MIJIN BABATA NENOVELS

MIJIN BABATA NE

MIJIN BABATA NE COMPLETE

Aruɗe take magana tana kallon Dr.

Gyara murya yayi yana murmishi yace,”……..!

NAGAJI DA TYPING????WALLE BAKU COMMENTS????SHIYASA KUKAJINI NAYI LAUSHI NAYI LUƘUS KWANA BIYU BANA TYPING???? TAYPING ƊINKU SHINE ƘWARIN GUYWAN MARUBUTA????
typing????️

????JEEDDATOU????

NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI

MALLAKIN:- Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER????????)

(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo

WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE

SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU

PaGe41&45

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

_????Gyara murya yayi yana murmushi yace,” Alhamdulillah,ta maganganun ta nagano bata da matsalan ƙwaƙwalwa,nan asbiti ne,Hauwa,Abban ki na gida”.

Cikin tattausan murya yake mata magana.

Hansai ta amsa da cewa,”Ali ɗan gidan Abban ki Aminu,ya ɗauko Abban ki ya kaishi asbiti shima”.

Sauke nauyayyam ajiyar zuciya tayi kafin ta ɗuƙar dakai tace,”Alhamdulillah”.,duk da ambaton Aliyu saida ya faɗar mata da gaba.

Dr tambayoyi yai mata cike da ƙwarewa irin nasu na Likitoci tana bashi amsa,daga bisani yasa aka kawo mai allura yai mata take bacci ya ƙara ɗaukan ta.


Ƙarfe bakwai da ƴan mintoci ta kuma farkawa,da salati bayan nan tayi addu’an tashi daga bacci,kana ta miƙe ta zauna,tanabin ruwan da ke tafiya cikin hannun ta da kallo.

Tani ta taso da hanzari tace,”sannu JIDDA, ya jikin?.

“Alhamdulillah”,ta amsa dashi murya ƙasa-ƙasa.

“Tou-tou Allah ya ƙaro dama”.

“Amin”,ta amsa dashi a taƙaice.

“Ko akira likitane?.

Tani ta ƙara tambaya.

“A’a temaka min zaki in rama sallolin da ake biyata”.

Da mamaki Hansai ta riƙe baki ganin ƙarfin hali wai sallah zatayi,ita in tana ciwo ai bata rama sallah,lafiya ƙalau ma bata dameta ba,sai taga idon mutane takeyi,taɓa baki tayi kana daga bisani tace,”tou bari intemaka miki,baki bari ƴarnan jikin ki har ya ƙara ƙarfi?.

Ta ƙarashe maganan da sigar tambaya.

Ahankali ta girgiza kanta,kana tace,”ke Tani inna mutu fa?,inje ince ma Allah maine?ince banji sauƙi ba?.

Lokaci ɗaya ta jero mata wa ƴannan tambayoyin.

Mamaki Tani take ƴar ƙaraman yarinya da magana babba,yarinyar nan dai wuni take talla,ya akayi tasan karatun islamiya.

Abinda ko ke faruwa,inde Jidda ta ɗau tallan goro da yamma,can gidan fura take tafiya,su suna da yawan islamiyoyi da boko,jikin wata islamiya take zama tana sauraran karatun su,anan duk ta iya abu-buwa da yawa,tana sha’awan karatun addini,amma ita talla bazai bari tayi ba,kullum tana ti-ti yawon talla.

“Temaka min manaTani”.

Ta ƙara magana,muryanta ciki-ciki.

Tani sa hannu tayi ta tallafo haɓanta,suka taka ahankali harcikin banɗakin ta barta tafito don ta kama ruwa tayo alwala,tace mata inta ida ta kirata,hakan ko akayi tana idawa ta buɗo ƙofa ta kirata,kamata tayi takaita kan kallabin ta da ta shimfiɗa ta zaunar da ita tabata hijjab ɗinta ta saka.

Rama salloli tafarayi tun na jiya har yau.


Zarah jiki yayi tsami yayi laushi,bata ƙara tabbatar da ƴan sanda basu da imani basu d mutunci ba,saida Aliyu yazo ya basu kuɗi ,suka ƙara ƙaimi amata rashin mutunci.

Duk tayi laushi,dana sanin abinda tayi takeyi yanzun da yanzun tana gida tana juya biyar ta zama goma.

Da tabari ta shigo ta same ta da icen dalbejiya ta jibga babu mai ce mata kanzil,Allah ya tsine ma Hansai take faɗa a zuciyarta.

Duk da haka bata saduda ba,jira take ta fita,duk wahalar da aka bata anan sai ta fanshe ajikin JIDDAH.


Uban dame suke tiƙawa a tsakanin su,mutane sun taru ana raba su amma sam basa ji,har yakai da mutane sun koma kallon su.

“Shegiya karuwa,karuwan cina yamin rana tunda ni ina iya sayan sabulu kizo ki ɗauke kina wanka”.

Faɗan Atiƙa datake ta huci kamar maciji.

“Karuwa gakinan ƙatotuwar ashawo ciki nawa kika zubar”.

Faɗar Sa’ina da take ƙoƙarin cakumo Atiƙa,dakyar aka shiga tsakanin su,amma basu dena cin mutuncin juna ba da ɓacin su.

NIKO NACE ALLAH YA WADARAN RAƘUMIN DAWA YAƘI ƳAƳA????♀️

“Shegiya ƴar iska ke Saminu da ya kawo dukiyar auren ki,ina ce har ubanshi kike lalata dashi”.

Faɗan Atiƙah da har yanzun huci take tana zare ƙananun ido irin na uwarta

Mutanan wajan salati suka ɗauka cike da mamaki.

Take dambe ya ƙara kaurewa tsakanin sun suna yaga ma juna kaya.

Daƙyar aka raba su,akaja Sa’ina akayi waje da ita.

Asafiyar ranan ko,ƙauyen nan labarin su ake lungu da saƙo.


Turo ƙofar da akayine yasa dukan su suka ɗago kai………….!

MORE COMMENTS
MORE TYPING????

MASOYA NAGODE DA ADDUOIN KU,ALLAH YABAR ZUMUNCI????
typing????️

????JEEDDATOU????

NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI

MALLAKIN:- Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER????????)

(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo

WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE

SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU

PAGE51&56

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

_????Kafin ya wuce da ita gidan Ummie gaban shi na faɗi,yan a tunanin draman da zasu kwahe da Ummie sa.

Ko da suka isa yace,”mata ta fara shiga ciki,fita tayi jiki a sanyayye ta nufi cikin gidan,don rabon da tazo gidan tun bikin Aliyu da sukazo da Abban ta da zai ɗaura ma Aliyu aure,ana gama ɗaurin auran suka koma ƙauye tun da suka koma Abban ta ya faɗi tun daganan ya kama ciwo.

Ahankali ta tura ƙofar tashiga da” asallamualaikum”.

Cikin sanyin murya tayi maganan can ƙasa-ƙasa.

“Waalaikumusalam”,Ummie dake ɗaura ma Cutie ɗan kwali,ba tare da ta ɗago ba.

Jin shiru ba’a ƙara magana ba ba’a shigo ba yasata ɗago kai,karaf idon su ya sarƙe da juna,da mamaki Ummie ke kallon ta,yau ne rana na farko da taganta cikin shiga mai kyau, don kullum zata ganta cikin duƙu-duƙun kaya,taso ta temaka mata amma masifar ZARAH ya hana ta temake ta,tunda ALIYU ya watsa mata ƙasa a ido,cikin ma wuyacin halin da take ganin ta bai mata daɗi yana ɗaga mata hankali yasa tadena zuwa Lafani.

Lokaci ɗaya ta faɗaɗa murmushin ta mai nuna alamun tsan-tsan farin ciki ganin ta tace,”a’a Hauwa Jidda ce agidan namu yau lale marhaban,ina Ibrahim ɗin?,ki shigo ma kin coge jikin ƙofa kamar baƙuwa”.

Murmushi tayi tana sunkuyar da kai ta ƙaraso cikin falon ta zauna a ƙasa.

“Keko Jidda wannan halin naki na ƙauyawan fulani nanan,sai wani noƙe jiki kikeyi kamar wata kifi”.

“Kwallahiya Ummie?.

“Lafiya lau ya kike,kitashi ki zauna kan kujera”.

Girgiza kai,Jidda tayi tana tura shi cikin hijjab.

Hmmm” ni wallahi ban san wannan hali,ina Abban naku nagan ki ke kaɗai?.

“Ni da Yayane bada Abba ba,Yaya bai gaya miki mun kwanta asbiti ba,yanzun haka Abba na shi baa sallame shi ba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button