MIJIN BABATA NENOVELS

MIJIN BABATA NE

MIJIN BABATA NE COMPLETE

Ɓoye mamakin ta Aisha tayi da yacika zuciyarta lallai Abeeda ba Allah sam a gabanta,sheɗan yayi mugun buga mata gangar mu’azu tayi nisa banta jin kira a zahiri ko tace.

“Shegiya ƙawata aikin ki na kyau sosai”.

Dariya suka fashe dashi tare da tafawa.

Aisha na mata kallon sakarya.


“Atiƙa-Atiƙa ke Atiƙa tashi ki ɗaukan min tallan kokon nan rana nayi”.

Faɗan Zarah dakw tsaye kan Abeeda da tayi ɗaiɗaya kan gadon kara kannan tugu-tugu ba kitso,miƙa tayi ta miƙe tana gantsaro ƴan matasan nonon ta da suka ɓullo kamar kan gero,suma azaban taɓawan maza ne yasa suka fito,turo baki tayi tana bin Zarah da wani mugun kallo tace.

Zara kin raina min wayo da yawa,ina bacci zaki wani tasheni akan banzar kunun ki ni bazani ba ki ɗauka da kanki kije ko kijira ƴar iskan can Sa’ina tazo ta je miki don wallahi bazani ba”.

Riƙe baki tayi tanabin Atiƙa da ido harta dasa aza tace,”kaji min shegiya ƴar iska nizaki gayama bazakije min tallan koko ba lallai wiyan ki ya isa yanka”.

Wallahi Zarah ko shure-shuren mutuwa kike bazani ba,zaki zubar min da aji talla Allah ya kiyaye wallahi in zaki jira Jidda ta dawo taci gaba miki ita ce bautantar ki amma bani ba,in kin matsy kije da kanki”.

Tana kai aya ta miƙe ta shige bayi batare da ta ɗauko buta ba.


Tura ƙofar suka tura a hankali suka shiga tana zaune bakin gado tayi tagumi lokaci ɗaya ya ɗuƙa guywowin sa a ƙasa ko ɗagowa ba tayi balle ta kalle su,lokaci ɗaya suka……………!

MORE COMMENTS
MORE TYPING????
typing????️

????JEEDDATOU????

NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI
JIDDATOU

MALLAKIN:- Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER????????)

(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo

WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE

SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU

PAGE61&65

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

_????Tura ƙofar suka tura a hankali suka shiga tana zaune bakin gado tayi tagumi lokaci ɗaya ya ɗuƙa guywowin sa a ƙasa ko ɗagowa ba tayi balle ta kalle su,lokaci ɗaya suka fashe da kuka lokaci ɗaya a tare,don Aliyu yasan tun yana ƙarami Ummie ta tsani kukan shi hankalin ta yanzun zai tashi ta shiga damuwa.

Runtsa idon ta-tayi tana jin wani abu yazo ya tokare ƙirjin ta sam batason jin sautin kukan Aliyu,lokaci ɗaya ta maida kallonta kan Aliyu da Cutie da suke kuka duk sun zuba mata ido.

“Ya isa haka Aliyu” ta faɗa da ƙarfi cikin ɗaga murya.

Lokaci ɗaya suka haɗe kukan su kamar haɗin baki.

~NIKO NACE LALLAI UBA DA ƳAR NAN TASHI ƳAN DRAMA NE,DAMA RAƊAN DAYAI MATA A KUNNE KENAN SUNA DARIYA ASHE DRAMA SUKA HAƊA~

“Kasan bansan ganin hawayen ka a ƙasa shine zaka zo ka tasa ni gaba dakai da mai kama da kyanwar ~MRS BASAKKWACE~ da baƙaƙen idon ta kamar na ~ZEE YERO~ kuna min kuka ,kutashi kuban waje in kuka zakuyi min kuma ka tafi da ƴarka can ku ƙarata”.

Cikin ɗaga murya take maganan.

Cikin marai-raicewa murya suka haɗa hannuwa suka ce,” sorry Ummie”.
a taƙaice.

Shiru tayi bata kalle su ba,bata kuma basu amsa ba.

Cutie sauka tayi a jikin Aliyu tasa guywowin ta a ƙasa ta kamo ƙafar Ummie ɗaya da yake ƙasa tace,”Ummie Dadyna bazai ƙara ba wallahi,kiyi haƙuri,kinga Dady ma yayi kuka”.

Maganan taso taba Ummie dariya amma ta danne dariya tace,”tashi kiban waje ko inyi ball dake mai bakin tsuntsu kawai,nayafe masa na haƙura haɗa kayan ki kukoma gidan ku,maza tashi kikira Iya ta haɗa miki kayanki don banson takura”.

Kumburo baki Cutie tayi kumatun ta suka ƙara cikowa kamar na ~LIPTON GIRK~ tacw,”ni anan zan zauna Momyta bata son”.

Saurin toshe mata baki Aliyu yayi yace,”mata kull yana girgiza kai,kar na ƙara ji yanada nake son ki haka Abeeda kinji”.

Gyaɗa kanta tayi.

Ummie ko tausayi ƴar jikan tata ɗaya tunƙwal take bata ace ka haifi ɗa kamar ka haifi ɗan shegw baka iya kula dashi balle kanuna masa so wannan wata irin ballagazan uwa ce.

Ummie kinyi haƙuri ko?,,faɗan Cutie davta kafeta da ido.

“Eh nayi badon halin ki ba da ubanki,tashi kije ki ce Iya ta baku abinci keda Auntyki JIDDA”.

Tashi tayi cike da farin ciki tai ma Ummie kiss a gefan kumatun ta ta fita da gudu cike da murna.

Harara ta galla ma Aliyu da kan shi ke ƙasa tace,” watou ka raina ni baka ɗauke ni da mutunci ba ko da matsayi shiyasa zan maka magana kasa takalmi ka shure maganata katafi lafani don baka da kunya kaje kace ma Ibrahim maine yayi haƙuri yabaka JIDDA koko tou wallahi sai kabani takaddan sakin ta don ko Ibrahim bai isa ya hanani ansan takaddan sakin JIDDA a hannun kaba,don haka ka gaggauta katashi ka kawo min takaddan sakin ƴata JIDDA don amana uwarta tabani ita don kawai anfi ƙarfinane na haƙura”.

NIKO CIKE DA MAMAKIN MAGANAN UMMIE NAKE DAMA JIDDA MATAN ALIYU NE?,TOU TAYA HAKA TAFARU BAI ZAUNA DA ITA BA YA AURE ABEEDA BISA DUKKAN ALAMU ABIDA BATA SAN DA WANNAN JIƘAƘƘAN A ƘASA BA,RANDA TAJI KO AKWAU ƘURA A ƘASA????

Tunda Ummie tafara maganan saki yaji kamar tana buga masa guduma akai a razane yake kallonta yana girgiza kai.

“Wallahi Aliyu ko mi zai faru sai ka saki JIDDA wato kun haɗo baki da matar ka abaka ita kuje ku maidata boyi-boyi ku bautar da ita,tou bazan yarda ba aci amanar baiwar Allah ba marainiya”.

Cikin kakkausar murya take maganan tanayi tana murza ƴan yatsu.

Aliyu ko sam a zuciyar shi bai ji zai iya sakin ta,don zaman da sukayi da ita a asbiti ta shiga ransa,zai lallaɓa Ummie ta barshi da ita ko bazasu tare ba.

Sosa ƙeyan shi yayi yace,”Ummie itama ya kamata a samo mata malami da zai rinƙa mata lesson ta iya karatu da rubutu kafin akaita makaranta na boko dana islamiya”.

Buɗe baki Ummie tayi lallai Aliyu ya raina ta watou tana gabas yana yamma duk maganan da tayi masa bai ma shiga kunnesa ba ,wani magana ya kawo mata,ƙwafa tayi ta tashi ta shiga ban ɗaki,don bama tasan mai zata kuma ce masa ba.

Murmushi yayi ya tashi ya fuce.

Ba kowa falon sai ƙaran AC da TV ga daining nan alaman anci abinci an tashi.

Suna gama cin abinci Cutie taja hanun Jidda wai suje ɗakin ta suyi wasa,hakan ko akayi JIDDA tabita bedroom ɗinta ta kwaso kayam wasan da Ummie ta sayo mata ta baje a tsakar ɗakin suka kama wasa JIDDA ko kamar saanta ta biye mata Cutie sai farin ciki take.

Har ya shigo basu sani ba hankalin su ya ɗauku wajan wasa,ya jima tsaye yana kallon su yana jin wani nishaɗi daɓa Abeeda ce da bazai taɓa tinanin ƙara zama da wata mace ba.

Nima nazo ayi dani faɗan Aliyu,dukkan atre suka ɗago suka zuba masa ido cike……….
!

MORE COMMENTS
MORE TYPING
typing????️

????JEEDDATOU????

NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI
JEEDATOU

MALLAKIN:- AMMIEY CAT WOMAN(THE CAT LOVER????????)

(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo

WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button