Hausa NovelsLabaraiMusayar zuciyaMusayar Zuciya Hausa Novel

Musayar Zuciya Hausa Novel

Landi ta miƙe cike tsoron faɗan Hajiyar ta nufi kitchen, saboda saurin ta bar wajen kamar ta kifa ta shige kitchen, Hajiyar ta buga uban tsaki ta haye sama tana faɗin

“Aikin banza kawai”

Nazira kam suna shiga ta faɗa gadonsu cike da farin cikin da ke huda zuciyarta, tana ta ihun murna har da su ɗaga kafafuwa sama saboda nishaɗin da take ciki,, Nana ta zauna kan gadon ta fito da kayan da ke cikin ledar, ta fara yaba ɗinkin cike da jin daɗin yanda aka tsarashi komi ya hau dai-dai, Basira ma ta yaba ɗinkin sosai har da ɗaukar rigar ɗaya daga cikin ɗinkunan tace da Nazira

“Wannan zai yi pitting ɗinki sosai mutuniyar”

Nazira ta tashi daga kwancen da take ta sauko gadon ta karɓi rigar, cike da farin cikin da ya kasa ɓoyuwa a kan fuskarta ta ɗorata a saman jikinta tace

“Ai telan ya san aikinshi sosai, shi yasa bana jin haushin biyan kuɗi ko nawa ya faɗa, don na san ba zai sakani ciwon kai ba…..”

Sallamar Landi da wata mai aiki ne yasa duk suka mayar da hankalinsu kansu, cikin ladabi suka gayar da su suka ajiye kayan abincin zasu fice Ɗakin, Nana tana ƴar dariya tace da su

“Sannunku da ƙoƙari ƴanmatan Hajiya”

Su Landi cike da jin daɗin kulawar da take basu kullum, suka amsa sannun da ta yi masu sannan suka fice ɗakin da sauri, saboda tsoron su daɗe su yi laifi wurin Hajiyar.

Nana ta sauko ta fara Saving ɗin Abincin suna ci gaba da zancen ɗinkin yabon mai telar da zagin wasu marasa cika alƙawali, sun baje sosai dukansu uku sun ci Abincin sannan suka yi sallah, Nazira kam sai da ta yi wanka ta yi sallah, Basira ta baje kayan kwalliyarta ta fara aikinta cikin ƙwarewa, Nana ma tashi ta yi ta shige toilet ta yi wankanta sannan ta fito ta shirya, cikin wata doguwar riga haƙa ta ɗaura ɗankwalinta, sai dai ban da mayuka bata saka ko powder ba don haka take yi abunta kullum har ta saba, sannan ta zauna tana kallon yanda ake ta fente fuskar Nazira sai ƙara fitowa take yi Masha ALLAH.

Bayan an ƙare kwwlliyar ne ta saka ɗaya daga cikin ɗinkunan da suka karɓo, ɗanyen boil ne pink color mai ƙuna da ratsin golden a jiki ga ɗinkin ya hau jikinta sosai ba ƙarya, Basira ta yi mata wani disign ɗin ɗaurin ɗankwalin da ya ƙara fito da ita cas-cas, Nana da Basira sai yaba haɗuwar da ta yi suke yi tana jin daɗi, itama kanta da ta kalli madubi sai da ta ji ta burge kanta matuƙa, saboda yanda ta fito tamkar ba ita ba kai kace wata sabuwar Amarya ce, Nana ta fara fesheta da kalolin turaruka tana santin kwalliyar, sannan ta ɗauko waya ta fara ɗaukarta photuna cike da farin ciki sai jujjuyawa take yi, Naxira ta kalli Nana bakinta a washe tana dariyar jin daɗi tace

“Ke ma ki zauna ayi maki don ALLAH zaki yi kyau da irin wannan kwalliyar fa”

Nana tana saka photunan Naxirar a status tace da ita

“Yasin bana so nafi son ganina haka, don haka barni a yanda kika ganni ɗin nan, idan ma kin ga zan yi maki cuss da yawa shi kenan sai in yi zamana ɗaki ba sai mun gaisa da shi ba”

Naxira ta haɗe fuska tare da riƙo hannunta tace da ita

“Me yasa a komi kike nuna kin fi son in yi ke ba sai kin yi ba? Yanzu ita kwalliyar miye a ciki da ba zaki bari ayi maki ba?”

Ganin yanda ran Naxirar ya ɓaci ne Nana ta zare hannunta cikin nata ta zauna, sannan ta kalli Basira tana ƴar dariya tace

“Shafa man powder kawai tun kafin ta yi kuka tasa mu yi asarar kwalliyar”

Basira tana dariya ta fara shafeta da kalolin powder, Nana tace ita sam bata son wata doguwar kwalliya, ayi mata make up sama sama sai Oil lips kawai, Basira tana dariyar halin Nanar tace

“Wallahi Nana ina yi maki addu’ar ALLAH ya haɗaki da wanda zai ce kullum sai kin yi masa kwalliya kala goma”

Nana ta ƙwace kanta tare da kai mata duka tana faɗin

“Muguwar banza to yasin ko yana so ba yi masa zan yi ba tunda Ni bana ra’ayi”

Naxira ta zauna tana dariya tace

“Shareta kawai Basira don ta san tana da kyau ko babu kwalliya ne shi yasa take gudunta, amman yanda take ɗin nan ace tana kwalliya ai ko mu sai mun lalace gurin kallonta bale…….”

Kiran wayarta da aka fara yi ne ta daina maganar, cikin zumuɗi ta ɗauki wayar sannan ta ja gyalenta tare da saka talkama a ƙafarta tana faɗin

“My Bear Oyoyo! Ok jirani minti biyu..”

Sai da ta kai bakin ƙofa da gudunta sannan ta waigo tace da su

“Idan kun ji Ni shiru ku sameni a cen ku gaisa bye! ”

Ta fice ɗakin da sauri suna yi mata dariya.

Hmmmm danƙari wannan book tafe yake da cakwakiya mai wuyar fassara, tare da zazzafar soyayya mai tsayawa a wuya, a gefe ɗaya kuma akwai tausayi mai tsayawa a maƙoshi, don haka ku garzayo ayi da ku kar ku bari a baku labari.

 

 

Name: [ZUCIYATA HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button