NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 18 – 19

 *_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
             _(ya dace ya gyara kansa)_
                 *_Bilyn Abdull ce????????_*

                   *_[18➖19]_*
…………..Duk yanda akaso nutsuwar Jiddah abin ya gagara, sai da y’an sanda suka kira Uncle yahaya waje
dansuyi magana sai akaga Jiddah ta lafa daga fisge-fisge da k’arar da takeyi. Hakanne yasaka Umma dake kuka son fahimtar wani Abu, amma batace komaiba tajigaba da tofama Jiddah Addu’a.
    Bayan kamar mintuna goma Uncle yahaya ya dawo, yana shigowa Jiddah ta tashi aguje zata bar wajen, rik’eta Zarah da walida sukayi da k’yar da taimakon Uncle yahaya suka kaita k’asa.
    Cikin kuka Umma tace, “Uncle d’insu ka fahimci abinda Na fahimta kuwa akan yarinyarnan?”.
     Kansa ya jinjina alamar eh, idonsa jajur shima saboda damuwa yace, “Maman Nafisa Jiddah batason maza su ra6i inda take, lallai akwai abinda ke faruwa dabamu saniba, dan dak’afa fa tazo gidannan tundaga can gidan. Kuma yanzu y’an sandarnan waifa anturosune su kamata saboda Alhaji garba da d’ansa suna asibiti sanadin kwala musu abu datayi. Amma halin da sukaganta a ciki yasakasu komawa”.
      Daga Umma harsu walida kuka suka kuma fashewa dashi, Uncle yahya yace, “Ba kuka zamuyiba Maman Nafisa, bara naje nayi sallah nazo da malam Alfah”.
         Da to suka amsa.
Uncle yahya yafice zuciyarsa cikeda tausayin Jiddah. Tunda ya fita sai Jiddah takuma samun nutsuwa, dan haka su Umma suka kamata zuwa d’aki saboda mutane makwafta dasuke shigowa jajanta abin, wasuko gulmace ta kawosu.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

            A asibiti kam da k’yar aka samu jinin dake zuba a kan Alhaji Garba ya tsaya, shiko bala sunama zuwa ya farfad’o, dan baiwani buguba sosai, allurar barci sukai masa danya samu Hutu.
            Ran Hajia Deluwa da Ashir kam yakai k’ololuwar 6aci, musamman ma da y’an sandan sukazo suna Kora musu bayanin wai ai Jiddah ta haukace, suko tayaya zasu Kama Mara hankali. Tamkar Ashir ya makesu haka yaji, hajia deluwa kuwa datasan abinda ya faru komawa tai gefe takira malaminta tace ya warware asirin dayay ma Jiddah, amma yayi wani Abu akan Alhaji garba danya Saki Jiddah, tanason akama Jiddah aimata hukunci.
      Da to kawai ya amsa mata, danshifa akwai abin tsoroma dayake hangowa gameda wannan abin da suka aikata, shiyyasama tunkan ta kirashi ya warware Na warin ja6a da jiddah keyi, saurama d’ayan.
        Shima Alhaji garba wajen karfe tara aka samu ya farfad’o, alurar barci suka sake masa danya samu nutsuwa.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

       Bayan an idar da sallar magriba Uncle yahya sukazo shida malam alfah, kallo d’aya yayma Jiddah yafahimci akwai sihiri a jikinta, dan indai daga ita saisu Umma ne zakajita luf, da namiji yashigo gidan zata hau ihu da fisge-fisge. Addu’oi yabada kafin safiya asan abinyi.

         Tunda aka bata ruwan addu’ar sai barci ya kwasheta, bata kuma sanin inda kanta yakeba har asubahi. Yayinda su Umma suka kusan kwana a tsaye suna Kai kukansu ga ALLAH.
          Washe gari Alhamdllh jikin nata, dan dakanta tai alwala tagabatar da salla.
    Bayan ta idar ne Umma tabata Qur’an, babu musu ta amsa tana karatu, har wajen awa d’aya kafin ta ajiye tahau yin azkar. Duk wannan abun dake faruwa y’an uwanta na zagaye da ita, saida ta kammala sannan ta gaida Umma, su Zarah suka gaidata suma suna rungumeta danjin dad’in ganinta normal.
    Babu Wanda yay Mata magana akan matsalarta, saima itace ke cewa “wai Umma ya akai nadawo gidane?”.
     Murmushi Umma tayi tana Kama hannunta, murya a tausashe tace, “Uncle d’inkine ya d’akkoki Jiddah”.
     Murmushi ta d’anyi amma batace komaiba. Ana cikin haka sukaji sallamar Uncle yahya, atake jikin Jiddah yafara rawa tashiga matsawa baya.
     Uncle yahya yad’an murmushi kawai, cikin k’arfin hali yace, “Haba jiddodona ninefa, ko baki ganeniba?”.
       “Na ganeka Uncle”. ‘tai maganar murya a raunane tana cigaba da matsawa’.
       “Kinga yi hak’uri karkiyi kuka, amma fad’amin tsorona kikeji?”.
       Fashewa tai da kuka jikinta Na kuma tsananta rawa, “Uncle kayi hak’uri, wlhy banason ganin maza ko muryarsu banason jiiiiii!!!!!!!”. ‘Ta k’are magar cikin razananniyar tsawar data gigitasu’.
      Dole sai fita Uncle yahya yayi, yana fita kuma tafara dai-daita, a hankali saita dawo normal, jikin Zarah dake kusa da ita tafad’a tana kuka, suma su Zarah kukan sukeyi.
         A waje Uncle yahya da Umma suna magana ne akan ya Kira Abba ya sanar masa halinda Jiddah take ciki amma yace wai k’arya takeyi, dan haka shikuma ya faffad’a masa magana akan wlhy koda zasuyi yak’i Jiddah bazata koma gidan Alhaji garba ba, dolene ya saketa koyanaso ko bayaso.
      “Kamin dai-dai Uncle d’insu, wlhy a shirye nake da igiyar aurena ta tsinke akan komawar Jiddah gidancan, acikin sati uku kacal an maidata haka inaga nan gaba kuma?”.
      “Ki kwantar da hankalinki Maman Nafisa, nima ina dai-dai dashi ai, dan yace gobe zai dawo daga legas d’in”.
        “ALLAH ya kawoshi lafiya”. Cewar Umma a zafafe.


*_HARGITSI_*.

           Dolene mukira wannan tsakani da suna hargitsi, dan kuwa komai ya rikice, ga jikin Jiddah da yak’i dad’i, dan koda maganar Abba daya dawo washe garin dawowarta gidan Alhaji Garba taji to zata fara fisge-fisge da k’ara.
     Tsakanin Umma da Abba da Uncle yahya kuwa anyi barank’an-barank’an, dan Abba yaje ya duba Alhaji Garba a asibiti ya shirys masa k’arya da gaskiya akan Jiddah, yayinda hajia deluwa ke tunzurashi a gefe.
     Umma da Uncle yahya sun dage sai Alhaji Garba ya saki Jiddah. Alhaji garba ya kafe akan wlhy bazai ta6a sakintaba. Abba ma yadage sai Jiddah ta koma, dan shima akwai nasa dalilin Mai tada hankaki.
     Lamari yayi tsamari sosai, yau kusan kwanaki takwas da Fara badak’alar amma babu wani sassauci, hakanne ya saka Uncle yahya shigar da Alhaji Garba kotu domin raba auren Jiddah.
      Alhaji Garba yasamu sauk’i harya koma gida, dan haka gidansa akakai masa sammaci.
     Sosai hajia dealuwa ke zubar masa tijara akan ya Saki Jiddah mana, aiba girmansa bane ace yashiga kotu akan wannan banzan maganar.
     A zafafe yace, “ke Yahanasu, nifa ba auren wannan yarinyar bane matsalata, kud’ina da Ubanta yaci sune matsalata, kinsan nawa ya amsa a wajena kuwa? To naira miliyan Hamsin, ya amsa yabiya banki bashin da yaci, bisaga wannan ne yabani aurenta akan zai biyani rabi nanda shekara biyu, nikuma nace Na hafe masa rabi, dan haka saiya biyani kud’ina Zan saketa”.
         “Humm wlhy Alhaji ban ta6a sanin Kai mayen Mata baneba sai yau, akan mace ka d’auki wannan uwar dukiyar ka bashi? To bara Na fad’a maka, rashin sakin y’arsa ba shine mafitaba, dan dama can bason Y’ar yakeba, kobakaga damuwarsama ta dawoba a kullu? To ka saketa, nikuma Zan baka dabarar da zakayi kud’inka su fito cikin sauk’i a hannun Alhaji zakari yaro”.
     Jimmm Alhaji Garba yay yana kallonta, saikuma ya gyara xamansa yana fad’in “kamar kuma Na yarda da shawararki, ke nama yarda, samomin takarda da alk’alami”.
    Da hanzari hajia deluwa taje ta d’akko masa, dandanan ya zana Saki a takarda yabata yace tabama driver yakaima Alhaji Zakari.

*_SANADI_*
     
      Wannan shine sanadin rabuwar Alhaji Garba da Jiddah.
    Su Umma Na tsakar gida zazzaune, Zarah da Walida na wanke-wanke, Umma Na girki yayinda Jiddah ke kwance akan tabarma tayi shiru tana tunanin rayuwa da yanda al’amura suka sauya cikin wata biyu kacal. Sallamar Abba ce ta sanyata mik’ewa zumbur, da gudu ta afka d’aki tajecan karshen gini ta 6uya. Yanzu haka take, ko Uncle yahya ne ya shigo saita gudu ta 6uya, addu’oin da malam alfah ke bata tanasha yasa aka samu rangwame tabar yawan k’ara, amma idan Namiji yacika kusantota tana wannan fisge-fisgen harma ta suma.
         Cikin hargowa Abba ya jefama Umma takardar sakin Jiddah yana fad’in “Hankalinki ya kwanta yagana, kin kashema Jiddah aure, saiki zuba ruwa a k’asa kisha kinji ko, itakuma daga yau dan Ubanta saita dainama mutane haukan k’arya, kuma wlhy kinji Na rantse Na zare hannuna daga duk wani lamarin Jiddah, ta nemi wani uban baniba d……..”
       Cikin katseshi Umma ta d’aga masa hannu ”Ya Isa haka Alhaji, dama baka a lamarinsu, dankuma ka fita yanzu bazanji komaiba, amma ina Mai tabbatar maka, ko watan watarana katina wannan maganar taka, sannan ka fad’ama Alhaji Garba, ina godiya matuk’a ni yagana akan sakarmin yarinya da yayi, kaikuma ka gane TUBALIN TOKA baya k’arko, duk abinda ba’a ginashi domin ALLAH ba to baya k’arko, abinda kuma akaima yarinyata nabar wannan ga ALLAH, shine zai Mata hisabi da koma wanene”.
     Umma nagama fad’a tai shigewarta tabi Jiddah, sukam su Walida dama tuni sun shige ai, daga d’aki suke jiyo abinda ke faruwa.
    Kwafa kawai Abba yay batareda ya iya cewa k’alaba, sai yanaji a ransa badan ALLAH ya Isar da mamansa taimasa akan yagana ba da wlhy yau itama Saki Uku zai Mata, to amma anriga an saka masa Kara da hakan.

      Duk wani masoyin Jiddah ya tayata farin ciki da wannan Saki, washe Gari da aunty Nafisa tazo itakam harda rawarta tasha su Zarah na tayata, Jiddah da Umma sai dariya suke musu.
    Tuni maganar sakin Jiddah ya karad’e dangi, kowa yaji dalili saiya tayata murna da hakan, tareda nemawa abba shiriya wajen ubangiji.
     A yanzu matsalar Jiddah ta tsoron mazace kawai matsalarsu, dan har yanzu bata shan inuwa da koda sautin muryar mazane, iya kokari kuma ana maganin akan warware sihirin jikinta, amma lamarin ba’a cewa komai sai sambarka.
     Abba dai ko sisinsa babu balle tambayar Yaya Jiddah hasalima yabar zuwa gidan gaba d’aya, shi a dole fushi yake, sannan ciwon Jiddah yace k’aryane. Kokad’an hakan baya damun Umma, dan a cewarta wannan matsalarsace.
       Alhamdllh jikin jiddah yad’an murmure daga ramar da tayi, saidai kulum tana gida bata fita ko ina, zuciyarta nason komawa makaranta, amma tanajin tsoron yanda zata fiti taci Karo da abokan gabarta maza.
      Ahankali kuma farin cikin gidansu ya dawo, sunkoma tamkar da, saima ka d’auka wani tashin hankali bai ta6a ziyartarsuba a kwanakin baya, yanzu fatansu kawai ALLAH yabama Jiddah lafiya ta koma normal.
        
*_A KWANA A TASHI_*

      babu wahala wajen Ubangiji, yau ga Jiddah tagama iddah, har wani d’an walima su Zarah da aunty Nafisa suka shirya Na murnar Jiddah tarabu da alak’ak’ai.
     Umma dai dariya kawai suke bata, Uncle yahya harda taya 6era 6ari kuwa shida maman Sadiq.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

           “Mustafa yanzu ya kake ganin zamuyi akan maganar wadda zataje musabak’arnan ta Saudia tunda yanzu babu yarinyarnan? Kagafa wasu kwanakine kawai ya rage Wanda bazasu gaza ashirin da biyu ba, a ko yaushe kuma za’a iya buk’atar ganinta ma”.
       “Wlhy malam nima abun Na damuna, shiyyasa nake kuma takaicin rashin Jiddah, amma yanzu inaga zamu samu wata d’alibar mukuma horata kawai”.
      “Eh to shawararka tayi sosai, ALLAH yasa mu dace”.
       Ameen Malam mustafa da Sheikh Aliyu dake zaune yana saurarensu suka fad’a.
    Daga nan wani zancen suka d’akko, mafi yawa akan gudunmawar da Jiddah tabama makarantarne Na ciwo musabuk’ok’i kashi-kashi da tayi. Shidai Aliyu na zaune yana nazarin wani littafi yana saurarensu, amma k’ala bai tofa ba, dan ba huruminsa baneba. Sai dai k’ok’arin yarinyar ya burgeshi kamar yanda su malam suke fad’a dukda bai santaba.
    

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

         Yau  Su Zarah duk suna makaranta, gashi Umma nason yin aike shago, Dauda kuma baikai ga zuwaba, rasa yanda zatayi tai, ta lek’a kozata samu yaro amma layin fetal yara duk suna makaranta. Dawowa tayi ta kalli Jiddah daketa hidimar d’aura abincin rana.
      “Jiddah koda kanki zaki fita dai siyen yis d’innan, kinga nariga nafara kwa6a fulawar alkubus d’inan, ki lek’a konan shagon sama’ilane, idan kuma kingamu da wani yaron saiki bashi ya sayo”.
      “To Umma kawo naje d’in”. ‘Jiddah tafad’a tana d’auraye hannunta data ta6a gawayi’. Tana gamawa ta kar6a naira d’arin hannun Umma taja hijjab a igiya ta fita bayan ta d’aura Nik’ab tamkar yanda ta Saba.
      Dukda tsoron dake addabarta da tsumar da jikinta yafara haka ta k’arasa shagon sama’ila, da k’yar ta iya mik’a masa kud’in tana fad’a masa abinda takeso, lokacin daya mik’o mata hannunsa yad’an ta6a Nata kad’an sai kawai tai baya jiki Na rawa, bai ankaraba kawai yaga ta zuba da gudu tabarsa rik’e da yis.
     Mamaki da al’ajab suka kamashi, dan haka yabiyota yana kwala Mata Kira, amma ina gudu take iya karfinta. 
     Umma Na gyara mata wutar sai kawai gani tai ta shigo a guje, tana tambayarta lafiya amma bata sauraretaba ta afka d’aki. Umma na shirin binta Sama’ila mai shago ya rabga sallama daga soro.
     Wata razananninayar k’ara jiddah ta fasa tana toshe kunnenta. Tuni hankalin Umma ya tashi, dan ita tashagala Jiddah ta samu sauk’i sosai, dan tadad’e batai irin wannan firgitar mai karfi hakaba.
        Jikin Umma na rawa ta lek’a dantaga wake sallama, ganin sama’ila saitake tambayarsa komi yafaru da jiddah?, iya abinda ya sani ya sanar mata, sannan yabata yis d’in ya juya.
     Dole Umma ta kira Uncle yahya a waya, babu shiri yabaro kasuwa, tsayawa yay suka taho da malam alfah.
     Tunda suka shigo gidan malam Alfah yaga halin da Jiddah take ya girgiza Kai kawai.
       “yahaya inaga yakamata mukai Jiddah wani waje, bak’in aljanin da suka had’ata dashi yanada matuk’ar naci, tunda munyi namu ba’asamu warakaba yakamata mu gwada wani wajen kuma nakega”.
       “Malam duk yanda kace haka za’ayi, mu mun aminta dakai d’ari bisa d’ari, Kai Ubane a garemu, ko bama kusa zaka iya zartar da komai akan jiddah”.
       “Nagode da wannan karamci, yanzu ita mahaifiyar tata saitai k’ok’arin fidda mana ita zuwa mota”.
      Da k’yar Umma ta iya fidda Jiddah, daga k’arshema saida taimakon Uncle yahya, aiko Jiddah sank’ame musuma tayi amota.
         Tafiya sukayi sukabar Umma a gida…………✍????






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button