NOVELSUncategorized

KWARATA 68

???? —— 67

         Biyu zuciyata ta kasu yayin da wani sashe yake cewa Sultana kada soyayya yasa ki manta da irin halakcin da Kawu yayi muku , kuna banzace a gidan Baba babu cin yau babu na gobe bare na anjima kaf ahalin Inna sun watsar
daku basa shiga sabgarku amma Kawu ya shigo rayuwarku yana taimaka muku , Sultana ya sakaki makarantar boko da islamiyya , yana tare daku yana tsotse duk wata damuwarku yau rana tsaka kwatsam sai ya nemi alfar wurinki kice a , a ? Yaga kina tangaririya rayuwa tana ta wurgel dake ance miki karuwa ɓarauniya kidahuma jahila baki fito tsatson mutunci ba amma yace yaji ya gani a hakan yana so ma ɗansa ke , ga “yar uwar Innarki sai tada jijiyon kai takeyi nata bazai auri na banza ba haba Sultana ki so sa don Allah ,

      Ajiyar zuciya na sauke yayin da wani sashe na zuciyata ya fara haskomin rashin mutuncin Dikko kai tsaye yake gargaɗina da ke Sultana ina hankalinki yake so ya tafi ? Dikkon me ? Mutumin da bai san komai ba sai rashin mutunci duka zafin kai , babu dariya bare fara’a kullum fuska a haɗe yanayin fushi da farin ciki iri ɗaya  , ga matsalar aljannu yanzu ƙarshe ki zaɓi Dikko wani abu ya haɗaku yayi miki tsinannen duka yace ki bar masa gidansa ina zakije a lokacin ?

       Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un sam Dikko bazaimin haka ba , taya ma wai zai fara korani ? Yama zauna dani babu aure kuma yayi haƙuri dani bai koreni ba sai da yake aurena zaice na tafi ? Zuciyata tace ai wancan zaman bana aure bane ba yasan zaki iya tafiya ko wane lokaci amma zaman aure daban ne haba Sultana yaufa da gobe ake magana , raba kanki da yau da gobe zama ne zakuyi daga nan har mutuwa , kifa tuno rashin mutuncin Dikko babu imani a rayuwarshi duk sissiye gidajenku da yayi har kin manta Sultana ? Babanki da kika fi so fiye da komai a duniya Dikko ya watse shi da ruwan dake kwance saman ƙasa , Babanki mai sanki ya mareki saboda Dikko ? Me ake da Dikko …?

      Zuciyata ta kasa bani mafita , alkairin Dikko ɗaya ta kasa haskowa rashin mutuncin Dikko kawai take gani yayin da take harzuƙa ni tana tambayata ina maganar ɗaukar fansar budurcinki daya kece miki ? Kin fasa ramawa a shekara biyun ne ? Abinda ya faru dani dashi a ranar daya ɓanɓare min budurci ta ƙarfi da yaji ya dawomin kamar yanzu ne yakeyin abun dani , da sauri na rufe idanuwana naci gaba da kuka zuciyata tana ci gaba da huramin wutar ƙiyayyar Dikko ,

      Da sauri na goge hawayena na shiga cikin palon da sallama , gaba ɗaya na gaishe su nayi ma Kawu sannu da zuwa na wuce , Maryam yaki , kawu ya kirani , gabanshi naje na durƙusa a saman ƙafafuwana cikin ɗa’a da ladabi , Maryam ai kin sanni ko ? Murmushi nayi ba tare dana kalleshi ba nace na sanka mana sosai , idan na baki guba zaki iya ci ? Cike da ƙwarin guiwa nace me kuwa zai hana Kawu ? Ai ba guba da zanci a abinci ko abun sha ba wuta idan ka hura kace na shiga sai nayi maka godiya zan shiga cikinta cikin aminci da salama Kawu , kallona yayi sosai cewa shin wani irin soyayya kike ma “yan uwan mahaifiyarki ? Goge hawaye nayi tare da cewa ina musu soyayyar da bana iya fasalta irinshi domin su ahalin uwa jigo ne mai girma ko soyayyarsu daban yake a zuciyata , tun kafin na sansu na gansu kullum mafarkina na gansu ina alfahari dasu kuma dana kasance a cikinsu inayin farin ciki bana fatan rabuwa dasu har abada dan su ɗin mutane ne masu mutunci da nuna soyayya akaina…

Yayar Inna tace kunji makirci ko ? Tou mu bama sanki gidan uwar wa muka nuna miki so ? Ke nan “yar tatsiyar alhaki dake har kin iya makirci , bama sanki bakya sanmu amma tsabar ƙwarewa da bariki mu zaki ma bariki ? Tou uwarki ma kanta a gabana aka haifeta ki sani ni nasan kina nan kinaji kamar ki cakamin wuƙa na mutu ,

     Murmushi nayi mai ciwo tare dayin magana a zuciyata nace tabbas hasashenki gaskiya ne , amma a fili nace haba Inna aiko da duniya tayi tirr da Allah wadai da dani , magana ce na faɗa mata ita da take cewa bata so na kuma a matsayinta na Yayar mahaifiyata….

     Kallona Kawu yayi sosai tare da cewa shin zaki iya auren ɗaya daga cikin ahalin mahaifiyarki kuwa ? Kallonshi nayi tare da cewa me kuwa zai hana idan har ya ganni nayi masa…! Idan ya ganki kinyi masa shi kuma ke bai miki ba fa ? Karka damu Kawu nayi alƙawarin sadaukar maka da kaina duk abinda kake so zan aikata , duk uwa sunanta uwa yayar uwa da ƙannen uwa duk iyaye ne yunwa mai tsanani da kewar abinci ya kamani , tsananin yunwa bana iya tashi ko ƙwaƙwƙwaran motsi bana iyawa ina kwance ina jiran mutuwa tazo , sai ga “yar uwar mahaifiyata tazo da ƙwano riƙe a hannunta sai tace “yata na ganki kinajin yunwa sosai wannan ƙwanon yana ɗauke da abinci mai daɗi na taho dashi na baki sai kuma naji nima ina da buƙatarshi kiyi haƙuri ni naci ke kuma ki jira wani ,  ita tafi ni jin ƙwarin jiki tunda har tana iya tafiya ni kuma bana ko iya tashi tsaye saboda yunwa ga kuma ƙamshin abinci yana ta dakar min hanci amma sai ta hanani bayan taga ni nafita buƙata , ta san wannan abincin shine rayuwata idan ta hanani zan iya mutuwa a ko wane lokaci amma ina kallonta ta zauna ta cinye abincin nan kaf a gaban idona tayi min ƙwalele sai nayi haƙuri , 

     Ina nan kwance na kusa mutuwa sai gata ta sake shigowa da wani kwanon abincin shima sai ƙamshi yake , sai ga ɗan uwa mahaifiyata shi kuma ya shigo da nashi abincin amma sai yace Sultana gashi kici amma kiyi haƙuri ya fara yami naji ance min kina nan yunwa zai kasheki shine naje na samo miki wannan kici dan ki rayuwa , saina ansa zanci sai wannan “yar uwar ta mahaifiyata ta ajiyemin nata kwanon tace kici wannan shine sabo bai lalace ba karki ci nashi zai lalata miki ciki , tou faɗamin wane zanci a ciki tsakanin mai kyau ko mai yami ? Wanda baiji tausayin karka mutu ba saiya tausaya maka saboda lalacewar ciki….?

      Gaba ɗayansu shiru sukayi suna kallona babu wanda ya bani amsa , kallon Kaka nayi nace Kaka wane zan ɗauka inci a ciki ? Cikin muryar tsufa tace ai wannan lalataccen shi kawai ya kamata kici , murmushi nayi na kalli Kawu nace abun mamaki shi ɗan uwan mahaifiyata yace abincin yayi yami amma ina dubawa sai naga ya fara tsutsa shin Kaka naci kona fasa ? Kaka tace ci kuwa , Kaka sai ita Yayar uwa ta buɗemin nata kwanon sai naga farfesun kaji ne da zafi ga ƙamshi tana kici wannan ki bar wancan ? Kaka tace kajin nan kuwa basa ciwuwa a gareki , dariya nayi na kalli Kawu nace ina fara cin abincin nan kawai sai ya koma min daddaɗa ina san duk wanda zaka bani ina san sa , ina sanka ina alfahari da kaf ahalin mamana fatan alkairi a gareku iyaye na gari , ???????? ina kaiwa nan na miƙe nabar palon.

      Ina shigewa Yayar Inna tace tou na gane wato habaici tayimin yarinyar can ? Nice na cinye abincin dan ki mutu tunda nace ɗana bazai aureki ba , shegiyar yarinyar makira munafika wannan idan ta auri ɗanka aisai ta rabaka dashi har abadan duniya , Kawu yace babu gudu babu ca da baya sati biyu masu zuwa zan ɗaura musu aure , ƙarshe dai saida rayuka ya ɓaci kowa ya tafi Kawu yana cewa zai turo Sultan idan Allah ya kaimu su gaisa…..

      Sai ƙarfe 2:19am na buɗe wayoyina kuma a dai² wannan lokacin nahau online na cire hoton Dikko dake a d p ina na saka hoton fulawa , layin Dady na kira yana shiga ya ɗauka yace baiwar Allah tun ɗazu nake kiranki wayarki a kashe , nace bari kaidai wurin yi maka record in maganar abokinka suka kusa kasheni shida Sultana shi yasa na rufe wayar na gudu dan tsira da rayuwata yanzu na samu wuri na tsaya haka nan na gwada sa’a har ina tunanin idan na kiraka a tsakar dare kamar nayi hauka ma ,

     Dady yace ai ni tuni nayi bankwana da bacci matsaloli suna neman kunnomin kai , na yadda da Bello 100% tun yana matashi nake tare dashi amma yau rana tsaka zai tattara wannan mutuntakar ya zubar , Hmmm ai danma bakaji abinda yace maka ba , kuma ya buɗe kaff wasu ɓoyayyin surruka yana faɗawa ita Sultana , Dady yace wai me yake cewa ? Ina zuwa na faɗa tare da tsinke wayar , canja layikan nayi layin Dikko zuwa cikin wayar da Dady ya bani , layin Dady zuwa cikin wayar da Dikko ya bani , bayan na gama na kirashi ya ɗauka.

     Da babbar wayata na kunno mishi maganar Bello , yaji Bello yana cewa wannan shine ƙudirina da kowa wace daƙiƙa saƙo da lungu rana da dare neman sa’ar mutuwarsa nake saina kashe shi…..

    Dariya Dady yayi tare da cewa shirmen banza shirmen wofi akan kaina dukiyata da iyalina zan iya shafe labarin duk wani banza daga sahun masu lumfashi a duniya , speaker na saka wayar na kara babbar wayata na fara ɗauka , Dady yaci gaba da cewa ganin bayan Bello ba wani abu mai wahala bane a wurina na barshi ne ya rayu na wani lokaci dan kauda min rayuwar yarinyar dake adawa da dukiyata idan ya aika ta zuwa duniya matacci nima saina turashi zuwa can ni kuma inci gaba da rayuwata babu maƙiya sa ido da wata baraza akan komai dana mallaka a duniya domin na kauda matsala a rayuwata….

        Ajiye recording in nayi a wayata sannan nace Alhaji Bello yana da hatsarin gaske bana tunanin zaka iya kauda matsala biyu a cikin kwana biyu na mutuwarka daya ibar maka , dariya Dady yayi tare da cewa ki bani zuwa jibi zakiji labari yasha banban yayin da za’a faɗa a gari cewa wani ɗan cacan ya sake , sai kuma yayi shiru ya canja maganar da cewa  ngode zan kiraki zuwa safe idan Allah ya kaimu lafiya…! Godiya nayi masa mukayi sallama na tsinke kiranshi na kira Bello.

     Cikin maye ya ɗauka kuma daga jin yanayin wurin tabbas yana gidan caca , cikin muryar maye yace ke kika kirani ɗazu ? Ey nice na kiraka , na kiraki wayarki a rufe , Ey na bashi ansa , wai nine ma ɗan ƙaramin ƙwaron nan zai kashe ko ? Nace haka ya faɗa kuma haka yake shiryawa yace gobe²n nan iyalinka zasuyi kukan mutuwarka , amma wai me yasa yakejin zafinka haka da yawa ? Me kayi masa yake san ganin bayan ka ? Saurara kaji abinda yace maka.

      Kunno mishi record in nayi yaji Dady yana cewa , ganin bayan Bello ba wani abu bane mai wahala a wurina , na barshi ne ya rayu na wani lokaci dan kauda min rayuwar yarinyar dake adawa da dukiyata idan ya aika ta zuwa duniyar matacci nima saina turashi zuwa can ni kuma inci gaba da rayuwata babu maƙiya sa ido da duk wata baraza akan komai dana mallaka a duniya domin na kauda matsala a rayuwata.

       Cikin maye Bello yay dariya yace ni kuma a cikin daren nan zan sakashi a tarko naci gaba da farautar rayuwarshi zuwa ƙarfe 10 dai² na safiyar gobe zan kasheshi na kuma kashe Sultana saina kashe su wallahi , yana faɗin haka ya tsinke wayarshi.

       Wai me kike nufi ne ? Ni zakima gwala² ne ? Dikko ne kwance a saman gado yana jawo Jiddah jikinshi tana zuƙewa tanaja baya tasha wando jeans ta haɗa da belt , Mardiyya ta bata shawara ta daina bawa Dikko haƙƙinshi dan tana sakin jiki yana murjeta sosai shi yasa ya rainata ta kame abunta ta rufe a wando , saida ta bari wasa yayi nisa taga ya fara sakin layi ta ƙwace kanta , Dikko yace meye haka ne wai ? Cikin kwarkwasa da salo mai ɗaukar hankali tana yauƙi tace ai mantawa nayi da zakayi aure saboda ni bankai mace ba shi yasa zakayi min kishiya ? Tou kaje wurin waccen zaka aura sai ta baka maganin damuwar ka , murmushi Dikko yayi tare da ƙurawa Jiddah ido yace yanzu me kike so ne ? Saida ta sake girgizawa tace idan kana so ka kwanta dani sai ka sauka ƙasa ka bani haƙuri , ba tare da Dikko ya kalleta ba yace ai gara in mutu da in baki haƙuri danni mace bata ɗagamin hankali wannan abu fa duk taimakon kai da kaine , sauka yayi daga saman gadon yana cewa idan kinji kina muradi sai ki nema na baki danni bana hora mace da tauye mata haƙƙinta ,

       Juyowa yayi ya kalli Jiddah yace duk macen data san kanta tasan mutuncin kanta bata tauye haƙƙin mijinta saboda wani tunanin banza nata , ni da mace neni na rantse da Allah duk mijin daya aureni sai yaga bariki na tashin hankali , ko inuwarshi na gani saina ɗage mishi zani na bashi natsuwa , amma ke har kinma samu an nemeki zaki rainawa mutane hankali waye yace miki horon  hana namiji haƙƙinshi shine ke nemawa mace mutunci da martaba wurin namiji ? Idan har baki sani ba wannan abun babu abinda ya kaishi zubar da mutum mace wurin namiji , ƙimarki da darajarki sonki yana ƙara samun nakusa a zuciyata duk macen da tayi ma namiji horon hana haƙƙi taci baya a zuciyarshi.

     Misali kece kikayi tafiya a cikin tsananin rana ƙishirwa ya kamaki sosai kamar zaki mutu yayin da kikejin wannan ƙishirwar bakya tarar ruwan da zaki sha wurin kashe miki wannan ƙishirwa , kwatsam sai gashi kinga ruwa a gabanki jikinki yana kyarma kika duƙa da niyar sha sai wani ya hanaki shan wannan ruwan ya tareki , idan kina iyawa a dai² wannan lokacin me zakiyi ma wannan mutumin daya dakatar dake daga biyama kanki buƙatar ki…….?

       Jiddah tace sai inyi kokowa dashi in karɓa insha , girgiza kai Dikko yayi cewa ni bana iya gudu ina shan ruwa domin nasan baya kashe min kishirwata , haka kuma bana ci idan bana cikin natsuwa domin idan har naci abu ba’a natsuwa ba tabbas zaisa min tashin zuciya ko kuma inyi amai , ni bana danne mace da ƙarfi na kwanta da ita idan har na kwanta da mace ba’a cikin natsuwa ba bana samun natsuwar da nake so , ni a wahalce ita a wahalce me kayi kenan ? Abinda nake so ban samu ba , ni ba sakaran namiji bane da zaki tsuke da jeans da belt in kamaki da ƙarfi in cire miki na afka kanki kamar wani dabba ƙarshe inji miki ciwo kinga kaina nayi ma tunda gobe idan nazo na laɓe bayanki ina buƙata ya zanyi ? Ya ƙarasa maganar yanayi mata kallon ukku saura kwata , yaci gaba da cewa amma shawara ɗaya zan baki shine ki sake masu baki shawara su koya miki yadda ake tattalin miji wannan wacce ta koya miki haka ba ƙawa bace ba tunda har ta koya miki yadda zaki nakasa rayuwar mijinki , mai maimakon ta koya miki yadda ake tattalashi….

    Tun asubar farko Mardiyya ce tsaye a cikin kicin ɗin Jiddah tasha wanka tasha jagira ta ranbaɗa powder da kwalli sai zuba ƙamshi takeyi kamar amaryar sarki , ta haɗu a cikin wani dakeken tsadajjen leshi baƙi tasha atacch ta zubo shi har tsakiyar bayanta , tayi kyau sosai , gaba ɗaya gidan ya karaɗe da ƙamshin girkin da takeyi Jiddah nacan kwance saman gado kamar asara dan Dikko tunda ya fita masallaci bai dawo ba gidansu ya wuce saboda takaicin Jiddah , Jiddah tana kwance Mardiyya ta dafo abinda zasu yi kalaci ta barbaɗe da asiri ta kawo mata , jakar ta sauko ta lashe , bayan Jiddah ta gama tace ta ajiye na Yaya a saman tebirin cin abinci bayan shima na Dikko an barbaɗe da magunguna…

      Misalin ƙarfe 11:40am ya fito daga wanka yana fitowa wayar shi ya ɗauka ya fara kiran An mata , lokacin da wayar shi ya shigo ina tsaye a jikin madubi dan fitowa na daga wanka kenan ina shiryawa Sultan zaizo misalin 12:20pm kamar yadda Kawu ya kira ya faɗawa Kaka ta sanar dani , a daddafe nakeyin komai dan har yanzu banajin daɗi jikina yadda ya kamata ,

     Wayar yana shigowa na tsinke kiran , sake kira yayi na ƙara kashewa , kallon number yayi yana cewa haba An mata me kuma ya faru ? Bayan jiya ban dakeki ba ranar dana dokeki ma ai bakiyi fushi dani ba yi haƙuri ki ɗauki waya An matan Dikko ya ƙarasa maganar yana sake kiran wayar , wayar yana sake shigowa na ɗauka cikin ɓacin rai nace wai me ye ne……?

    Ke…. wa kike ma hayani ? Dakai nake , me yayi zafi ne to ? Haba An matana , yayi maganar cikin sanyin murya , natsuwa tazo jikina na nemi haushin Dikko na rasa kamar an tambayeni nace aure zanyi da ɗan Yaya mamana a cikin sati biyu mai zuwa , yanzu ma na fitowa wanka zaizo wurina mu gaisa , wane irin aure haka da rana tsakiya ? Ko dama kun jima kuna soyayya ne ? Cikin kuka nace a , a , ni banma taɓa ganinshi ba sunansa ma ban taɓaji ba sai jiya sunanshi Sultan , murmushin takaici Dikko yayi tare da cije leɓonshi na ƙasa yace to nima gani nan zanzo , a , a ka bari yazo ya tafi sai kazo , Dikko yace idan har nace zanyi babu wanda ya isa ya dakatar dani saina zo gani nan zuwa…….. Yana faɗin haka ya kashe wayarshi.

       Cikin ruɗewa naci gaba da shiri kar Sultana yazo ya haɗu da Dikko tunda tun jiya Babanshi ya faɗa zaizo idan kuma ya koma yace Babansa yazo ya samu nayi baƙo ai abun babu daɗi ,

     Yarinya Dikko zaki tonawa asiri ? Ni zaki faɗa ma aurenki nan da sati biyu ? Duk duniya naga mai aurenki idan ba ni ba , lallai An mata baki da hankali inma banda wawanci da rashin lissafi kai tsaye sai ace za’ayi miki aure da wani kawai kinma yadda kin hankaɗeni gefe ɗaya , naga jakin Sultan ɗin ina fama da matsalar Yazeedu zaki sake tattago wata , yana gama sa kaya kiran Inna ya shigo wayarshi…

A zuƙuwa ya ɗauka , bayan sun gaisa Inna take faɗa masa mutuniyarshi ta faɗa mishi zatayi aure ? Cikin farin cikinta da jin daɗi take bawa Dikko labari cewa ai auren zuminchie ne dake a familynsu auren haɗi akeyi , cikin yanayin farin ciki Dikko yace to kun tambayi ita yarinya tana san yaron ne ? Duk abinda ya faru jiya kamar ansa Inna ta kwashe kaf ta rattabawa Dikko , dan ita bata san Dikko da Sultana soyayya akeyi ba kuma bata san waye Dikkon ba kawai dai tanayin waya dashi dan yayi tsayuwar arfa wurin ganota ya sadata da “yar ta shi yasa ta bashi wani matsayi na musamman a rayuwarta gashi kuma yana ƙoƙarin kiranta a waya yana gaisheta lokaci².

            Inna ta ƙara da cewa aiko bata sansa su babu ruwansu haka suke haɗawa a can gidan aure ake fahimtar junan , cikin ƙarfin hali Dikko yace Allah yasa alkairi Inna ta ansa da amin tace itama zata dawo kafin bikin , Dikko ya ansa da a dawo lafiya yana faɗin haka ya tsinke wayarshi.

      Ajiye wayar yayi yana cewa An mata da gaske bari zakiyi a rabaki dani ? Haba yarinya Dikko Yazeed Sultan gaba ɗayansu nine zakaran rukuminsu gani nan zuwa a dai² lokacin daya rataya kayan da zai saka a jikin wani ƙarfe ya rungume turare yana bugawa , wani irin turare ne na “yan gayu mai masifar ƙamshi da tsada wanda ni da naji kuɗinsa naji dama kuɗin ya bani na siyawa “yan gidanmu gidan zama , shi turaren ba kaya yana a jikinki kake shafawa ba , sargafe kayan akeyi saman wani abu sai a riƙe ta inda turaren ke fita cikin hannun haggu ana zungurashi da hannun dama turaren yana fitowa , tou idan wani yana wurin akayi feshin shi kanshi turaren saiya bi kayanshi da jikinshi , idan kuma aka sakashi a jikin kaya ko an wanke ƙamshin baya fita kuma haka ƙamshin zai kama jikin wanda ya saka kayan.

          Alhaji idan kuɗin nan sun haɗu ka kawomin dan zanba yaran da zasu tayani aiki wani abu a ciki yau nake so na kashe yarinyar nan gata nan na kamota , Bello ne kwance saman kujera ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya yana magana da Dady a waya ,

     Dady yace kuɗi sun haɗu kana ina ne kaida yarinyar ? Bello yace ina sabon gidan bayan sabon gidan sarki ai ka gane gidana da nake gini ban gama ba ko ? Dady yace Eh Bello yace to ya taho da kuɗi ka ɗauki gawar Sultana , Dady yace gani nan zuwa ya tsinke wayarshi.

       Bello kallon yaranshi yayi yace yana zuwa sai ku rufeshi da duka harsai ya mutu mu kuma mu ɗauki kuɗin saimu gudu ,

      Shi kuma Dady yana gama waya da Bello ya kira “yan sanda cewa a bashi jami’ai cikin kayan gida su biyoshi dan zuwa inda wani ya kashe wata yarinya , bayan ya gama waya da polisawa yace haba Bello tunda dai burinka ganin bayana nine nan zan ga bayanka a banza a wofi dani kake zance ko ka manta waye ni ? Muke da gwamnati mu’ahhukuma hannunka dumu² a kisan Sultana “yan sanda na kama sai su kashe ka , Sultana ta mutu Bello ya mutu damuwa ya ƙare…..

        Kukan motocin Dikko na jiyo suna shigowa wani irin kuka sukeyi suuuuuu ba ƙara sukeyi ba cikin laushi suke kuka suuuu ina lissafi a zuciyata saida mota biyar ta shigo , wani irin farin ciki naji a zuciyata a bayyane kuma nace barka da zuwa mutumina , a ƙagare na saka hijabi nayi waje cikin jin daɗi.

      A harabar gida su Ashiru sun wasu kuma sun hana shiga ko fita harsai mai gidansu ya gama abinda yakeyi ya tafi ikon mallaka kenan , wani ne ya buɗe min mota na shiga inda Dikko ke zaune yana ta soɓaro baki cikin sakata , ina shiga ya rufe murfin motar , kallon Dikko nayi cikin jin daɗi tattare da shauƙin so , ɗan kauda kanshi yayi gefe yayi kyau sosai a cikin ƙananan kaya amma idonshi ya faɗa ma’ana yaɗanyi rama ,

      Murmushi nayi tare da cewa kayi kyau Dikko , ba tare daya kalleni ba yace ngode An matana ya ƙarasa maganar yana murmushi tare da ɗaga girarashin duka amma bai kalleni ba , sai yayi shiru , ni kuma na sake cewa baka da lafiya ne ? Lafiyana qalau yayi maganar yana duba wayarshi , to kayi shiru ina magana kana kallon waya ,

      Ey amma kuma kallon wayana bai hana naji abinda kike cewa , Dikko na faɗa maka , kin faɗamin zakiyi aure kin cire hotona a d pn ki , na sani ai , kayi haƙuri haka Allah ya tsara , ajiye wayar yayi tsakanin ni dashi ya juyo yana kallona yace ku mata kullum tunanin ku ɗaya ne , daga aure sai ku haihu bakwa gina rayuwar zaman auren da soyayyar junanku , bata yuwu kawai magini ya fara gino katanga daga sama baza ta zauna ba saboda a saman iska yake ta ɗora buloluwanshi , ni kuma ta ƙasa na fara nawa nayi foundation mai kyau bayan na zuba masa siminti tsaƙƙuwa da yashi na bi a hankali na ɗora buloluwa na da ko wace daƙiƙa cikin salon iya gini , na bashi ruwa katanga ya zauna dai² da dai² cif da cif faɗamin taya wannan katangar za’a iya ɗauketa a sake mata wurin zama ne ? Sai a sauke bololuwan ai , bulo dubu ne Dikko ya jera taya zasu sauko duka ba tare da wani ya roshe ba ? Kallon shi nayi cewa aiko wasu sun roshe dole a samu rayayyu , bulo dubu ne aka cire kuma ana so a sakeyin irin katangar da ake so a sake ma wurin zama shin gini zai kai kamar waccan da wurin cire bulo wasu suka rushe ?

       Sai ayi dashi da fasassun , taya zasu zauna bayan babu dashi a cikin wacce aka rushe , sai a siyo sabo a ɗora , taya za’a haɗa sabon bulo da tsoho ? Ai gini dai ake buƙata abinda tsohon ya bada sabo zai bada irinshi , bolo ina 9incis ne sai akaje siye sai suka ce babu 9 sai 6 , sai insa su bugamin wani inci 9 idan aka samun banbancin siminti fa , wancan yaji suminti sabon kuma yashi yayi yawa………..? Sai ayi filester , ai bana buƙatar filester An mata wato kina tunanin zaki iya rusa soyayya ta ki gina ta Sultan akan tawa ko ?

     Ai idan kayi tunani da babu kai zuwa kayi , tabbas babu ni zuwa nayi kuma nazo kenan bana tafiya , Sultan zaizo yayi ta gininshi a saman iska ne domin nasan zuciyarki ta gama ginuwa da soyayyar Dikko rabaki dani a halin yanzu tamkar raba bawa da mutuwa ne , kinkuwa ga abinda baya yuwuwa ne duk wanda yazo saiya koma idan har kina ganin baki mutuwa to na yadda soyayyana zai goge a zuciyarki yarinyar kirki kawai kin shigemin zuciya yayi maganar yana sauke gilashin gefenshi saboda Ashiru yana magana , 

       Mai gida wai wani daga ciki akace zai shigo yana ƙofar gida , Dikko yace a , a ya bawa Ashiru ansa yana ɗage glass in , nace kaji mulkin mallaka gidan ubanshi ne fa , ai ni kuma katsinar gaba ɗayanta a hannunmu take ko ina namu ne , banda nan dai ke yarinya shima nan ɗin nawa ne idan kuma kince a , a yanzu in nuna miki ki gani ,

      Shiru nayi shi kuma yaci gaba da rattafo kalamai masu girma zuwa zuciyata kaina kwalwata da tunani na , yaci gaba da ginawa kamar yadda yace , karatunshi mai wahar gogewa ne , kalamanshi na da daɗi , soyayyarshi tana da girma , yaci uwar awa biyu yana ɗorani a inda bana iya saukowa , saida ya tabbatar na hawo sosai yace inje zaizo anjima idan Sultan ya tafi , saida na rungumeshi na fita , shidai baya san yana taɓani kona rungumshi zai ƙyaleni saina sauka a jikinshi da kaina , ɗan gayun namiji kenan ga kyau ga tsafta ga wanka ga ƙamshi saboda yawan wankanshi idan ka taɓa jikinshi sai kaji wani irin laushi kamar ka taɓa bayan zomo , ina nan tsaye har suka fita jikina sai ƙamshin shi yakeyi gaskiya Dikko na daban ne.

        Saida motocinsu suka ɓace daga wurin ko ɓushi²n ƙurarsu babu sannan motar Sultan ta shigo……

PLS CLICK ON ADS
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


Related Articles

Leave a Reply

Back to top button