MIJIN BABATA NENOVELS

MIJIN BABATA NE

MIJIN BABATA NE COMPLETE


“Ke mai bakin surutu tsiya daga ina?,ina Abeeda?,ko Aliyun ne ya kawo ki”.

Ummie ce kema Cutie magana da ganin ta kawai tayi agabanta batare da tasan sanda ta shigo ba don harta bata tsoro.

Turo baki tayi ta yamutsa fuska kamar zatayi kuka ta hau kujera tare da kalmashe ƙafa tace,”Ummie yunwa”.

A taƙaice tayi maganan.

Buɗe baki Ummie tayi kafin tace,”kaji min ƴar jakan uwa,ni zaki turo ma baki kice min yunwa”.

“Ummie yunwa”,ta ƙara maimaitawa a taƙaice.

“Zo cinye ni,tunda ninayi miki magana baki ban amsa ba kin shigo kamar wata aljana wai Ummie yunwa”.

“Dadyne fa ya kawo ni,yace ince miki banci abinci ba”.

“Ina Aliyun?.

“Ya wuce”.

“Tashi kije kitchen kice Sadiya tabaki abinci”.

Tashi tayi da gudu ta nufi hanyar kitchen.


Aliyu ko bazama yayi police station neman Zarah tanan ne zai iya gane inda yarinyar take.

Saida yaje police station uku ana huɗu ne ya samu nasaran ganinta.

Sanda aka fito da ita zuwa bayan kanta inda zasuyi magana.

Zarah ƙasa tayi da idonta tana hawaye dama can shakkan Aliyu take don baida mutunci ko kaɗan tsaye-tsaye yake mata magana babu ko kara.

“Gwaggo nazo ja miki kunne ne wallahi,matuƙar yarinyan nan ta mutu ko wani abu ya sameta wallahi tallahi billahillazi ko duka arzikina zai ƙare,sai na ƙarar don inga an hukunta ki,baruwana da ke ƴar kakana ne,sannan mijinki kawunane mafi soyuwa a gareni zan rufe ido a wulaƙanta min ke,police kuci gaba da hukuntata”.

Cikin kakkausar murya yake mata maganan yanayi yana murza yatsun sa suna ƙara,iya abinda ya faɗan kenan ya ciro rafar ɗari biyar ya aje musu akan tebur ya juya yabar wajan.

Duk wani dake tsaye a wajan saida yayi mamakin maganganun shi,sannan ya aje uban kuɗi ya tafi.

Zarah ko duk ta rikice tasan halin Aliyu saide bai furta ba sai ya aikata,tayaya asirin da tayi mai na bazai ƙara waiwayan ƙauye ba ya karye har yazo,dole takoma wajan mallam,don maganin ɗan iskan yaron nan.

Acikin zuciyarta take wannan maganan,duk da ana dukan ta amma saƙa mugunta take a ƙasan ranta.

Nan ko police sun samu abin nema take suka ɗauke kuɗin suka tasa ƙeyarta ana bugu har cikin cell.


Kai tsaye uduth ya nufa,da kwatancen da police sukayi masa ya isa ward ɗin da take.

Tura ƙofar yayi ya shiga da sallama.

Hansai da Tani ansawa sukai suna duban mai shigowa.

“Sannun ku babaa, ya mai jikin?.

Yai maganan yana kallon gadon da take kwance ɗaure da roban ruwa,tana bacci gwanin ban tausayi,ga kayan jikinta duƙun-duƙun,lokaci ɗaya yaji tausayin ta ya shiga jikin sa da jijiyar sa.

“Mai akace damuwar ta?.

Yatambaya akaro na biyu.

Nan Hansai tamai bayani,bai wani gamsu ba,yafita ya nemi likita ya ƙara yi masa bayani,kafin ya fito yaje chicken republic yayo take away yakai musu,har lokacin bata farka ba.

Inda Abba yake ya koma,lokacin har an gama dubashi an kwantar dashi shima sai bacci yakeyi,wajan likita yaje yamai bayanin hawan jinine yai sanadiyar kawo mai mutuwar jiki,rashin kulawa da zuwa asbiti yasa jikin sa ya mutu gaba ɗaya.

Dr Munir yabashi tabbacin zai iya tashi,inde aka dage masa da gashi.

Sallama sukayi ma juna bayan an samu mai kula da Abba namiji,zai biyashi.

MrS BaSaKkWaCe
typing????️

????JEEDDATOU????

NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI

MALLAKIN:- Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER????????)

(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo

WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE

SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU

PAGE 36&40

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

_????Sallama sukayi ma juna bayan an samu mai kula da Abba namiji,zai biyashi.

Kai tsaye gida ya wuce daga farfajiyan gidan ya gane hajiyar gidan bata dawo ba,taɓa baki yayi da girgiza kai cike da takaici.

Ɗakin shi ya wuce kai tsaye,bayan ya aje key da wayoyin shi ya cire kaya,ya shiga toilet ya watso ruwa tare da ɗauro alwala,yai shafa’i da wutiri,kayan baccin sa ya saka ya hau gado ya ɗau wayar shi yafara dannawa.

Sai 10:30pm yajiyo shigowan ta ta ƙure waƙa a motor kamar club.

Girgiza kai yayi cike da takaici,watou a tinanin tafiyar kwana yayi shiyasa taje tai dare,ƙwafa yayi.

Itako sam bata kula da motor shiba tafito ta wuce ciki riƙe da takeaway ɗin da tayi order.

Ɗakin kaca-kaca da kaya gefe ta aje ta cire kayan ta watsar a gefe ,tura kayan da ke kan gadon tayi gefe ta hau ta zauna bata damu da tayi wanka ta canja kaya ba,buɗe takeaway ɗin tayi tafara cin abinta tana danna waya hankalin ta kwance.

Washagari tunda sassafe ya tashi nufi gidan Ummien sa,basu tashi ba ya zauna a falo suna ta hira da Iya mai ma Ummie girki,tun yana yaro suke tare da Iya ke gidan ,tana da kirki ga tsafta tare da halin dattako,sam bata nuna kwaɗayi a abinda ba abata ba.

Umurni yabata tamai girki yana da marasa lafiya a asbiti baban wai course mate ɗin shi,aiko a mintina ƙalilan ta haɗa musu breakfast,harta gama ya ɗauka ya tafi dashi, su Cutie basu tashi ba.

Abba yafara kai mawa,ya farka amma yana kwance sai bin Aliyu da ido yake ,yana mamaki,yana so ya motsa bakin shi ya tambaye shi ina Jidda amma ba dama sau hawaye.

Aliyu aje kwandon yayi jiki na rawa ya ƙarasa jikin gadon yana faɗin,”subhanallah Abba hawaye kuma mai yafaru?.

Kallo wanda ya kwana da Abba yayi,yace,”ya jikin nasa?.

Ɗan dattijon gyara zama yayi yace,”alhamdulillah,daya farka na kira Likita ya duba shi,an ƙara mai allura”.

“MashaAllah ubangiji ya ƙara masa lafiya”.

“Ameen ya Allah”.

“Ga abinci nan na kawo ma,zanje in duba ƙanwata da take Uduth”.

“Tou ɗannan Allah yayi albarka”.

Amin ya amsa dashi,kafin yakai duban shi ga Abba dashi yake kallo,har yanzun amma hawayen ya tsaya yace,”Jiddah itama tana ƙarƙashin kulawan likitoci,jikinta taji sauƙi,yanzun haka zanje wajan sune,Allah ya baka lafiya zanje indawo”.

Cikin murya ƙasa-ƙasa mai cike da tarin ladabi yake maganan,yana gamawa yai ma mai kula da Abban sallama ya wuce.


Jidda ko ɓangaren ta ƙarfe uku da wasu mintoci ta wani farka a razane tana kira Abba-Abba-Abba”,can cikin bacci Tani ta jiyo ta ta tashi a razane take Hansai da tayine yai sanadiyan tashin ta.

Idon ta arufe yake tana kiran Abba.

“Tani riƙe mata hannuwa tayi tana faɗin sannu Jiddah kin farka”.

Cike da kulawa take maganan.

Muryan da tajine yasata waye manyan idanuwan ta da sukayi mata nauyi.

Ganin su Hansai yasa take mamakin,kallo tafara bin ɗakin dashi,daga gani nan ba ƙauyen su bane,ya akayi tazo nan waya kawo ta.

Hansai tace,”sannu Jidda Kulu bari akira Likita”.

Da mamaki take kallon Hansai nan asbiti ne tou mi ya faru waya kawota nan.

Hansai jiki na rawa taje ta kira Likita suka dawo tare.

Dudduba ta yayi,kafin yai mata tambayoyi yace,”ya sunan ki?.

Ahankali ta buɗe baki tace,”Jiddah”.

Good yace,yana gyaɗa kai,ya nuna Hansai yace yasunan wannan?.

Kallonta takai gareta tsawon minti ɗaya,tace,” Hansai,wancan kuma Tani duk ƴan ƙauyen mune ,ina Abba na?,wake kula dashi ,mai ya kawo ni nan?.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button