MIJIN BABATA NENOVELS

MIJIN BABATA NE

MIJIN BABATA NE COMPLETE

SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU

PaGe66&70

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

__????Nima nazo ayi dani faɗan Aliyu,dukkan su a tare suka ɗago suka zuba masa ido,cike da mamakin yaushe ya shigo sam basuji takowar sa balan tana buɗe ƙofar sa.

Idon shi cakkkkk akan JEEDAH da itama shi take kallo ido cikin ido kallon kallo suke mai juna,a hankali ta jaye idanuwan ta don lokaci ɗaya taga wasu kibiyoyi daga ƙwayan idanuwan shi suna fitowa suna shiga nata.

Murmushi Cutie ta sake tare da haɗa hannayen ta-tafa su waje ɗaya tace,”perfect match,Dady ka ɗauke ta mukoma gidan mu wallahi kunyi matuƙar dacewa”.

Ɗan sosa ƙeyan shi yayi yana murmushi ya sa guywowin sa ƙasa yana shafa lallausan gashin kanta yace,”Cutie kin cika magana babu wani perfect match,kuci gaba da wasan ku,bari inje gida in dawo”.

“Dady Momy fa,kace mata nayi missing ɗinta over one billion”.

Shafo kanta yayi lokacin ɗaya takaici da haushin Abeeda ya sauka a zuciyar shi,ɗan gajeran tsaki yaja can ƙasan maƙoshin sa yace,” zan faɗa mata,ki kula da kanki”.

“Ummie dai ta kula dani,ni mai zan iya ɓa kaina”.

Ta faɗa tana wani ƙyafta manyan idanuwan ta.

Murmushi yayi tare da sake mata peak kiss a goshi,tare da miƙewa yana satan kallon JEDDATOU da kanta ke ƙasa kamar ruwa ya shanye ta-tawutsiyar ido ya ke kallonta har yafice,sai da ya tabbatar ya fice ya kulle ƙofar ya wani jingina da jikin ƙofar ya sauke wani nauyayyan ajiyar zuciya yana runtsa idon kallon ta yake cikin ido da ɗazun suke kallon juna,murmushi ya sauke harsai da kumatun shi suka lotsa a zahiri ya furta “gaskiyan kine CUTIE mun dace sosai”.

Jin motsi kamar wani na fitowa yasa yai saurin bin hanyar waje.

Da mamaki Ummie take kallon bayan shi dama bai fita ba,mi ya tsaya yi,lallai sai ta tsaya tsayin daka akan Aliyu game da Jiddatou sai tayi bake-bake taga yanda zai ganta har ya hure mata kunne ta soshi.


Zai shiga kenan tana danno hancin motor ta waje,da baya yaja motor sa ya buga tagumi yana bin motor ta da kallo har ta ɓace ma unguwan kafin ya samu daman shigewa da tashi motor.

Halin Abeeda yadena bashi mamaki tsoro kawai yake bashi ta rikiɗe ta sauya kamar ba Abeedan da suka soyayya ba kamar zasu lashe junan su,ko kaɗan a da bata son ɓacin ransa yanzun ko saide ya mutu ba ruwan ta da damuwar shi.

Cike da tinani kala-kala yai packing ya shiga ciki.


Ɓangaran Abeeda koda tagan shi ko ɗarrr bata ji ba don bala’in haushi Aliyu ke bata,duk yabi ya takura ma rayuwar ta,gwamma da tabi shawaran AISHA da yanzun kanta yayi murfi yabarta a baƙauyiya bagida jiya,dayanzun ya ɗinkira mata ciki ya barta dareno,thank God da tacire mahaifan gaba ɗaya ta huta da ɗaukan ciki,in yaso in tama son wani haihuwar taje asa mata wani.

????????????????????????????????OHHHHHH NI MATAR DATTIJO WACCE MIKI ANA CIRE MAHAIFA A MAYAR,LALLAI KINA RUWA GAKI GA KADA


“Yauwa ƴar halak irin albarka ƴaƴar da aka haifa tsiya na bacci,zo ki ɗau min tallan ku……!

Sa’ina da yanzun shigowan ta ɗauke da jaka a kafaɗa,da alaman kwanan waje tayi,tawani katse Zarah da ganin ta yasa ta washe jajayen haƙoranta take mata maganan ɗauka talla.

Kambala’i injiwa Zahra ɗaukan talla,ko kaɗan ba ajina bane,ke kika jama kanki da yanzun Jiddah na nan da ita zatayi miki,wa a birnin ma a ina take,kiyi yanda zakiyi ta dawo kici gaba da ɗaura mata tallan,amma ga dubu uku ki raba ma almajirai,amma wallahi bazan ɗau talla ba”.

Tana magana tana girgiza jiki tana ya mutsa fuska.

Sa hannu tayi a acikin jaka ta ɗebo dubu uku ta watsa ma Zarah dake tsaye buɗe da baki.

Zarah a hasale tace,”kaji min ƴan jaka da lalainta ƴaƴa ,tallan ce bakuyi min kun gwammace kuyi ta yawo kwararo,lungu-lungu,amma dai zanyi manaji,duƙawa tayi ta kwashe kuɗin ta kalmashe shi tasa a lalita,ɗaukan roban kunun tayi ta ɗaura akai tafita.

NIKO NACE YAFI MIKI,GA RANAN JIDDA DE KIN GANI,ƳAƳAN DA KIKA HAIFA SUN GAGARE YI MIKI WACCE KIKAI MA RIƘON SAKAINAN KASHI TAFI MIKI AMFANI DASU

~ASALIN LABARI~

Malam Muhammad mai gemu,shine asalin kakan su Jiddatou,haifaffan ƙauyen……..!

MORE COMMENTS
MORE TYPING
typing????️

????JEEDDATOU????

NA MARUBUCIYAR:-????
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
ND NOW
AWANI GARI
JIDDATOU

MALLAKIN:- (THE CAT LOVER????????)

(????S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE????)
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo

WHATSAPP NUMBER:- 08167151176
WHATPADD:- MRS BASAKKWACE
GMAIL:- MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
IG ACCOUNT:- KHADDEJATOU BASAKKWACE
TWITTER:- @MRSBASAKKWACE
SNAPCHART:- KHADEEJATOU BASAKKWACE

SADAUKARWA GA-:-
MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU

PAGE71&75

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

_???? ~vASALIN LABARIN~

Mallam Ibrahim Muhammad mai Gemu shine sunan cikakken sunan mahaifin su JIDDATOU,su biyune awajan iyayen su,shida wan shi Abdullahi,sun taso wajan maƙwafcin su Mallam Ibrahim,kasancewar tun suna ƙanana ,Allah ya ɗauki ran iyayen su ta sanadiyan gobaran wutan da baa san dalilin tashin sa ba,kasan cewar maƙwaftakan da,da amin takan da,tafi na yanzun,ada maƙwafcin ka zaiyi yanda ya gadama da ƴaƴanka,saɓanin wannan lokaci da kowa nashi ɗan yasani.

~TO WANNAN KENAN~

Mallam Ibrahim yana da mata ɗaya Zarah wacce take ɗiya ga ƙanwar mahaifiyar sa,auren ladan noma akai musu,watou na jeka ga ɗakin ka.

Shekaran su shabiyar basu taɓa koda ɓatan wata ba,hakan yasa shi zuwa maƙwaftan garin su ya auro wata yarinya mai suna Aisha.

Zarah tayi bala’i tayi bore ba,amma hakan bai hana Ibrahim aure ba.

Aisha tasha tsagwama da kyara a wajan Zarah,bata da sakewa sai in Ibrahim na gida,inko bayanan bautan duk duniyan nan sai tayi shi.

Shekaran ta guda,sai ga ciki ya bayyana a jikinta.

Zarah kamar tai hauka,ta kasa zaune ta kasa tsaye,alokacin ta fantama zuwa gidan bokaye,duk inda taje saide aci mata kuɗi ace cikin zai zube,amma shiru,maye yaci shirwa.

Wahal-halun duniyan nan ta ɗauko ta ɗaura mata.

Inda ko ɓangaran Ibrahim tarai-raiya kawai takesha kamar ƙwai acikin cokali,komi yasamo Aisha,komi Aisha,ran Zarah ɓaci yakeyi kamar zata mutu,tai ta zage-zage da habaice-habaice.

Bayan wata tara ta haifo ɗiyarta mace,mai kama da ita,buɗan bakin Zarah ko cewa tayi taga haihuwa zataga yanda yarinya zata rayu a doran ƙasa.

Aisha ko addua kawai take ma ƴarta Allah ya tsareta,Ibrahim ko komi lodowa yakeyi,jikin sa na rawa,da wanda zaiyi amfani da wanda bazaiyi amfani ba siyowa yakeyi.

Ranan suna yarinya taci sunan mahaifiyar su Hauwa’u,suke kiranta da JIDDATOU,kulawan duniya Ibrahim ya ɗowa ma wannan ƴa,har matan ɗan uwan shi sunzo daga birni da ɗan uwan nashi da ɗansu ɗaya Aliyu mai shekara goma,Aliyu ko yarinyar nan wuni take awajan sa,har Aisha kece masa kana son ta nabaka ita,sai yace eh Ummie na zamu tafi da ita ko?,Ummie ta gyaɗa kai suyita dariyan yarintar sa.

Zarah ko kamar ta kashe su don haushi da takaici,ta tsani matan Abdullahi,basa zama inuwa guda.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya da daɗi ba daɗi,Aisha nata rainon ƴarta cikin kulawa haka mahaifinta ta,bata fito da ƴarta tsakar gida matuƙar Zarah na nan,don cin zalinta take da gan-gan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button