KannywoodLabaraiMalam Zaidu

Mu ma mutane ne, in kun ga kuskure ku dinga fada mana, Malam Zaidu Gidan Badamasi

Fitaccen jarumi kuma furodusa na masana’antar Kannywood, Aminu Shehu Usman, wanda aka fi sani da Aminu Mirror ya bukaci mutane su dinga yi musu gyara idan sun ga sun yi kura-kurai, Daily Trust ta ruwaito.

A wata tattaunawa da Daily Trust tayi da shi, Aminu, wanda yanz aka fi sani da Malam Zaidu daga fim din da yayi na Gidan Badamasi, ya ce ya samu nasarori masu tarin yawa daga shigarsa masana’antar zuwa yanzu.

Ya fara gabatar da kansa inda yace an fi saninsa da Aminu Mirror a shekarar 1999 zuwa 2000 da doriya, amma abin da ya fi bashi mamaki shi ne yadda yanzu aka fi gane shi da Malam Zaidu.

Ya ce an haife shi a Kusfa, cikin Zaria, ya yi karatunsa na addini da firamare duk a garin Zaria sannan ya zarce kwalejin Alhudahuda. Daga nan ya koma Kwalejin Ilimi da ke Zaria yayi karatunsa na matakin NCE.

Dangane da masana’antar Kannywood kuwa ya ce ya fara harkar ne a 1997 inda ya fara bayyana a fim 1999 kuma tun bayan nan ya ga tarin nasarori.

Burin Masoya shi ne fim dinsa na farko wanda a cewarsa Ghalin Money ya shirya kuma ya fito ne a matsayin dan jarida.

A cewarsa, ba zai iya tuna irin yawan finafinan da yayi ba kawo yanzu amma dai ya fi son ‘Gidan Badamasi’ saboda yanzu ya fice da sunan da ya samu a fim din fiye da Aminu Mirror.

Yayin da aka nemi sanin babban abokinsa a Kannywood, ya ce Marigayi Ahmed S Nuhu ne, kuma kowa ya san su tare sannan su na da matukar kusanci don har ana gobe zai rasu sun hadu.

An nemi jin sakonsa ga masoyansa inda ya ce:

“Gaskiya abubuwa yanzu sun sauya, yanzu mu na iya yawo ba tare da an tsangwame mu ba, ba kamar da ba.

“Don haka ina kira ga masoyanmu da su kasance masu ansar mu don mu nishadantar da su. Don ka fito a fim a wani yanayi, hakan ba ya nufin shi ne asalin halinka.

“Sannan muna ganin soyayyar da su ke nuna mana kuma za mu cigaba da nishadantar da su. Kuma idan sun ga mun yi wani kuskure, kada su yi kasa a guiwa, su sanar da mu, don a shirye muke da mu gyara saboda mu ma mutane ne.”

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button