELS

MIJIN BABATA NE

MIJIN BABATA NE COMPLETE

SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU

PAGE96&100

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

_????Basu suka bar unguwar ba sai asubah,suna bari police na zuwa,Abeeda kuka kawai takeyi,tun baa kai ko ina ba ta fara tarin da ta sani,ɗaya daga cikin masu kama mutanan yasame ta ya buga mata gindin bindiga ,take ta faɗi ƙasa wanwar,aiko ruƙo hannun ta yayi ya fara janta a ƙasa kamar dabba.


Bayan sun fito daga meeting office ɗin sa ya koma yaje ya duba wasu files namasu sa hannun jari a company su na motor,daga bisani ya miƙe ya kwashe kayan sa ya nufi asbiti inda Abba ya duba jikin Abba alhamdulillah har ban ɗaki yake iya zuwa da kanshi,sun daɗe suna hira kafin yai musu sallama ya wuce.

Kiran Jabeer abokin sa yayi ya tambaye sa ya samo masa lesson teacher yace masa eh yace tou yana gidan Ummie yazo dashi.

Kusan atare suka ƙarasa gida Ummie da Jaafar,da Teacher da aka samoma JIDDA,sai da sukayi maganan kuɗin wata,ya rubuta masa takaddun da zai sai mata,kafin ya kira masa JIDDAN ya ganta,Jabeer tunda yaga Jidda yaji ya faɗa ƙaunar ta,kallo ɗaya bisa ƙa’ida yai mata yaji tatafi dashi kalan matan da yakeso tana da natsuwa sosai da kamun kai daga ganin yanayin ta.

Bayan ta wuce ne Jabeer ya kalle Aliyu yace,”abokina,wannan ƙanwar tamu tayi min fa”.

Take ƙirjin Aliyu ya buga dummmdummm,yanayin shi na ƙoƙarin canjawa,amma yajawo jarumtar shi ya dake ya ƙaƙalo murmushi akan fuskan shi,ɗan sosa ƙeyan sa yayi yace,”kai fa Jabeer ɗan iska ne,duk inda kaga mace so kake,wannan tafi ƙarfin ka karatu zatayi”.

Dariya Jabeer ya sheƙe dashi kafin yace,”abokina wannan natsuwar ta tamin wlh auranta zanyi”.

Wani tuƙuƙun abu kamar dutsi ya tokare zuciyar Aliyu wani baƙin ciki yaji da Jabeer yace auranta zaiyi.

Ɗan taɓa baki Aliyu yayi kafin yace,”sai kuma kayi”.

Yai maganan a taƙaice.

Jabeer ganin Aliyu bai son maganan yasa ya watsar da alwashin sai ya sace zuciyar yarinyar da tashi salon batare da Aliyu yasani ba,kan ya farga ta faɗa ƙaunar shi dole ko abashi ita.

Ɗan taɓa hira sukai kafi sukai ma Aliyu sallama,suka shiga motor Jabeer suka tafi,sun tsaida magana gobe mallamin zai fara zuwa.

Ciki ya shiga ba kowa a falon sai ƙaran AC da ya ɗau sanyin da ya gauraye da wani daddaɗan ƙamshin turare da aka turara gidan dashi,lumshe ido yayi,kai tsaye bedroom ɗin Ummie ya nufa,tana zaune kan kushim tana waya,zama yayi gefenta,sai da ta ƙare ya gaisheta ta amsa.

Bayani yai mata gobe zaa fara zuwa koya ma Jidda karatu,taji daɗi tayi murna sosai sai saka masa albarka takeyi.

Zama sukayi jimmmm daga bisani yakauda zaman shiru yace,”Ummie na sake Abeeda sam bazan iya zama da ita ba”.

Arazane Ummie take duban sa tana salati da sallamewa tana tafa hannuwa.

“Aliyu mai yai zafi haka?.

Ta tambaye shi tana riƙe baki.

Muskutawa yayi yace,”Ummie tun baya nazo nagaya miki damuwa ta,kika nuna halin ko in kula tou yaya kike so inyi,zan iya zama da ko wacce mace koda ɓarauniya ce,amma banson mace mai yawa,Ummie na ƙyaleta tana yawo cikin garinan bance mata komi,ban isa ma ta gaya min zata fita ba,sai lokacin da ta gada ta dawo Ummie,har yakai Abeeda da tafiya katsina bikin ƙanwar ƙawa”.

Cike da takaici yake maganan kamar zai fashe da kuka.

Cike da mamaki Ummie tace,”bikin ƙanwar ƙawa kuma har katsina?.

“Eh Ummie,bari in gaya miki yanda mukayi jiya”,nan ya kwashe komi ya faɗa mata.

Girgiza kai Ummie tayi tace,”Aliyu miyasa ka kulata,gaskiya banji daɗin al-amarin nan ba,Abeeda da kamar bazatayi ba”.

“Ummie ta fitar min arai kwata-kwata,Ummie don Allah ki tallafa min ki agaza min wallahi ina son Jidda tun ina ƙarami kibani matata Jiddah”.

Yai maganan yana wani fashewa da matsanan cin kuka.

Daidai lokacin Jidda ta turo ƙofa hannun ta cikin da Cutie a sanyaye suka shigo,bayan sun gama jin duk maganan da Ummie da Aliyu sukeyi.

Jidda duƙawa tayi gaban Ummie,Cutie ma haka.

Jidda ƙasa tayi da kanta cikin sanyayyar murya tace,”Ummie kinga fa yana kuka,dama ni matar Yaya ce,Ummie in dagaske ne abinda naji Ummie ki temaka zan zauna dashi,koda kuwa baya sona,ni ina son shi.

Daga Ummie har Aliyu da take kukan shi ya tsaya cakkk cike d mamaki suke kallon Jidda.

JIDDA ko ɗago kai tayi taga duk sun zuba mata ido yasa tai ƙasa da idon ta da sauri,karde maganan dake zuciyarta tayi suɓul da baka yafito fili.

“Ummie kinji ko tana sona zata zauna dani”.

Ummie ko mamakin yahanata magana.

Da ƙyar ta iya cewa kutashi ku ɓace min daga gani,watou kafin ya shigo sai da ya zigo ki ko Jidda kizo gabana kimin rashin kunya”.

Yace wallahi Ummi ni ban……..!

DAGA WANNAN SHAFIN NADENA POSTING AKO INA MASU MIN COMMENTS KAWAI ZAN SA SU A SABON GROUP ƊINA DANA BUƊE
typing????️

????JEEDDATOU????

NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI
JIDDATOU

MALLAKIN:- (THE CAT LOVER????????)

(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo

WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE

SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU

PAGE101&105

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

_????Yajima yana tunani iriiri da tarin dana sani kafin bacci ɓarawo yai awan gaba dashi.


“Wai Aliyu lafiya har 08:00am ta gauta bai zo ya ɗauki yarinyar nan ba ina ta kiran wayan shi tana ƙara baa ɗauka”.

Ummie ce ke magana tana ƙara danna kiran number Aliyu.

Jidda na zaune daga can gefenta,yayinda Cutie ke kan cinyarta.

Ummie ɗagowa tayi ta kalle Jidda tace,” kaita wajan Adamu driver ya kaita”.

Tou Ummie Jidda ta amsa a taƙaice,yayinda ta sauke Cutie ta ɗau lunch box ɗinta da jakan ta suka fita.


Aliyu ko bashi ya farka ba,sai to 11:00am,daƙyar ya miƙe yai wanka kansa na sarawa,cike da mamakin baccin da yayi,sallah asubah ya gabatar a gurguje,yajima ya adduan Allah ya sassauta zuciyar Ummie akan sa,kafi ya tashi ya sauya kaya ya feshe jikin sa da turaruka,ya fara neman waya da key ɗin motor bai gani ba.

Agurguje yafita waje ya duba ya hango motor shi a haraban gidan parking ɗinma gata ga kamar ta.

Buɗe murfin motor yayi a kulle,tou ina ya aje key da wayoyin sa,yake tambayan kansa a cikin zuciyar sa.

“Yallaɓai barka da kwana”.

Baba mai gadi ne duƙe a bayanshi yake biƙa gaisuwan sa wajan ubangidan sa.

Dafa goshi Aliyu yayi,kafin yace,”Baba bana son duƙawar nan,dan Allah tashi”.

Baba mai gadi miƙewa yayi yana murmushi,tare da sa hannu agaban aljihun rigar sa yaciri key,ya miƙa ma Aliyu,yace,”Alhaji jiya kabar motor a kunne,naga baka ƙara fitowa balle ka kulle ba,nai karambani nasa Salim ɗan Alhaji Sada nan maƙwafcin mu da yake zuwa miyi hira ya kashe yaban key ɗin”.

“Allah sarki Baba aiko nagode”,an san key yayi ya buɗe motor,har Baba zai juya yace,”tsaya Baba,Babako daga jin haka yasan kakan shi ta yanke saƙa,Aliyu akwai kyauta.

Kuɗi ya ɗebo,da baisan yawan suba ya miƙa ma Baba,Baba amsa yayi yana ta zuba masa ruwan godiya da addua kala-kala.

Ameen kawai Aliyu ya amsa dashi,yaja murfin motor shi ya rufe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button