MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idiriss Musa_
3️⃣4️⃣
_*Allah wants us to be grateful for all the blessings He has bestowed upon us as the one who is always thankful receives more rewards than the one who is thankless. However, if a person constantly complain while having everything Allah will surely punish him.May Allah guide us all.*_
_______Cikin zafin nama Faruq ya janyo *Ummi* da iya ƙarfin sa har Saida kanta ya bugu da hannun kujeran, ba tare da ɓata lokaci ba ya ingiza Suwaiba saman kujerar,wani irin ihu ta kurma lokaci ɗaya wanda saida ilahirin gida ya amsa, gabaki ɗaya zuba mata ido sukayi suna kallon ikon Allah, wani irin hayaƙi mai warin gaske ne ya fara fitowa ta ƙarƙashin wannan kujera, ita kanta Mummy sosai ganin wannan abu ya tsoratar da ita banda salati da sallalami babu abinda take.
Cikin abinda bai fi mintinan ba Suwaiba ta fara wani irin miƙa lokaci ɗaya jikinta ya fara sandarewa
,Saida ya zamana babu abinda ke motsi a jikinta sai kai, da gudu Sale ya ƙaraso gurin ta yana kiran sunan ta, buɗe baki tayi da kyar tace,”Tabbas banyi tsammanin zuwan wannan ranar nan kusa ba,tir da masu hali irin namu, son duniya da abinda ke cikin sa yasa mun mance da ranar nadama, yau gani cikin halin da babu wanda zai fitar dani,duk kuma a sanadiyar uwa wacce ta kasance mai son zuciya, kallon mummy tayi tace,”Naso ace akwai *Musaddam* anan ta yanda zan faiyace masa gaskiyar zance, tabbas baki da hannun gurin kisan mahaifinsa saidai ma rufa mana asiri da kike yi, ina mai niman yafiyar ki dan kuwa nasan tawa ta zo ƙarshe”.
Share hawayan fuskarta Mummy tayi tace,”Kin wargaza min farin ciki na ta hanyar ra taya min alhakin mutuwar sa a kai na, kun kashe min miji a gaba na wanda har yau babu wanda yasan da wannan zancan sai yanzu da nake faɗa, menene laifi na? Menayi muku da na cancanci wannan Sakamakon”.?
Kuka sosai Mummy take tana tuna lokacin da Muhammad yake bata amanar ƴaƴan shi, tunawa take da lokacin da ɗan ta gudun jinin ta yake furta kalmar tsana a gare ta ɗanta mafi soyuwa a gare ta”.
Kallon ta Suwaiba tayi tace,”Akwai abinda na birne cikin gidan nan zan faɗa miki inda yake in sha Allah komai zai dawo daidai muddin aka fitar dashi”.
Cikin hanzari Faruq ya ƙaraso inda take yana cewa,”faɗi inda kike birne”.?
Kwatanta masa gurin tayi cikin sauri mai gadi da shi kansa Faruq suka shiga haƙa gurin bakin su ɗauke da addu’a, wani irin hayaƙi ke tashi cikin ramin wanda lokaci ɗaya gurin ya turnuƙe da hayaƙi gabaki ɗaya,sam hakan bai sa sun dakata daga haƙun wannan rami ba.
Wani farar tsuntsuwa da ranta suka gani kwance cikin ramin,da alama kuma fara ce tas,amma tsabar wahala da Jigata ta koma wani irin kala, jikinta kuwa an ɗaure ta da jan kyalle,saida faruq yayi addu’a ya tofa a jikin wannan tsuntsuwa san ya ɗauko ruwan goran da Kaka ya basu ya watsa cikin wannan rame, wani irin jijjiga ramin yake nan take wannan tsuntsuwa ta daina motse alamar jigata, ɗauko ta yayi ya kwance wannan jar kyallan, ƙwancewar sa keda wuya wannan tsuntsuwar ta ɓace ɓat.
Hamdala faruq yayi suka dawo cikin falon, shigowar su kuwa yayi daidai da ƙwalla wani irin razananniyar kara da Suwaiba ta sake tana kiran idona bana gani ku taimaka min Sale Sale Ni’ima ku taimaka min ,can kuma ta fashe da dariya, kallo ɗaya zaka mata ka fahimci abubuwa guda uku ne suka mata dirar miƙiya, makanta, hauka, shanyewar ɓarin jiki. Innalillahi wa inna ilaihi raju’un duniya kenan duniya duniya, Allah yasa mufi karfin zuciyar mu..
Sosai Sale yake kuka da nadamar abinda son zuciya da burin mallakar dukiyar da ba tasu ba ya jefa su.
***********
Kwance wannan jan kyallan yayi daidai da farkawar *Musaddam* a fargice yana salati, jin haka yasa Kaka ya fito yana murmushi ganin yanda *Musaddam* ya tashi ya tsaya yana kalle kalle, dafe shi yayi yace,”Sannu ko yaro”.
“Yauwa sannu Mummy na bata zo ba”.?
Murmushi yayi yace,”Ƙwantar da hankalin ka tana nan zuwa amma sai gobe,”.
“Ina so naga Mummy dan Allah ku bani waya ta na kira ta, inaji a jikina bata cikin ƙoshin lafiya dan kuwa idan lafiyar ta kalau tofa zata kasance anan tare dani,dan Allah ku kira ta kuce ɗanta gudun jinin ta yana son ganin ta, share hawayan daya gangaro masa yayi yace,”, ko dai mutuwa tayi ne?” Idan mutuwa tayi ku faɗa min ni Musulmi ne kuma na yarda da ƙaddara kuma nayi imani da akwai mutuwa saboda haka ku faɗa min kawai,”….
Miƙa masa ruwan da ta kawo masa kaka tayi tana cewa,”wannan rigimar sa babu maraba dana wancan ja’irar”.
Murmushi shima kaka yayi yace,Abinda nake shirin faɗa kenan kika riga ni”.
Shidai *Musaddam* binsu da ido kawai yake ya ma rasa abin faɗa dan kuwa shi yanzu babu abinda yake da muradin gani sama da mahaifiyar sa, karbar ruwan yayi ya sha, wani irin sanyi yake ji yana ratsa jikinsa sai yace,”Inajin ɓacci”.
Murmushi kaka yayi yace,”to ga guri zauna.
Jin haka yasa Kaka yayi hamdala,kiran Faruq yayi ya shaida masa abinda ke faruwa,jin haka yasa Faruq da *Ummi* sukayi sujjada dan nuna godiya ga Allah mahaliccin kowa da komai.
Lokacin da suka sanar da Mummy wani irin kuka ta fashe fashi tana jin wani irin sanya yana ratsa gaɓɓan jikinta, rungume ta *Ummi* tayi tace,”Mummy yanzu ba lokacin kuka bane ba yanzu lokacin nuna godiya ga Allah ne, yin kuka kamar butulci ne dan Allah ki daina kuka, ita kanta magana take tana kuka , ɗaya ɓangaran kukan farin ciki, ɗayan kuma zulumin yanda *Musaddam* zai karɓe ta,shin zai ma iya tunawa da ni kuwa”? Wacece wannan budurwar wacce tsabar so da kaunar da yake mata yasa yake mafarki da ita duk da kuwa yana halin rashin lafiya”.?
Janyo hannun ta Mummy tayi tace,”Maza muje ki zamu kiyi wanka ki ci abinci, sannan kiyi bacci gobe tunda safe zamu bar garin nan,”.
Bin bayan yanta tayi ba tare da musu ko gardama ba.
Suwaiba kuwa cikin wannan dare mummy ta nema musu mota shata aka washe su sai ƙauye garin gado,babu abinda take sai faɗe faɗe gashi babu damar motsa jiki ido kuma ba’aganin gari…..m
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idiriss Musa_
3️⃣5️⃣
_*Life is a question that no one can answer, death is an answer that no one can question. No matter how great you are, your earthly journey will come to an end one day. Let us live everyday like it’s our last day, by doing good and by forgiving one another.*_
*_May the Almighty continue to bless you & your family and forgive all your sin._*
_______Zaune take tana ɓaran gyaɗa soyayye tana ci murmushi ne da tsantsar farin ciki a kan fuskar ta, sallamar Sale yasa ta mike jiki na rawa tace,”Barka da zuwa ƴan albarka fatan dai anci nasara”.?
Da mamaki yake kallon ta yace,”Inna yaushe kika fara tashi da ƙafar ki kuma cikin sauri haka”.?