Musayar Zuciya Hausa Novel

Musayar Zuciya Hausa Novel
MUSAYAR ZUCIYA
HADIZA D AUTA
Ƴanmata biyu ne cikin motar, ɗaya tana driving ɗin motar yayin da ɗayar take zaune a gefenta tana nazarin wani littafin husnul Muslim dake hannunta ɗaya, ɗaya riƙe da carbin roba tana lazimi jefi-jefi. Nazira ta kalli Nana da hankalinta ya ɗauku ga littafin tace
“Wai Nana yanzu ma ba zaki bari mu tattauna abun da ya dace ba?”
Nana ta ɗago da kanta tare da ɗora idanuwanta gareta tana murmushi, ba tare da tace da ita komi ba, cikin ɓata fuska Nazira tace
Tattalin So Hausa Novel
“Don ALLAH ki ajiye littafin mu yi magana Ni dai”
Nana ta rufe littafin ta mayar a ƙaramar jakar da ke saman cinyarta, sannan ta dawo da kallonta ga Nazira tace
“Hakan ya yi maki ko?”
Nazira ta ɗan harareta kaɗan tana ƴar dariya tace
“Ko kefa!? To yanzu faɗa man ina zamu fara zuwa? Wurin ƙunshin ko wurin saloon ɗin? Ko kuwa mu fara zuwa in karɓo ɗinkuna na?”
Nana ta yi murmushin da ya ƙarawa doguwar fuskarta kyau sannan tace
Musayar Zuciya Hausa Novel
“Mu fara zuwa ayi maki ƙunshin ina ga hakan sai ya fi, idan an gama sai mu je wurin Madam Ngozi ta gyara maki kan, da mun kammala da cen sai mu karɓo ɗinkin mu yi gida kawai”
Nazira cike da jin daɗin wannan tsarin na Nana tace
“Thanks my beautiful sis, Amman ke wai da gaske kike yi ba za ki yi kwalliyar tarbon my Bear ba?”
Nana ta ɗan haɗe fuska kaɗan sannan tace
“Bani a ciki gaskiya”
Nazira tana ƴar dariya tace
“Kin ci bashi Hajiya zan rama ne ai!”
Nana tana ƴar dariyar itama tace
Musayar Zuciya Hausa Novel
“Oho Ni dai kam ba zan yi ba”
Haka suke ta firarsu cikin raha da annushuwa har suka je gidan ƙunshin, tsawon awa biyu ƙunshin ya cenye masu sannan aka kammala, suka biya kuɗin suka fito zuwa shagon Madam Ngozi, a cen ma sun ci lokaci kafin a gama saboda sun taradda mutane, bayan sun gama ne suka nufi wurin karɓo ɗinkin Nazira, cikin sa’a ko da suka je ledar ɗinkin kawai ya miƙo masu suka fito cike da murna.
Suna kan hanyarsu ta komawa gida ne Nazira tace
“Ban san ya zan yi ba idan na ƙure lokaci a shagon kwalliyar nan ba, wai ko dai mu juya mu je in yi wankana a cen a shirya Ni kawai?”
Nana da ke ta kallon gaban titin cikin murmushin da ke fuskarta har lokacin tace
Musayar Zuciya Hausa Novel
“Eh hakan ma ya yi, amman me zai hana mu fara zuwa gida mu ci abinci ki yi wanka?, Saboda na kira Basira zata zo har gida ta yi maki kwalliyar”
Nazira cike da masifar jin daɗi tace
“Wowwww! Da kin gama burgeni my sis don na tabbatar da cewa sai na fi fitowa a cikin kwalliyarta, na ji daɗi sosai Wallahi ai na manta shaf da ita ne Allah, amman ki ƙara kiranta yanzu ta zo da wuri don ALLAH, gudun lokaci ya Ƙure muna har ya zo ba a gama ba”
Musayar Zuciya Hausa Novel
Ta ƙare maganar cikin damuwar da ta kasa ɓoyuwa a kan fuskarta, Nana ta yi ƴar dariya sannan tace
“Kar ki damar da kanki a kan hakan, wataƙila ma ko da zamu je mu taradda ita gida tana jiranmu”
Nazira ta yi saurin riƙo hannunta tace
“I love you so much my sis, shi yasa a kullum kike ƙara matsayi a zuciyata, ALLAH ya nuna muna ranar aurenku ke da yayanmu mu sha rawa”
Ta ƙare maganar tare da sakin sitiyarin motar tana tausaya, Nana ta maka mata harara tana cewa
“Ki bi a hankali Hajiya, kar garin murna ki je ki ɓaradda mu ki hana mu ganin lokacin to”
Ta ƙare maganar tare da haɗe fuska alamun ba wasa ɗin nan, Nazira tana dariya ta ɗora hannunta ɗaya a kan sitiyarin tana juyashi cikin ƙwarewa tace
“Haka ne kuma fa, sai dai kin san me?”
Nana tace “A’a sai kin faɗa”
Nazira ta shiga natsuwarta sosai sannan tace
Musayar Zuciya Hausa Novel
“Ina jinki a jikina tamkar ƴar’uwata da muka fito ciki ɗaya, amman ban san me yasa wata rana Hajiya take yin wasu abubuwan ba, ko ko ita bata gano yanda kike ƙaunata da zuciya ɗaya bane Oho?”
Nana ta sauke ajiyar zuciya sannan tace
“Har kullum ina cewa da ke ki daina kama irin waɗannan abubuwan a zuciyarki, Hajiya uwa ce gareni kamar yanda take a wurinki, duk abinda kika ga ta yi man ba don bata sona ta aika abun ba, saboda haka ki daina kama irin waɗannan ƙananun abubuwan plss! don ALLAH”
Nazira ta sauke ajiyar zuciyar itama sannan tace
“Na daina amman kema ki ci gaba da haƙuri da halinta don ALLAH, don na san wata rana zata gano gaskiya ta daina ƙin zamanmu da juna”
Nana ta kawar da zancen da murmushin da baya rabo da kan fuskarta tace
” Yau dai wata zata yi kwalli da Angonta, mu dai don ALLAH kada ki bari ya gano kin fishi zumuɗin haɗuwarku, amman fa ban ce kada ki nuna masa farin cikin ganinsa ba yasin”
Musayar Zuciya Hausa Novel
Nazira ta fashe da dariya tana cewa
“Idan naje ai fuskar shanu zan masa, in yace lafiya in ce da shi Nana ce tace in yi maka hakan…..”
Nana ta zaro fararen idanuwanta masu kama da an ɗiga zaiba tace
“Rufani ki saya kar ki janyo in kwana a prison yau, wannan mayen ƙarfen naki ai zai iya yin gunduwa gunduwa dani in ya ji ina lalace masa hanya”
Nazira banda dariya ba abinda take yi har suka shiga Gate ɗin gidansu, tana dariyar ta yi parking tana cewa
“My sis kin cika tsoro da yawa fa, to miye a ciki ai kina da ikon da zaki sakani in yi abu ko?”
Nana ta janyo ledar kayan ɗinkin ta fito tana cewa
“Eh kam! amman ban da wannan tsakaninki da ƙalbinki sam! bani a ciki tabbas!”
Musayar Zuciya Hausa Novel
Ta yi gaba tana ƴar dariya Nazira ta rufe motar ta biyota a baya tana faɗin
“Yasin kika ce kada in yi magana har ya tafi hakan zan yi ALLAH”
Nana cike da bugun zuciya a kan maganganun nata tace
“Allah ya kiyayeni da wannan gangancin to”
Suna dariya suka shiga gidan, sai dai hango Basira da akwatin kayan kwalliyarta a gefenta, yasa Nazira buga wani uban tsalle tare da ihun murna ta yi wurinta da gudu ta rungumeta, Nana ta ƙaraso babban falon ta ajiye ledar ɗinkin dake hannunta, ta zauna kusa da Basirar itama tana murnar ganinta, sai ga Hajiya tana saukowa ƙasa idonta a kansu tana faɗin
“Tun da na jiyo ihunki na san kun dawo gidan, ke kan Nazira yaushe zaki natsu ne ki daina wannan rawar kan naki ne?”
Nazira ta ɓata fuska cikin Muryar shagwaɓa take cewa
“Me na yi kuma yanzu daga dawowata Hajiya?”
Hajiyar ta zauna ranta a haɗe Basira ta fara gayar da ita ta amsa ba yabo ba fallasa, Nana ma ta kalleta cikin ɗar ɗar tace da ita
“Mun dawo Hajiya Barka da gida”
Hajiyar cikin haɗe fuska tace “Sannunku”
Nazira ta ɗauki akwatin Basira tare da riƙo hannunta tace
“Zo mu je sama ki huta kafin in kammala abunda zan yi mu fara tun kafin lokaci ya Ƙure muna”
Tana janta suna hawa sama take maganar, Nana a bayansu riƙe da ledar ɗinkin Nazira suka haye, Hajiya ta bisu da kallo zuciyarta cike da takaicin ƴarta Nazira, saboda ganin kamar bata san ciwon kanta ba kwata-kwata, don ta tsani saka Nana da mutanenta da take yi a jikinta irin hakan, ta kasa gano akwai tazara mai yawa a tsakaninsu tun tuni, ta dawo da kallonta a kan t.v’n dake falon yana aiki ta yi ƙwafa, a ranta tace
_”Ban san me yasa a kullum na kalli yarinyar nan nake jin faɗuwar gaba ba, bana sonki Nana bana ƙaunar ina buɗa idanuwana ina ganin shawaginki cikin gidan nan, ina tsoron ki zamewa Nazira musiba a rayuwa, don wannan shegen kyaun naki Ni kaina tsoro yake bani”_
Ta sauke ajiyar zuciya ta miƙe cikin matsananciyar damuwar da ta kasa ɓoyuwa a kan fuskarta, har zata haye saman ta dawo ta ƙwallawa mai aikinsu kira, ta iso jikinta yana rawa ta duƙa kanta a a ƙasa saboda bala’in tsoronta da take yi, Hajiyar tace da ita ta je ta kaiwa su Nazira abincinsu sama, kuma ta tabbatar da sun gama ta je ta fito da kayan.