MIJIN BABATA NENOVELS

MIJIN BABATA NE

MIJIN BABATA NE COMPLETE

WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE

SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU

PaGe 26&30

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

_????Aliyu ko matuƙar mamakin halin Abeeda yake,da kafin suyi aure ba ƙaramin biyayya take masa ba kamar zata maida shi ciki,ko kaɗan bata son ganin ɓacin ransa,amma yanzun dattin ɗakin ta yafishi daraja a idon Abeeda.


Mahaifin Abeedah ko duk hayaniyar da ake yanaji,bai iya kukan zahiri sai na fili,jikin sa ya tsanan ta da zafi,gashi babu mai temako akusa,don har ya cire rai da ita,jin ana faɗin ta mutu.

Addua yake a zuciyar sa Allah ya saka ma Jidda,shi kuma Allah yakawo masa ɗauki a rayuwar shi,in kuma lokacin sa yayi Allah yasa ya cika da kalman shahada.


Zarah ko nacan police station tana amsan azaba kala-kala ,duk marasa imanin police ɗinnan sun gama ƙara canja mata kama gaba ɗaya.


Saida likitici suka kwashe awa uku akan ta kafin sukayi nasaran dawo da numfashin ta,don dogon suma tayi lokacin da Zarah ta buga mata sandan.

Don ko su kansu likitocin har suncire rai da zata shi,duk da akwai alaman rai atattare da ita.

Hansai ko hankalin su duk a tashe yake tunda sukaji shiru ba wanda yafito balle suji tana raye ko ta mutu.


Tafiyan awa biyu da rabi yayi daga shi sai ƴarshi komi ta gani a hanya sai tace Dady saya min,ko kuma ta tambaya miye wannan,wani yabata amsa wani yai murmushi yaja mata hanci,hartai bacci ta tashi tace,”Dady bamu iso ba?.

Murmushi yayi ya shafo kanta da ɗanyan hannun shi yace,”mun zo mana yanzun zamu ƙarasa”.

Gyaɗa kai tayi ta kwanta taci gaba da wasa da yatsun ta kamar wata babban mace.

Cutie kenan akwai manyan ce kamar wata ruƙon tsofaffi.

Parking yayi a dai-dai killan gidan su mahaifin shi ba kowa a a wajan sai bisashe da suke ta kiwo,yara ne daga can nesa suke wasan su,kulle motor dayayi ta hanyar danna key yasa motor tai kuka,take yaran hankalin su ya dawo kan su.

Zuba musu ido sukayi,shiko ɗaukan Cutie yayi suka fara tafiya,yaran ko zuba musu ido sukai kamar sunga tv.

“Assalamualaiku”,sallama ya rinƙa kwaɗawa,amma ba kowa shiru,har ya juya zai fita,ya lura da Sa’ina dake zaune ƙarƙashin dalbejiya tana damɓara kwalliya kamar wata jaka yasa ran shi ya ɓaci.

Cutie ko tana arba da ita dawani saki ƙara ta ƙanƙame Aliyu,tana faɗin Dady dodo”.

Lokacin Sa’ina ta ɗago ta kalle su tawani saki baki da hanci.

Shafa kan Cutie yayi yace,”ba dodo bane,ƴar iska ce”.

“A’a Dady”.

Aliyu ko wani mugun kallo ya watsa ma Sa’ina kafin yace,”ke mahaukciya baki iya amsa sallama bane?.

Washe haƙora tayi da sukai ja kamar ma aikatan cokula tace,”Ali banji bane”.

Ɗan tsaki yaja yace,”dalla ina Abba”.

Taɓa baki tayi tace,”yana ɗaki”.

“Ni kike taɓa ma baki,shegiya mai suffan buranya,inna ƙaraso sai na karya ki”.

Ranshi ɓace yake maganan.

Shiru tayi tai muƙus don tasan shi da rashin imani yanzun sai ya nema ya karyata,gashi tana shirin zuwa wajan saurayin ta.

Dogon tsaki yaja ya nufi ɗakin Abba,kwance yake jikin sa ne kaɗai ke rawa gashi yai fitsari da kashi ɗakin duk ya ɗume da wari,ga yunwa naci cikin sa.

Har Aliyu ya tusa kai yai saurin dawowa baya yana toshe hanci.

“Ke da mutum a ɗakinnan ?ya tambayeta cikin tsawa.

Jiki na rawa tace “eh baida lafiya ne Jiddah ne ke kula dashi”.

Ina Jiddah take da bata gyara shiba?,maike damun shi?.

Lokaci ɗaya ya jero mata wa ƴannan tambayoyin.

“Jidda an tafi da ita asbiti tun jiya baa dawo ba”.

“Miya faru da ita?.

Dama-dama tawani fara kame-kame.

“Zaki min magana ko sai na taka ki mai suffan burai”.

Dama Zarah ne,nan ta kwashe abinda ya faru ta gaya masa,ransa yai mugun ɓaci sai huci yake kamar ya daki babu.

“Ke tou uban miye amfanin ki da bazaki dubashi ba banza ballagaza wanda tasha a mama,dalla tashi kije ki gyara shi tas”.

Yanda yake ihu yake tada jijiyoyin wiya ba ƙaramin razana tayi ba,jiki na rawa ta miƙe ta nufi ɗakin Abba yaune rana ta farko kenan da tunda ya fara ciwo shekara huɗu kenan bata ko leƙa shiba ta ga yayake.

Azuciyar ta kuwa tsine ma Aliyu kawai take,toshe hanci tayi tana tsoron ta fita ya kileta,gashi saida tayi wanka taci kwalliya zaisa ta aikin kashi tou ita ta yaya ma zata fara.

Ƙwafa yayi ya samu turmi ya zauna ya ɗaura Cutie kan cinyarshi da tuntuni tawani ƙanƙame shi,a zuciyar shi ko ganin rashin kyautawan shi yayi da har ƙanin mahaifin sa ɗaya tilo da ya rage masa a duniya yana ciwo bai san ma yanayi ba,gashi yana da halin temakon sa,rabon sa dashi tun ɗaurin auran sa da Abeeda ko ban gajiya bai samu zuwa yayi masa ba,sabida kunyar da abinda yai masa.

Tana kuka wi-wi-wi tana sharan majina,kwalliyan ta ƙara dame fuskan tazama kaman buranya ta ɗebi ruwa ta gyara shi ta canja mai kaya,duk da sunyi dauɗa acikin su ta samu wasu ta sauya masa ta fita da kayan can.

Fitowa tayi tace mai ta gama,sauke Cutie yayi ya miƙa mata wayar shi yace tayi game.

Ɗakin ya nufa,ba ƙaramin tausayawa Abban nasu yayi ba ɗaukan shi yayi ya fito dashi yakai sa motor Cutie na biye dashi ,abaya ya kwantar dashi yana hawaye yayinda suka shiga gaba shida Cutie.

Cutie tsura masa ido tayi na seconds kafin ta kai duban ta kan Aliyu tace,”Dady waye shi”.

“Cutie Baba nane,sunan shi Abba,ke kuma Kakan ki ne”.

Yana juya motor yana mata magana.

Cikin mintina ƙalilan ya harba motor kan titi sai cikin gari.

NAGODE SOSAI DA COMMENTS ƊINKU ALLAH YABAR ZUMUNCI????????????❤️
typing????️

????JEEDDATOU????

NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI

MALLAKIN:- Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER????????)

(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo

WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE

SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU

    *PAGE31&35*

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

_????Cikin mintina ƙalilan ya harba motor kan titi sai cikin gari,asbitin daji yakai shi wajan wani abokin shi Dr Munir inda aka anshe shi aka shiga dashi A&E don bashi temakon gaggawa.


Ɓanagaran Jidda ko likitoci bayan sunyi nasaran cetou rayuwarta suka fito inda suka kira Hansai da Tani sukayi masu bayanin ta farfaɗo,amma basu san lafiyan kanta tana cikin hayyacin ta ko ta samu taɓin ƙwaƙwalwa sai ta farka daga bacci tukunan zasu iya gane haka,da ta farka su tabbatar da sunzo sun gayama likita,don a ƙara dubata,su ci gaba da addu’a,godiya sukayi suka tashi suka nufi ɗakin da aka kwantar da ita.


Zarah ata ko ina jin jiki takeyi,tun balle da akace ƴar kishiyan ta ta kashe,hatta wa ƴanda aka haɗa su cell ɗaya gana mata azaba sukeyi.

Duk ƙiban nan ta zaizaye ta rame tayi zuru-zuru kamar wata jaɓa.


Hajiya Abeeda ko bata damu da tasan inda mijinta da ƴarta suka je ba,ta shiga cikin gari abinta,taje gidan wannan ƙawa taje na wancan,su kwashi jiki su bi can ta saki baki tana ta basu labarin mijinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button