
Gwalalo ido Ummie tayi cike da mamaki,ranta lokaci guda ran Ummie ya ɓaci,ohh dama Maman abokin nashi da ba ta da lafiya yake amsan abinci yana kaiwa,ashe Abba ne da Jiddah.
“Mi ya sameki keda Ibrahim ɗin?.
Nan ta kwashe ciwon Abba tun daga randa suka koma bikin Aliyu ta gaya mata,da kalan azaban da tasha,da sanadin kwantawan ta asbiti,ta gaya mata batasan yanda Aliyu yasan Abba baida lafiya ba har ya kawo shi asbiti,amma yanzun jikin sa alhamdulillah.
Ummie tun kafin ta gama ta fara sharan ƙwalla,lallai bata kyauta ba,ta yada zumun ci,da Abdullahi na raye da bata kwashe shekarun nan ba bataje ba nan lafani ga baki ga hanci ko motor haya zata hau ɗari shidda ne,balle ga motocin gidan birjit sai wanda ta zaɓa zata hau.
Share ƙwalla tayi kafin cikin dasha-sh-shiyar murya tace,”ina Aliyun ya tsaya?.
“Yana waje yace,” zai shigo”,ta bata ansa a taƙaice.
Aliyu ko yana jikin ƙofa yanajin komai dake wakana,ya turo ƙofar ahankali ya shigo,jikin sa a sanyaye ,ko kafin ya ƙaraso tsakiyan falon Ummie ta ture Cutie dake kwance ajikin ta ta rai ɓace tayo kansa,yana ɗago fuska yaji saukan mari tassss-tasssaa ke ratsa falon hagu da dama take marin sa.
Jikin Cutie na rawa ta ƙara haye wa cikin lallausan kujeran falon ta tura kanta saƙon kujeran a firgie JIDDA ta miƙe tana zaro ido.
Bata taɓa gani an doke babba ba a ƙauyen su,gani take in yaro ya girma ya wuce duka,koda ko wani irin laifi yayi,haka take ganin ƴaƴan ƙauyen su suyi ta ma iyayen su raini amma ba mai dukan su,ashe ba haka abin yake ba.
Iyah dake haɗa masu Ummie breakfast da sauri ta aje ta fito falon tana faɗin subuhanallah,lafiya wa ake ma…….!
Turus tayi ta haɗiye maganan dake fitowa daga bakin ta ganin Ali zaki ake mari.
Ƙasa yayi da kan sa,gaban sa na tsanan ta faɗi yana jira kawai tasamu bulala ta fara dukan shi,inde haka zaisa ta huce daga fushin da hau,don ko bijire mata da yayi akan auran Abeeda da wasiyar mahaifin shi da yayi batayi fushi haka ba,ta kauda komi don ta faranta masa ya rabbbb sa’iduni ya furta a zuciyar shi.
“Aliyu,ni kake rainawa,ka ɗauke ni ako da yaushe ba abakin komi ba,banda mahimmanci awajan ka ko,tou wallahi Aliyu ko ban maka baki ba,duniya zata gaya ma,akoda yaushe ba burin ka ka faranta min ba,saide ka ɓata min ko,nagode Allag yasaka maka da alkhairi Allah yama albarka,Allah yabaka abinda kake nema duniya da lahira”.
Cikin mummunan ɓacin ran da bai taɓa sani zata iya ba take maganan,tana kai ƙarshe batare da tabi takan kowa ba dake falon fuuuuu ta wuce hanyar birthroom ɗin ta.
Daga Iyah har JIDDA suna tsaye cirko-cirko,JIDDA cike take da dana sanin da bata gaya ma Ummie ba da tasan ranta zai ɓaci har ta mare shi ta gaya munanan kalamai akan shi.
Iyah ko mamaki take mai Aliyu yayi haka da haryasa Hajiya tayi wannan mugun fushin akan sa.
Cutie ko tana maƙure waje ɗaya jikin ta har rawa yakeyi.
Jidda jiki a sanyaye ta ƙarasa inda yake tsaye dafe da kumatuka da sukayi ja ta duƙa ta ruƙo guywowin sa,wani abu yaji ya ziyar ce shi mai kama da shocking ɗin wutam lantar ki da sauri ya ja baya ƙirjin sa na tsanan ta bugu.
Jikin ta sanyi yayi ahankali ta ta buɗe baki tace……..!
MORE COMMENTS
MORE TYPING
ƘILA ZAKUJINI SHIRU KWANA BIYU SABIDA WANI UZIRI DAKE GABANA LOVE U OLL MY FANS????❤️????????
typing????️
????JEEDDATOU????
NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI
MALLAKIN:- Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER????????)
(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo
WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE
SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU
PAGE 56&60
BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM
_????Jikin ta a sanyaye a hankali ta buɗe baki tace,”Yaya kayi haƙuri wallahi ban san ranta zai ɓaci ba harta yanke ɗanyen hukunci haka akan ka,don girman Allah kayi haƙuri ka yafe min”.
Ta ƙara she maganan da muryan kuka,ji yayi duk ba daɗi lokaci ɗaya a zuciyar shi,tayi matuƙar bashi tausayi yanda take maganan.
Duƙawa yayi yana fuskan tan fuskan ta,sa hannun shi yayi a hankali kan lallausan fuskan ta ya share mata hawayen da suka zubo yana murmushi kamar bashi aka gama kashe da mari ba yace,”ƙanwata karki damu Ummie zata sakko zanje in bata haƙuri “.
Yauwa abinda yakamata kayi kenan gadanga,fushin mahaifiya,bala’i ne da masifa akan ɗanta,hatta Allah fushi yake dakai in kasa mahaifiyar ka cikin ƙunci tashi kaje kabata haƙuri,don gujewa fushin ubangiji.
Faɗan Iya da take tsaye ta bayan su tun ɗazun da sai yanzun tayi magana.
Murmushi yayi yace,”zan bata haƙuri Iya,Ummie ta mai fahimta ce da haƙuri,nasan zata haƙura”.
“Yauwa tashi kaje”.
Faɗar Iya akaro na biyu.
Miƙewa yayi yana fasha fuska,tare da riƙo haɓan ta yamiƙar da ita.
Cutie da gudu ta taho wajan sa ta ƙan-ƙame shi,duƙawa yayi ya ɗagota ya shillata sama,sukayi hanyar bedroom ɗin Ummie,yana raɗa mata magana akunne tana gyaɗa kai tana murmushi.
“Abeeda wai ke bazaki bikin ƙanwar Najaatu bane a katsina,ki tambaye mijinki,in zai barki”.
Faɗar Aisha da suke zaune wajan shaƙatawa,suna ciye-ciye,duk sunci ado kamar bazasu mutu ba.
“Kam bala’i da yasani da kar ya sani uwar su ɗaya uban su ɗaya,kayan ankon ma na wajan ɗinki,tafiyata zanyi,aini aduk fitata ban jiran umurnin Aliyu inde zan jira umurnin sa tou bazani ba,kulle yake min kamar matan mallam,ban ɗauka ba kuma bazan ɗauka ba yasani ,banda lokacin sa”.
Taɓa baki Aisha tayi cike da mamaki take kallonta ita ta isa tafita gaba gaɗi batare da sanin Abubakar ba da ta kwana gidan su,bikin nan ma ya tubure yace baiga uban da zataje yi ba biki katsina bikin ƙanwar ƙawan ƙawa cabɗi.
“Azahiri ko tace,”ai da yaganki sakwa-sakwa rainaki zai rinƙa yi,mazan nan in baka nuna musu kaima jan wiya ne kana da taurin kai ai sai sharan gidan ka yafika walwala”.
“Kide bari ƙawata,ni wallahi ko ƴa mantawa nakeyi ina da ita,don shike mata komi,kwana biyu ma ban ganta ba ko tana gidan uwarsa ne oho,duk inda yakaita shi ya jiyo bani da asara”.
Lallai lamarin Abeeda yana matuƙar ba Aisha mamaki itade duniya kawai tasa agaban ta ,wani kallo Aisha ta watsa mata a zuciyarta tace ƴar wahala,kibiye ma matan bariƙi sunan ki bazawara wata rana,bakina ganin yana ƙaunar ki bazai iya turaki gidan ubanki ba,ni naiman haihuwar ma muke ido rufe bamu samu ba keda yake jaka ce kin samu kina wulaƙantawa,azahiri ko haƙori ta washe tace.
“Ƙawata aikin ki nakyau wallahi,karki yarda ko ƙara haihuwa balle harki tsufa,atara miki ƴaƴa ,shikuma yaje ya ƙara aure”.
Kaɗa manyan idanuwan ta Abeeda tayi kamar zasu faɗo ƙasa tace,”aure ai wallahi Aliyu bai isa ya auro wata ƴar iska ba,yamin alƙawari dagani babu ƙari,ke in taƙai ce miki Aliyu bai iya haɗani da kowa a zuciyar shi balle har yaji shaawan yimin kishiya,haihuwa ko bazan iya buɗe mai ƙafa ba kullum yaci kamar yasamu shinkafa,ke in taƙaice miki ancire min mahaifa,yanda bazan haihu ba kwata-kwata,inci duniyata datsinke da kyau,ba wanda yasani sai ke da yau na faɗa miki don kema ƙawar arziki ce baki bani shawaran banza “.