Yadda Rasuwar Desmond Tutu Ta Girgiza Afirka Ta Kudu


Al’ummar Afirka ta Kudu na ci gaba da jimamin rasuwar Archbishop Desmond Tutu, fitaccen malamin addinin Kirista kuma mai fafutukar kare hakkin dan-Adam, wanda ya riga mu gidan gaskiya ranar Lahadi.
Tutu, wanda mutane a ciki da wajen Afirka ta Kudu ke kwatanta shi da ma’aunin gaskiya na kasar, ya rasu a birnin Cape Town yana da shekara 90 a duniya kamar yadda Aminiya Ta rawaito
“Rasuwar Archbishop Desmond Tutu wani sabon babi ne na jimami a ban-kwana da al’ummar kasarmu ke yi da fitattun ’yan Afirka ta Kudu wadanda suka gadar mana da ’yantacciyar kasa”, inji Shugaban Kasa Cyril Ramaphosa.
Ko da yake a baya-bayan nan an daina jin duriyar Tutu, ana tuna shi musamman saboda barkwancinsa da dawwamammen murmushinsa, da kuma fafutukarsa ba dare ba rana wajen yaki da rashin adalci ko wanne iri.
“Kama daga duron turjiya a Afirka ta Kudu zuwa mimbarin manyan majami’u da sauran wuraren ibada na duniya, da ma dandamalin karbar Kyautar Zaman Lafiya ta Nobel, archbishop din ya yi fice a matsayin jagoran kare hakkin bil-Adama wanda ba ruwansa da bambancin akida ko launin fata”, inji Shugaba Ramaphosa.
Alhini
Sanarwar mutuwar Desmond Tutu ta fito ne daga mukaddashiyar shugabar Asusun Archbishop Desmond Tutu, Dokta Ramphela Mamphele.
“A karshe dai ya rasu salim-alim a Cibiyar Jinya ta Oasis Frail Care dake Cape Town yana da shekara 90”, inji sanarwar.
Gidauniyar Nelson Mandela ta kwatanta Tutu da cewa, “mutum ne abin misali. Mai fikira. Jagora. Makiyayi”.
A cewar Thabo Makgoba, Archbishop na Cape Town, “lallai ne mu karrama wannan mutum mai addini…wanda alakarsa da Mahaliccinmu ce farkon rayuwarsa da karshenta.
“Ya kasance ba ya tsoron kowa; duk lokacin da ya ga an aikata ba daidai ba, ko ma wane ne ya aikata, zai fada.
“Ya kalubalanci duk tsare-tsaren da ke kaskantar da mutuncin dan-Adam”.
’Yan wasan kurket na Afirka ta Kudu sun daura bakin kyalle a damatsansu yayin wasansu da tawagar ’yan wasan Indiya don jimamin mutuwar Desmond Tutu.
Kwanciyar asibiti
A karshen shekarun 1990 ne aka bayyana cewa Archbishop Tutu yana da cutar kansa; a shekarun baya-bayan nan kuma, kamar yadda jaridar The Guardian ta Birtaniya ta rawaito, an sha kwantar da shi a asibiti saboda wasu larurori masu alaka da maganin da ake yi mishi.
Kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, ya rawaito cewa marigayin ya bayyana a bainar jama’a bara, lokacin da aka tura shi a kan keken daukar marasa lafiya ya je aka yi mishi allurar riga-kafin COVID-19.
Sai dai a lokacin bai ce uffan ba.
An haifi marigayin ne a wani karamin gari da ke yamma da birnin Johannesburg mai suna Klerksdorp, ranar 7 ga watan Oktoban 1931.
Ya samu horo na malanta, amma bacin rai game da rashin ingancin tsarin ilmantar da ’ya’yan bakar fata ya sa ya sauya alkibla ya zama malamin addini.
Ya zauna a Birtaniya na dan lokaci, inda ya ce yakan nemi a yi masa kwatancen hanya duk da ba ya bukatar haka don kawai ya ji dan sanda farar fata ya ce mishi “Sir” – wato Yallabai.
Fafutaka
Tutu ya kalubalanci manufofi da dama a kan batutuwan da suka shafi bambancin launin fata, da luwadi, da akida.
A 1986 ya zama archbishop, ya kuma yi amfani da mukaminsa wajen kiraye-kirayen kakaba takunkumi a kan tsarin mulkin wariyar launin fata, daga bisani kuma ya shiga fafutukar kare hakkokin mutane a fadin duniya.
Tuni dai Desmond Tutu ya ce ya shirya mutuwa, kamar yadda ya bayyana a wata makala da ya rubuta a jaridar The Washington Post a 2016: “Na shirya wa mutuwata, kuma na fayyace karara cewa ba na so a yi amfani da na’urori don taimaka min na ci gaba da rayuwa”.
[ad_2]