MIJIN BABATA NENOVELS

MIJIN BABATA NE

MIJIN BABATA NE COMPLETE


“Dady-Dady katashi kamin wanka natafi school,Momy tace in tasoka ai ita ba ƴar aiki bace,kuma kar in ƙara tashinta in tana bacci”.

Faɗan wata ƴar cute girl da bata wuce shekara biyar ba da take tsaye bakin gadon mahaifinta tana bubbuga ƙafafuwan sa.

Girgiza kai yayi lallai Abeeda bata da ranan shiryuwa,ace ka haifi ƴa bazaka iya kula da ita ba,taɓa baki yayi ya miƙe yana kallon agogon da ke manne jikin ginar ɗakin lokaci guda yace,”muje bedroom ɗinki,inyi miki wanka kinji Little cute”.

Ko alaman damuwa babu atattare dashi don inda sabo ya saba da halin Abeeda,kamar ba auran soyayya sukayi ba,burinta guda tahau motor tasa manyan kaya sam bata damu da gyaran gida ba,balle kula da ƴar da ta haifa,gashi mugun halinta baisa ta zauna da ƴan aiki.

Daf da zasu shiga bedroom ɗinta ta tace,”Dady ka samo min Nany gaskiya”.

Shafa kanta yayi yana murmushi yace,”inshaAllahu Little Cute ɗina ,zansa Hajiya Mama ta samo miki new nany”.

Tsalle tayi cike da murna tace,”thank you Dady i love you”,tare da manna masa kiss a hannu.

Tare suka sake ma juna murmushi.

Wanka yayi mata ya shiryata kafin yaje kitchen ya dafa musu indomie da ƙwai ,abaki ya bata kafin taje ta ɗauko jakan ta ya kira driver ta ya tafi da ita makaranta.

Nufan ɗakin matan shi Abeeda yayi,tana kwance kan gado ga uban tulin kaya ba ninki,ranshi yaji yayi matuƙar ƙara ɓaci da halin Abeeda ƙwafa yayi ,sai lokacin tasan ma anbuɗo ƙofa anshigo sam bata sani ba.

Ɗan gajeran tsaki taja ta gyara kwanciyar ta taci gaba da danna wayarta alaman chart take a hasale yayo kanta yasa hannu………!

THANK YOU FOR UR COMMENTS FANS LUV YOU LODI-LODI

DON JIN YANDA ZAA KWASHE SAI NAGA RUWAN COMMEMTS KAMAR MUNA WATAN TAKWAS????
typing????️

????JEEDDATOU????

NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI

MALLAKIN:- Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER????????)

(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo

WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE

SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU

PaGe 11&15

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

_????Ɗan gajeran tsaki taja ta gyara kwanciyarta taci gaba da danna wayarta alamun chart take a a hasale yayo kanta yasa hannu ya fisge wayar ya bugata da bango ta fashe ta watse.

Buɗe baki tayi da hanci ta kalle shi ta kalle inda wayar ta fashe.

Azuciye yake kallonta,kallon raini da ƙasƙanci ya kumbura yayi fam.

“Wai dan Aliyu wannan wani irin wulaƙanci ne,har yakai yau da ka fasa min wayata”.

Cikin ƙunan rai take magana,don chart ɗin da suke da ƙawayen ta awani group ya ɗau daɗi gashi ya fasa wayar.

Murza ƴan yatsu yakama yi yana nuna ta da ɗaya,yace,”Abeeda wallahi tallahi sai nayi mum-munanan saɓa miki,ke wata irin sakarya ce ƙazamar gida,wacce bata san ciwon kanta ba,wallahi Abeeda baki san inda yake miki ciwo ba,ji ɗakin ki,inda kike kwana kamar juji bola,anjima kifita ko ɗan kamar matan gwamna”.

Nau yayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin yaci gaba da faɗin ɗakin ki kenan inaga falo,toilet kitchen tirrr da auran ƙazama irinki,bedroom ɗina dana ƴarki sai in ni na gyara,tou wallahi daga yau nazo na ƙara ganin kina chart baki aikin da matan gida maana matan aure sukeyi ba wallahi sai na mummunan saɓa miki,mtsewww.

Ya ƙarashe maganan dajan tsaki.

“Aliyu ni ba ƴar aiki bane inko kanaso kaga waje tass kanemo ƴar aiki,kuma wallahi ba abinda zan gyara”.

Cike da rashin kunya take maganan kana,ta miƙe ta faɗa toilet kai ko ɗan kwali babu tabarshi tsaye.

Girgiza kai kawai yayi yafita ranshi na ƙuna.

NIKO NACE DAMA DUK WANDA BAIJI BARI BA,YAJI YEHO,YANZUN ALIYU TAURIN KANKA WA GARI YA WAYA


Abba na inshaAllahu zakaji sauƙi ka taka kamar yanda kowa ke…..!

“Kina fitowa ki ɗau lalamen ga ki bashi abinda ya rage kisha kizo ki ɗebo ruwa kafin lokacin gada yayi koko sai nazo na lallasa miki jiki”.

Maganan Zarah ne ya katse mata maganan da take wa mahaifinta,miƙewa tayi jiki a saɓule tacire hijjab ɗinta tasa akan ƙofa tafito ta ta ɗau ƙwaryan dake buɗe duk ƙuda nabi kana,ta ɗauke ludayin dake gefe kan wani fayfay tasa acikin lalamen ta nufi ɗaki.

Aje ƙwaryan tayi ta gyara masa kwanciya ta yanda zata bashi baibiyo ta hanci ba ta ɗeba takai mai baki taga ya kauda kai,murmushi tayo don tasan mai kauda kan yake nufi.

Zama tayi ta lanƙwashe ƙafarta ta fara sha ,ganin ta fara sha yafara murmushi,don wani lokaci bai fara shan fura ko lalame sai yaga tasha ta ƙwoshi kafin yake karɓan wanda taba shi,hakan ko akayi sai da ta ɗansha,duk da lalamen baida wani yawa,kafin tabashi yasha.

Tana gama bashi ya goge mai baki ta gyara mai kwanciya kafin ta kwashe kayan tafita ta ɗau bokati tafita rijiyan dake jikin gidan su ta baya ta ɗebo ruwan ta cika ko ina.

Fakan idon Zarah tayi ta kamfata ruwan taje tayi wanka,duk da babu kayan da zata sauya,wannan masu warin datti da dauɗa ta kuma sawa tafito ta anshi sautun zuwa cin kasuwar gada.


“Wallahi Salman nagaji da zama da Abeeda,ƙazantar ta tayi yawa”.

Aliyu ne cike da takaici yake gayama Salman damuwar shi.

“Ni wallahi Aliyu da kaji maganan Ummie game da aure da baka shiga halin damuwan nan ba,jiyanda ka susuce kazama kaima wani ƙazami dakai”.

“Wallahi ko Salman nabiye wa son zuciya,nayi zaɓen ƙyale-ƙyalen banza,zaɓen tumin dare”.

“Wallahi fushin Ummie ne kaje ka lallaɓatw kabata haƙuri Allah bashi kwana biyu kanuna mata kana son waccan yarinyar”.

“Hakane ko aboki koko amini zance,duk da bata nuna mani komi game da auran Abeeda banbi wasiyar mahaifina ba,ɓacin ran da nasa mata a lokacin shi kaɗai ya isa yabibiye ni”.

Tattaunawa suka rinƙa yi yanda zasu ɓullo ma wannan alamarin.


Dafda magariba ta dawo niƙi-niƙi da kayan da suka fi ƙarfinta.

“A’a Hauwa Jidda kindawo gadan ne,wai bakijin kunya goɗai-goɗai dake kina zuwa cin kasuwa?.

Haɗa rai Jidda tayi tamm kamar zata fashe ta haɗa giran sama dana ƙasa,a hasale tace,”Maa’u ina ruwanki,banjin kunyar ke da kike da kunyar ai baki zuwa”.

Maa’u ƙawar shashancin Atiƙa ce duk sa’ani suke da Atiƙa bata da kunya sosai.

Riƙe ƙugu Maa’u tayi,kana tace,”ke mayya bora kawai harkinyi bakin da zaki zageni yau keda Zarah ne,sai naja an lakaɗa miki dukan tsiya”.

Tsaki Jidda taja,tare da cewa kije ki faɗa mata inyaso karta barni da rai”.

“Kam bala’i haka kikace?.

Ko tanka ta Jidda bata kuma yiba.

Wucewa tayi kai tsaye gidan su Jidda tana kuka ta kwashe ƙarya da gaskiya ta faɗa ma Zarah da ƴaƴanta,zarah tacika tai fam jiran jidda take ta ɗau mummunan mataki akanta.

Jidda ko da ƙyar tasamu yaron da ya temaka mata ya ɗauko mata kayan.

Assalam…….,batakai da ƙarasa sallaman ba ko sai dai taji sauka abu akanta wanda yayi sanadiyar ………..!

YAUWA FANS DA COMMENTS ƊINKU NAKE ƘARA JIN ƘARFIN GUYWAR TYPING KUCI GABA DA SAMBAƊO COMMENTS,INA GANIN COMMENTS ƊINKU SOSAI NAKE GODIYA LODI-LODI????????
typing????️

????JEEDDATOU????

NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button