MIJIN BABATA NENOVELS

MIJIN BABATA NE

MIJIN BABATA NE COMPLETE

MALLAKIN:- Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER????????)

(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo

WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE

SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU

PaGe17&20

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

__????Assalam….,bata kai da ƙarasa sallaman ba ko,sai dai taji saukan abu akanta,wanda yayi sanadiyar zubewar ta ƙasa wanwar babu motsi.

Duk da haka Zarah bata kula da aika-aikan da tayi ba,ta bita ta hau ruwan cikin ta tana ta bugu bata ji bata gani.

Hansai ce tazo wucewa taga tana dukan ta,amma ko motsawa batayi,tazo a zuciye ta ja Zarah gefe ta wurgar,kan Jiddah ta nufa tana girgiza ta.

“Ke Hansai kina shiga min hanci da duƙunƙune akan lamuran gidana,in banda iskanci ƴarki ko ƴata”.

Cike da masifa take hayayyaƙo ma Hansai.

“Tou sakaryar mace sha-sha-sha samna,kin kashe masu ƴa kin huta”.

Kuru-ruwa Zarah ta sake take mutane suka fif-fito,ga Jidda kwance bata ko motsi.

“Na shiga uku na lalace ni Zarah”.

Cike da tashin hankali duk ta ruɗe take magana.

“Aiko baki shiga uku ba tukunan,yanzun zan ruga gidam mai gari inkai ƙaranki,Allah bashi a turo da ƴan sanda daga birni atafi dake ki bayani”.

Faɗan wani ɗan matashin yaro da jiya yadawo daga cirani.

Hansai tace,”wallahi ko hanzarta Zarah bata da mutunci bata da imani”.

“Dan Allah kuyi haƙuri kuyi min rai”.

Atiƙa da Sa’inah ko duk sunyi ƙulu-ƙulu da ido ,sun rakuɓe a gefe.


“Ummie na tuba”.

Faɗan Aliyu dake duƙe gaban mahaifiyar sa ya haɗa hannuwan shi biyu tare da maraice murya.

Murmushi tayi tare da gyara zama,tace,”mai kayi kuma da kake neman tuba?.

Ta tambaya cike da mamaki.

“Ummie kinfa sani,Ummie na tuba zan zauna da ita”.

Riƙe baki tayi da mamaki,kafin ta kuma cewa,”wai kai lafiyan ka kuwa?,wa zaka zauna da ita?,ina Abeedah?.

Lokaci ɗaya ta jero masa wa ƴannan tambayoyin.

“Ummie ɗiyar baba Ibrahim nake nufi,na gaji da auran Abeeda Ummie,ƙazantat-ta yayi yawa,Ummie harfa Cutie bata kula da ita”.

Taɓa fuskan tayi,ta kauda kai gefe kafin tace.


“Wai ke Aisha kina tunanin zan maida kaina ƴar aiki ne?,wallahi bai isa ba.

Faɗan Abeedah dake zaune rashe-rashe a ɗakin ƙawarta Aisha.

Aisha murmushi tayi kafin tace,”kar ki saki jiki kiyi aikin gida ,wallahi ƙawata jikin ki ɓaci yakeyi,ni kin gani kafin ya fita sai yayi komi,tunda yace bai son ƴan aiki”.

“Ai ke kin huta,kin samu mijin marainiya,kin dace miji,ba kalan nawa ba sai girman kai kamar fir’auna”.

Dariya suka sheƙe dashi suka tafa.

SHIN WANI HALI JIDDAH TAKE

SHIN MAI UMMIE ZATA CE MA ALIYU???

ANYA KUWA AISHA BA RAINA MA ABEEDA HANKALI TAKE BA??

MORE COMMENTS
MORE TYPING????

MASOYA COMMENTS ƊINKU YANA ISKE NI,INA GODIYA INA FARIN CIKI SOSAI,LUV U LODI-LODI????????
typing????️

????JEEDDATOU????

NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI

MALLAKIN:- Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER????????)

(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo

WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE

SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU

PaGe 21&25

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

_????Dariya suka sheƙe dashi suka tafa,Aisha wani shu’umin kallo tabita dashi.


Aliyu bazan taɓa yarda dakai ba yanda kakeson matar nan naka,in ɗauko ƴar mutane abaka,ƙilama kun haɗa bakine kai da ita a ɗauko ta ku azabtar da ita,ku maidata bora,abinda nasani kawai zaka iya rubuta ta kaddan saki,inkai wa mahaifinta ya samu wani ya bata,don bazatai ta zaman jiran gawon shanu ba”.

Cikin haɗa rai take magana,babu alamun dariya ko wasa a tattare da ita.

Subuhanallah,ni Aliyu naga ta kaina,komai zance ma Ummie da wiya ta fahimce ni,don na ɓata rawana da tsalle,dana amince da wasiyar mahaifina da duk haka bai faruba,da yanzun gida biyu maganin gobara.

A ƙasan zuciyar shi yake wannan maganan.

Miƙewa Ummie tayi tana ƙoƙarin shigewa cikin gida,yai saurin ruƙo saleɓen zanin ta,tsayawa tayi cak batare da ta kalle shi ba.

“Ummie pls forgive me”.

“Aliyu ka kiyayeni,kabani takaddan saki kawai,kaje ka zauna da wacce ka zaɓi farin cikin ta fiye da nawa”.

Cikin fushi take maganan.

Gaban shi tsananta bugu yake,yaune rana na uku da ya taɓa ganin mugun ɓacin rai fuskan mahaifiyar shi,gaskiya na tafka babban kuskure ya faɗa a ƙasan zuciyar shi.

Azahiri ƙara marairaice murya yayi yace,”Ummie na kiyi haƙuri”.

Hmmmm Aliyu ɓace min daga gani inka ƙara zuwa min da maganan nan ranka sai yayi mugun ɓaci”.

“Tou Ummie inshaAllahu”.

Miƙewa yayi jiki a saɓule yai mata sallama,ya tafi yana tunanin mafita,lokaci ɗaya kuma yayi murmushi.


Kan kuce mai har ankai ma mai gari labari,take ya buga waya zuwa birni akaturo masa ƴan doka.

Ɓangare guda ko Tani ta rinƙa ƴaban ruwa Hansai na watsa ma JIDDA amma ko kaɗan bata dawo ba,alama dai rai kamar ya fita.

Zarah tayi yunƙuri guduwa mata suka riƙe ta masu jin haushin ta suka naɗa mata bugu tsiya,sai da ta kasa tashi,ana haka ƴan doka sukazo suka tafi da ita ,yayinda suka ɗau JIDDA,zasu kaita asbiti,su Atiƙah sai kuka suke.

Sai da suka fara kai Jidda asbitin UDUTH kafin suka wuce da Zarah police station bayan sun bar Jidda da police mace guda da Hansai da Tani.

A&E aka shiga da ita likitoci da nursing suka rufu akanta.


“Dady wai ina zamuje ne?.

Cutie take magana ta naɗe hannuwan ta cikin riga da wando yellow purple ɗin ɗan ƙaramin hijjab yasa mata da takalmi purple,akwatin ta yake sa mata kaya.

“Weekend zamuje,ran sunday zamu dawo sabida school”.

Ya faɗa batare da ya kalle ta ba yaci gaba da sa mata kayan a ɗan akwatinta.

Tsalle tayi da murna,ta hau bayan shi tana dariya.

Dariya yayi shima daidai lokacin yana rufe akwatin.

Ɗauka yayi suka fito riƙe da hannun juna.

Daidai lokacin tafito taci uban ado kamar bazata mutu ba,kallon-kallo sukai ma juna,yawani murtuke fusa,yayin da ita harara ta galla masa.

“Good morning momy”.

Faɗan Cutie da ta tsare Abeeda da ido.

Batare da ta kalle inda take ba taja dogon tsaki ta wuce ta fita ba tare da ta ko gaisheshi ba.

Murmushin takai ci yayi tare da shafa kan Cutie.

Cutie ko jikin ta duk yayi sanyi.

Koda suka fito harta banka ma motor ta wuta ta wuce.

Aliyu ko matuƙar mamakin halin Abeedah yake.


ALIYU INA ZUWA HAKA????

SHIN WANI HALI JIDDA TAKE,TA MUTU KO TANA RAYE.

WANI HALI ZARAH TAKE

DAMA ASHE ALIYU BA AURAN ABEEDA KAWAI YAKE DASHI BA????.

INA GODIYA DA COMMENTS ALLAH YABAR ƘAUNA
typing????️

????JEEDDATOU????

NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI

MALLAKIN:- Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER????????)

(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button