NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 14 -15

       Duk abinda ke faruwa su walida naji, dan haka suka had’e kai a tsakar gida suna dirzar kuka.
    Itama Umma yana fita tafad’a kan gado ta fashe da kuka maiban tausayi.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

       Tunda Jiddah ta koma sashenta taketa juya maganar hajia deluwa a zuciyarta, da mamakin kalamun saurayi da hajia ta Kira da Ashir Wanda take kyautata zaton d’ansune kenan. Lallai ita taga takanta, mutanan gidan kowanne da nashi matsalar….
     Motsin dataji a bayantane ya sakata saurin juyowa, gabanta yay mummunar fad’uwa saboda ganin Ashir. Murmushi ya sakar mata yana matsowa gab da ita, “Auntyn mu gaisuwar bangirma nazo kawowa”. Yay maganar yana d’aga Mata gira d’aya.
       Baya Jiddah ta matsa sosai jikinta harya Fara tsumar tsoro, Ashir ya kuma kwantar da murya tamkar yana gaban matarsa ko budurwa yace, “Wani ya ta6a fad’a miki kinada k’yau kuwa babie? Da sabon jini kika dace babie ba dad ragowar basirba, kizo nabaki dukkan farin ciki dan nine dai-daike nasan dad babu abinda zai iya miki wlhy, shegen aure-aurensane kawai da basa k’arewa……”.
      Duk maganarnan da Ashir yake jikin Jiddah 6ari kawai yake, dan tsaf tagama fahim manufar Ashir a kanta, babu abinda takeyi sai Addu’ar Neman tsarin ALLAH daga shed’ancinsa, yayinda tuni hawaye sun cika Mata idanu. Ganin Ashir yamatso zai kamata yasata afkawa d’aki a guje Ashir ya take Mata baya…………..✍????  



????????turk’ashi, Uban ko d’an?.


*_Ammafa kun iya buk’ulu, irin wannan addu’a da kuke jama Maimuna kar Sheikh Ali ya angwance_*????????????





*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button