MIJIN BABATA NENOVELS

MIJIN BABATA NE

MIJIN BABATA NE COMPLETE

Ran Zarah bai mata daɗi ba,sanda taji Abba ya ƙara aure,tai alƙawari sai tako raba auran.

Bayan sati ɗaya aka wanke Atiƙa aka kaita ɗakin miji,Aliyu ya aiko mata da kayan ɗaki na birni,Abba ya ziyarce ɗaurin auran Atiƙa tayi murna an mata kayan da baa taɓa ma wata ƴa a ƙauyen ba.

Zagi da cin mutunci ba wanda Abba bai gani ba wajan Zarah bai ce mata komi ba,saida ya tashi tafiya ya dube ta cikin mutane ya danƙara mata saki ɗaiɗaya har uku,ya shige motor driver yajashi suka wuce,yabarta tana ihu tana hauka,da ƙyar mutane suka jata cikin gida.

Abba ko ranshi fesss yatafi,ji yake kamar an sauke masa wani nauyi akan sa.

Soyayya Jidda da Aliyu suke yi a ɓoye,Ummie sam bata sani ba,ta waya suke yi a fili ko halin ko in kula suke nuna ma juna.

Duk a soyayyar da suke,bai hanata karatun taba.


Hajiya Abeeda ko har yanzun bata kula kowa gani take kamar Aliyu zai dawo ya maidata ,amma gashi shekara biyu shiru ko ahanya basu taɓa haɗuwa ba.

Zarah ko shige da fice na bokaye akan Abba ya maida ta,amma duk ta gama saida tumakan ta,bokaye sun gama cinye kuɗin amma shiri,ko zanin ɗaurawa mai kyau bata dashi yanzun.

Tayi-tayi tasa Atiƙa ta saida kayan ɗakin ta taje tabi mata mallamai ta mallake mijinta da dangin ta taƙiya tace ita lafiya take zaune da mijinta bazata bayar ba Abban ta yasai mata in ta ita ne saide ta kaita da gadon kara.


“Aliyu zama haka ya isa kane mi mata kayi aure”.

Faɗan Abba da Aliyu ya kawo su Jiddah gidan.

Nan ya kwashe yanda sukai da Ummie ya faɗ ma Abba,Abba ko yace zaima Ummie magana.

Aikam yai ma Ummie magama,da taso ya bijire ya nuna mata illan haka,don Jidda matan shi ce,sai ya saketa zata iya auran wani,badon taso ba ta amince.

Sun tsada ranan biki tunda de matan shine.

Ranan biki na zuwa,akai biki isu-isu babu wani bidi’a atiƙa tazo kamar karta tafi haka takeji,Abba da kansa yakai Jidda gidan Aliyu da ya tsaru.

Satin su guda Ummie ta maida Cutie gida.

Rayuwar gidan su Aliyu da Jidda gwanin ban shaawa,suna zuwa makaranta da Cutie,Aliyu bai yarda ta kula ko wacce ƙawa ba ,iyakan ta da ƙawa aji itama ƙawarta ɗaya Jamila.

Watan ta uku tafara laulayin ciki taga gata d tarairaya wajan Aliyu da Ummie da Inna da Abba,kamar akan ta zaa fara musu haihu,aiki sai tayi da gaske Aliyu ke tafiya,cikin nada wata takwas tadena zuwa school,sabida girman da yayi jikin ta yamata nauyi sosai.

Ummie zuwa tayi ta ɗauke ta da kanta ta maidata gidan ta,don tayi tayi Aliyu yadawo da ita gida yaƙiya,saide ya dawo yaga batanan ,aiko shima ya tattara yakoma gidan Ummie.

Ranan wata talata ta tashi da ciwon naƙuda,a gaggauce aka kaita asbiti,zuwan su ba wiya ta haifo ƴan biyu duk maza.

Aliyu murna kamar zai zuba ruwa a ƙasa haka Ummie da su Abba.

Inna dawowa gidan tayi don ma Jidda wanka jego.

Inda Abba ya bugama Atiƙa waya da ƴar wayan da yasai mata,jiki na rawa taje ta gayama Zarah,Zarah kamar ta mutu,tace sai taje taga uwar uban da akeci.

Aiko ana gobe suna,suka taho,Zarah jikinta yayi sanyi sosai,yanda taga ana nan nan da ita kunya kamar ta nitse.

Ranan suna yara suka ci sunan Abdullahi,da Muhammad,anci ansha an goge wiya,anyi rabon kaya kamar ba’a so.

Zarah sakan baki tayi tana mamaki rabon kaya na kuɗi kamar baa so.

Da suka tashi tafiya,akai musu shatara ta arziki,Zarah ta fashe da kuka ta nemi yafiyar Abba,da Jidda,nan suka yayyafe juna suka tafi.


Abeeda da taga ba sarki sai Allah harta samu labari auran Aliyu da yayi na ƴar uwansa,dole ƙanwar naƙi yasa ta fito da ɗaya cikin zaurawan ta tayi aure,yana da mata uku ga tarin ƴaƴa.


Jidda sai da tayi arba’in biyu kafin ta koma,bayan sunje ƙauye sun dawo,samo mata nany akayi,don rainon ƴan biyu ga school.

Cutie nata girma tana zama ƴammata,tun tana ma Aliyu maganan Momynta harta bari.

Jidda ce tabashi shawara yakamata akai Cutie gidan kakanin ta,aiko yabi shawaranta,tare yakaita da ƴanbiyu,iyayen Abeeda sunyi murna da farin ciki,kuma yai musu alƙawari zai rinƙa kawo ta in yasamu lokaci-lokaci inya samu.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya da daɗi ba daɗi,ya zaƙi gobe maɗaci,ko haƙori da halshe suna saɓawa balle mutum.

Su Jidda suna zaman lafiya,burin su su faranta ran junan su basuso su ɓata ma junan su.

Abeeda ko ta fuskanci matsi da takura ga kishiyoyi da ƴaƴansu,ga matsalan rashin haihuwa,ta koma asbiti don a maida mata mahaifa,Dr yace bazai yiwu ba,haka ta dawo ta haƙura taci gaba da bautan ƴaƴan miji,tunda ita bata haihuwa,dole yasa ta aje girman kai ta koyi girki,ga girkin gidan mai uban yawa.

BAYAN SHEKARA BIYAR.

Wata ƴar budurwan yarinya na hango mai shekara shabiyu tare da wasu ƴan matasan yara masu shekara shidda,ta zaune tsakiyan su tana koya musu karatu.

Wata ƴar matashiyar dattijuwa ta sakko daga matattakalan bene ta dube su tace,”Cutie tashi in aike ki gida Ummie kisa driver ya kaiki”.

Tou Momy,momy nima zanje,ɗayan ɓa yace shima zaije tace tou taji.

Saƙon ta basu suka tafi kaiwa.

Aliyu da fitowan sa yanzun ya rungumo ta ta baya,yace,”gaskiya na gaji da ganin ki haka new baby nakeso,kan tai magana ya sun kuceta yayi bedroom ɗinsu na falo bai direta ko ina ba sai kan gado.

Dagudu nafito don ba hurimina bane

~ƘARSHE~

SUBUHANAKALLAHUMMA WABIHAMDIK,ASH HADU ALLAH ILAH HA ILLALLAH WA ASH HADU ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA RASULAHU,KUSKUREN DANAYI ALLAH KAYAFEMIN,ABINDA NAYI DON ALUMMA SU AMFANA,ALLAH KABASU IKON AMFANI DASHI

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button