MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Dariya sosai Faruq yayi harda rike ciki.
Ganin sun iso kamfanin su mai suna MUS_SAF Company yasa ya tsuke bakin sa, ko sauka daga motar Ba suyi ba aka rinƙa loda musu shinƙafa da kayan abinci nauyi daban daban kama daga manja taliya mangyaɗa da dai sauran su.
Saida aka gama lodawa cikin ɗaya daga cikin motocin kamfanin sannan yaja mota sukayi gaba, basu tsaya ko ina ba sai gidan Marayu, rabin motar aka sauke musu sannan suka suka fita.
“Faruq ina ne gidan wannan malamin?”
Murmushi yayi yace”Sauka bara na tuƙa”, haka.kuwa akayi Faruq ne ya kai shi har ƙofar gidan, sallama yayi aka kira masa matan sa, ta’aziyya yayi musu sannan yasa aka shigar musu da kayan abincin banda godiya babu abinda suka masa,sanin cewa wannan abu ne wanda ya saba yin sa.. yasa basu kawo komai a ran su ba,shima kuma bai faɗa musu komai ba.
Koda suka fita daga anguwar basu tsaya ko ina ba sai gurin siyar da motoci, da mamaki Faruq yake kallon sa yace,”Idan ban mance ba ka faɗa min cewa ba zaka sake siyan mota ba.”
“Eh haka ne yanzu kuma na canza ra’ayi.”
“Tom Allah ya yafe maka”.
“Kai ma”.
Da haka har aka fitar musu da sabuwar mota wacce sai wani da wani suke da ita kaf faɗin garin.”Ya dai wannan motar tayi kyau kuwa.?”
“Sosai ma wallàhi har wani kashe min ido yake”.
“Tom alhamdullah gashi wannan motar taka ce Faruq kuma bawai na biya ka bane ba ka yarda dani dama ina da burin saya maka mota idan baka mance ba kuma na faɗa maka”.
Da fe kansa kawai yayi yana jin wani irin farin cikin da sabon so da ƙaunar *Mussadam* yana daɗa ruruwa cikin zuciyar sa, buɗe baki Yayi da niyyar magana cikin sauri yace,”bana buƙatar jin komai daga gare ka idan har da gaske ni dan’uwan kane kamar yanda kake faɗa a kullum”.
Haka Faruq yana ji yana gani *Mussadam* ya hana shi magana…. babu yanda ya iya haka nan ya haƙura suka koma gida…
A Kofar gidan su kawai ya ije shi.. wanda ya kawo musu motar kuma ya bashi kuɗi yayi tafiyar sa yana ɗaga masa hannu.
Da addu’a kawai Faruq ya bishi.
Koda ya isa gida ya iske har Littel Nusaiba ta iso gidan murmushi yayi yace,”Oyoyo My Littel Mummy”.
Ya motsa fuska tayi tace,”Ni wallàhi wannan rashin kunya na yaran zamani yana mattukar damu na big Sister..ki duba maimakon ya zo gabana ya durƙusa amma kalli abinda ake min”.
“Gaskiya baka kyauta ba maza zo ka durkusa”.
“Hhhhh tom shikenan amin aikin gafara My Little Mummy,Au sorry Mummy na”.
Gabaki ɗayan su dariya suke…samun guri yayi ya zauna yace,”Nayi kewar ki Mummy na”.
Share hawaye Nusaiba tayi tace,”Nayi kewar ka sosai kuma nayi kuka da naji abinda ya same ka”.
“Hhhh Mummy wallàhi gado baya barin gida kenan Little Sis gadon ta tayi kalli yanda take magana hatta muryar su iri daya fa.”
“Wallàhi na daɗe da lura duk abubuwan da Safnah take ina ganin su tattare da ke Auta”.
“To Ni dai wallàhi karki wani goyi bayan shi… shekarun mu ɗaya da ita fa bare kuce gado na tayi…kuma kalla saboda surutu ko gaisawa ba kuyi da ƙawa ta ba”
Sam *Mussadam* bai ma lura da wata halitta zauna a wannan falon ba sai yanzu da mamaki ya juya dan su gaisa, ware idanuwansa yayi ganin wacce take zaune ta tsare shi da idanuwa baki buɗe alamar itama cike take da mamakin gani sa, shine yayi ƙarfin halin kiran sunan ta yace,”Fairuza”.
“Na’am aboki”.
“Dama kina ƙasan nan?.”
“Wallàhi kuwa gani..ai ku ne kuka ɓace bat ba’a ganin ku kuma baku niman mutane”
“Wallàhi ba haka bane abubuwa ne suka min yawa”.
“Shikenan ai tunda yanzu gani yaya labari ya ai yu ka?”
Sauke ajiyar zuciya yayi ya juya gun Mummy yace,”Mummy wannan tare da ita mukayi makaranta shekarun baya sunan ta Fairuza”.
Murmushi kawai Mummy tayi tace,”Sannun da zuwa Fairuza,”.
“Yawwa hajiya”.
Haka nan kawai Mummy taji yarinyar bata kwanta mata a rai ba.
Tashi *Musaddam* yayi da niyyar shigewa ɓangaran sa,cikin sauri ta miƙi sai jin hannunta kawai yayi cikin nasa.
“Ina kuma zaka tafi daga zuwan ka? Ka zauna mana muyi hira”.
Kallon dayayi mata yasa tayi saurin janye hannun ta daga nashi dan kuwa har yanzu bata mance tsari da kuma yanda yake tafiyar da rayuwar sa ba.
“Na dauka yanayi na rayuwa ko kuma gushewar shekaru yasa kin canza daga duk wa’annan munanan ɗabi’un naki, ashe har yanzu sunanan? to Allah ya shirye ki”.
Daga haka yayi wucewar sa ba tare daya sake furta koda kalma ɗaya ba.
Kuka ta fashe dashi ta fita daga gidan, kiran ta Nusaiba take amma ko sauraratta ba tai ba.
……
SAFNAH ALIYU JAWABI
09055560552
08136756004
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idiriss Musa_
4️⃣0️⃣
_______ “Auta ina kika samu wannan yarinyar?”
“Wallàhi wallàhi bansan…
“Dakata banson rantsuwa abinda na sani shine bana son dangantakar ki da wancan yarinyar.daga yau ba na so na sake gani ko kuma naji labarin kina ƙawance da ita, tsakanin ki da ita kawai gaisuwa irin ta addinin musulunci fatan kina ji na.?”
“In sha Allah nima wallàhi bansan cewa haka halin ta yake ba sorry”.
“Shikenan ai Allah ya kiyaye na gaba kai duniya Allah ka shirya mana zuri’a”.
Haka suka ci-gaba da hira har kusan magrib Nusaiba tana gidan.
********
Wani irin hon take mai firgitar da ƙwaƙwalwa da gudu mai gadi ya buɗe mata get da guda ta shiga cikin sauri mai gadi yayi tsalle ya koma gefe ,kashe motar kawai tayi ta fito da kukan ta kamar ƙaramar yarinya.
Jin Muryar ta yasa Alhaji ya fito da sauri jikin sa har rawa yake rungume shi tayi ta ƙara sautin kukan ta, shafe bayan ya yake a hankali alamar rarrashi yace,” Shalele ta faɗa min Matsalar mota ce ko gida? Dubai ko Umura? Kuɗi kike buƙatar ko me?”.
“Farin ciki Daddy na farin ciki”.
“Wani irin farin ciki ne wannan Shalele da har zai ɗaga hankalin ki”.
” *Mussadam Aliyu Muhammad* shine kawai farin ciki na Daddy idan kuma babu shi tabbas zan iya mutuwa zan mutu Dadd”…
Ganin yanda jikinta ya sake gabaki ɗaya alamar suma yasa.Daddy ƙwalla wani irin ƙara yana kira mai gadi buɗe min ƙofa”.
Da guda ya nufi asibiti da ita,da taimakon Dr aka samu ta farfaɗo saidai fa babu abinda take ambata sama da *Mussadam* *Musaddam* *Musaddam*!!!
Sosai Daddy ya rikice kallo ɗaya zaka mishi ka fahimci yana cikin tashin hankali ganin halin da take cikin yasa Dr yace,”Alhaji akwai bukatar a samawa wannan yarinyar abinda take so gudun shigar ta wani mumunar hali gaskiya.”
“Hmmm Dr sanin kanka ne da ina da hali babu abinda Shalele ba zata samu ba cikin duniyar nan, amma wannan wani abu ne na daban wanda dukiya na,karfi na ba zasu iya sama mata ba wallàhi”.
“Wanan yaron da take ambatar sunan sa Wanene shi.?”
“Ba kowa bane face *Musaddam Aliyu Muhammad*”.
Jinjina lamarin Dr yayi yace,” a a gaskiya kam ina zuwa bara nayi mata allurar bacci dan kuwa wannan ciwon bashi da magani sai dai sauki daga Allah”.
**********
Sun sha hirar su sosai da Maimuna dan kuwa sai kusan ƙarfe goma ta tafi gida cike da kewar juna.
Yau ma kamar jiya banda tunanin sa babu abinda take har barci yayi awan gaba da ita.