NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 27 – 28

      Uncle yahya bai zame ko inaba sai gidan Umma, ya iske ita kad’aicema a gidan, tana falo zaune tana sauraren redio.
     Zama yay suka gaisa kafin yaymata bayanin komai kamar yanda yaji.
     Umma zata birkice masa yace, “Kinga kwantar da hankalinki Maman Nafisa, ni nasan matakin dazan d’auka akan Yaya wannan karon, bayace kafin sati biyun da mukasa zai d’aura Mata aure ba, toni kafin sati d’ayan dayasa nima Zan d’aura mata”.
        “Oni Yagana, wai Alhaji kuwa yasan miyakeyi? A ina yata6a ganin nema akan nema? Balle wannan da harma an biya sadaki? Anya kuwa lokaci baiyiba dazan raba jaha dashi?”.
     “A’a dan ALLAH kibar fad’ar haka Maman Nafisa, ki duba yarannan dake suke kallo suji sanyi a ransu harsu Nafisa dabake kika haifesuba, mucigaba da masa Addu’a, dan son zuciyane kawai ke d’awainiya dashi, ita kanta hindun nasan akwai dalilinta nayin hakan, amma mu insha ALLAHU a garemu alkairi zai zama”.
       “To ALLAH ya rufa mana asiri, wlhy ni sam Uncle d’insu bana ganin laifin Hindu, dan tunkan zuwanta gidannan yake fama da mugun halinsa, ita idan kagama ta aikata d’orata akayi a layi”.
      “Wannan gaskiyane Maman Nafisa, ALLAH dai ya rufa mana asiri, ni bara naje wajen malam d’in mu tattauna, daga nan zan wuce kasuwa”.
     “To ALLAH ya tsare, ya raya mana su Sadiq yabiyaka da mafificin alkairi kaima”.
     Da amin ya amsa yana ficewa.


★★★★★★★

       Kai tsaye gidan Malam Uncle yahya yanufa, dukda ya iskeshi da bak’i haka yasaka aka kai Uncle yahya falonsa ya taso ya saurareshi.
    Bayanin dazai gamsu shima yay masa, shikansa malam ya girgiza da lamarin Abba, amma saiya bishi da addu’ar fatan shiriya kawai.
     Sun k’ark’are magana akan zasu d’aura auren ranar juma’a bayan sakkowa masallaci, nanda kwana 4 kenan, kuma Abba zakari bazai saniba sai a wajen d’aurin auren.
     Daga baya idan an kimtsa Jiddar saita tare.


★★★★★★★

      Koda Aliyu ma yazo da yamma haka malam ya sanar dashi sun dawo da d’aurin aure Juma’a.
     Kansa a k’asa ya amsa da “ALLAH ya kaimu baba, ALLAH yasa haka shiyafi alkairi, duk yanda kuka yanke yayi”.
    Malam ya jinjina kai yana saka masa albarka.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

      Yau dai kam malam Aliyu yasan dolene ya danne zuciyarsa yayma Maimunatu bayani yanda zata fahimta, dan yanason saiya gama da matsalarta kafin yaje ga waccan sarkin kukan (Jiddah????).
     Yau jikinta dad’an sauk’i, saidai abinda ba’a rasaba irin Na Mai laulayi.
      Kamar yanda ya saba ya bud’e Mata hannayensa ta shige sunamai begen juna.
     Bayan ya watsa ruwa sun dawo fallo takawo masa kayan marmarinsa, gefe takoma ta zauna, dan yanzu bata iya sha ita, ganin yayi shiru yakasa sha yanata kallon fruits d’in saita taso tadawo kusa dashi.
     ‘Dago fararen idanunsa yayi yana kallonta amma baiyi maganaba.
     Tad’an langa6e kanta gefe cikin salon kwantar da hankali tace, “Wai mike damunkane Annur? Kwana biyunnan nalura Abu Na damunka amma kana 6oyewa”.
      Ajiyar zuciya ya sauke yana juyowa sosai gareta, “Maimoon ba 6oyewa nakeba, kawai dai ina tunanin ta yadda Zan fidda maganar ne gareki, dan bansan Yaya zaki d’auketa ba, kinsan Ku Mata duk dad’in zamanku da miji akazo wannan ga6ar idonku rufewa yakeyi”.
     Cikin d’an nazartar maganarsa tace, “Indai nice bazaka fuskanci hakan daga gareniba insha ALLAH Yaya Aliyu, akoda taushe Zan kasance Mai biyayya a gareka da girmama buk’atarka, kodan nasamu rabauta a wajen ubangijina da gamawa da wannan rayuwar Mai tak’aitaccen kwanaki lafiya”.
       Jawota yay jikinsa ya rungume sabodajin dad’in kalamanta, “Nagode gimbiyata, ALLAH yaymiki albarka, ina sonki da k’aunarki fiye da tunanin Mai hankaki”.
       Maimuna dai Na saurarensa, yayinda a gefe d’aya zuciyarta ke tunanin mike faruwa? Kodai rabuwa zaiyi da itane?…….
    Tunaninta ya katse lokacin da Aliyu ya d’agota daga jikinsa.
      Hannayenta ya rik’e cikin NASA, idanunsa a k’asa dan kimarta tawuce ya kalli cikin idonta yafad’a Mata zai k’ara aure. “Maimoon Zan k’ara aurene”.
     Wata zabura tayi tana cire hannunta daga cikin nasa, yayinda tuni wasu hawaye masu zafi sun Fara bin kumatunta, tana niyyar mik’ewa yakai hannu zai ruk’ota, amma saita kauce tashige d’akin baccinta da gudu.
    Kansa ya dafe a hankali ya furta “Ya salam”.
      Kasa tashi yay a wajen kusan minti talatin, saida ya tabbatar inma kukane take, tayi Wanda zai rage nauyin da zuciyarta tayi, kafin yamik’e ya bita.
      Zaune ya isketa saman stool d’in mirror ta kifa kanta akan Mirror d’in tana shashshekar kuka..
    Yad’an dad’e tsaye a bayanta yana kallonta, kafin yasaka hannu ya d’agota zaune sosai. Yanda fuskarta tai jajur sai tausayinta ya kamashi, kafad’unta ya Kama ya mik’ar da ita tsaye, yaja hannunta zuwa saman gado, koda suka zuna saiya sakata a jikinsa, ya saka hannayensa yana share Mata hawayen.
         “Haba Maimunatu, mumini Na k’warai shike kar6ar dukkan abinda yazo a shari’ance garesa koda yana kallonsa k’untata a rayuwarsa, kefa Mai ilimice, iliminma Na addini, sannan ALLAH yayiki cikin Mata masu hankaki da Nisan tunani, nasan kishi abune Mai zafi, amma idan muka gaurayashi da hak’uri da k’yautata zaton Alkairi a junanmu saimu sameshi da sauk’i, kisaka a rankin mijinki Na matuk’ar sonki, kuma insha ALLAH zaiyi adalci agareku, itama wadda zata shigo matsayin k’anwa a gareki ki k’yautata Mata zaton samunta Mai k’yawun hali da fatan zamu zauna lafiya, dan ALLAH ki kwantar da hankalinki kodan babiena dake tare dake, badan bana sonki bane zanyi aurennan, bakuma dankin gazamin a komai baneba, kawai dai kisaka a ranki San k’ara aure ga kowanne namiji tamkar an haliccemu dashine, dan ALLAH kiyi koyi da halin matayen MANZON ALLAH (S.A.W), hakan shine zaikuma girmama k’aunarki a raina, dan abinda Mata basu ganeba, shirme da sukeyi yayinda mazajensu zasu k’ara aure shike janye k’aunarsu da tausayinsu a zukatan mazanma gaba d’aya, amma idan kika kwantar da hankalinki saikiga Mijin Nata k’ok’ari danya faranata miki Yakuma kare martabarki ga wadda zata shigo, dukda dai nasan akwai azzaluman maza da inhar zasu k’ara aure burunsu shine su wulak’anta matayensu Na gida, suyita tozartasu gaban yarinyar da zasu aura, wannan kuma ba daidai baneba zaluncine, kuma sai ALLAH ya sakama Matar, shiyyasa saikiga yarinya kanta shigo babban burinta shine data shigo ta kori Matar gidan, kinga tunkan tazo cikin gidansa ya gama wargaza farin cikin gidansa gaba d’aya. Nidai insha ALLAH bazan kasance irin wad’annanba Maimoon, dakinga kuma Zan kauce kiyi azamar maidoni, dan kinada kima da daraja Mai yawa a zuciyar Aliyunki wlhy”.
     Tashi zaune maimuna tayi sosai tana k’ara share hawayenta, ”Kayi hak’uri Yaya Na fahimceka, ka yafemin tasowar danai Na barka d’azun, wlhy Yaya kishi Nada zafi, dama Ashe haka duk wadda za’aima kishiya takeji Yaya?, Yaya kamin Addu’a ALLAH yabani ikon jurewa, wlhy ina sonka sosai, amma hakan bazai sakani bijirema ubangiji naba, domin yayimin dukkan ni’imarsa…..”. Tak’are maganar da k’ara fashewa da kuka.
    Jikinsa ya jawota ya rungumeta tsam, tsantsar tausayinta da k’aunarta na ratsashi, sun dad’e a haka kafin ya d’agota ya mik’e, ruwa ya d’ebo a Kofi ya dawo ya isketa zaune inda ya barta tana cigaba da zirarar da hawaye, alkur’ani ya d’akko ya bata sannan yakoma ya zauna yana Mata nuni data karanta, batayi musuba tabud’e tafara karantawa a zuciyarta tana cigaba da hawaye, yayinda shikuma yake tofa Mata addu’oi a ruwa yana kallonta.
        Yadad’e yanayi, yana kammalawa ya kar6i alkur’anin yabata ruwan addu’ar, kar6a tayi ta shanye tana masa murmushi, dan tad’anji nauyin zuciyarta ya ragu.
     Koda ta shanye ruwan addu’ar saiya jawo kayarsa jikinsa yashiga nuna Mata tsaftatacciyar soyayya. (daganan naji bulum????⛹‍♀).
      Saida yakuma bata nutsuwa da kuma jaddada Mata k’aunarta dake ransa sannan suka dawo falo yasha fruits d’in……………✍????




⛹‍♀⛹‍♀duk Wanda naji ya zagi Maimunatu yau dashi za’a biya bashin Abba zakari????????????.


_Maman Salma sak’onki ya iso ga bilyn Abdull, ina godiya kwarai da gaske da addu’arki, alkairin ALLA YAKAI gareki aduk inda kike a fad’in duniya????????????????????????❤????????????????_.







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button