MUTUM DA DUNIYARSA 39 – 40

Gab da la’asar aka tashi, bayan Jiddah tayi gaisuwa da mutane da hotuna tasamu ta sulale batareda sunko gaisa da Aliyu ba.
★★★★★★★
Koda suka dawo gidama ba zama sukayiba, dan shirye-shirye aka faraima Jiddah Na mik’ata gidan miji.
‘Dakin Umma taje ta k’unshe a k’arshen gado saboda azabar ciwo da kanta kemata, duk hayaniyar y’an yinin biki ta addabeta.
Anayin Sallar magriba kuma Fandau ta tasota aka fara tsumata dawasu sirrikan k’amshi Na musamman.
*_08:00pm_*
Angamawa Jiddah dukkan abinda ya dace da ita, sai iyaye dasuka baibayeta ana Mata nasiha, Umma ma a wannan Karon kasa cewa komai tayi, saima hawaye dake bin kumatunta, dan haka takasa magana. Said da k’yar tace, “ALLAH ya bada sa’a, yabaku zaman lafiya, adaiyi hakuri, ayi hak’uri, ayi hakuri dakomaima za’aci karo dashi”. Daganan Umma tayi shiru bata sake maganaba.
Sosai su Zarah ma ke kuka, dan Walida ma hardasu amai, hakan saiya saka mutane dayawa kuka, dukmai d’iya mace yanacin Karo da Abu biyune a irin wannan ranar, farinciki dakuma d’acin rabuwa da y’arsa.
Haka aka fita da Jiddah gidan Uncle yahya, acanma fad’an Tasha sosai da nasiha, Uncle yahya ya kamo hannunta har wajen motar y’an d’aukar amarya, dagashi sai Jiddah suka shiga d’aya, sauran jama’a suka shiga.
Sun Isa gidan Aliyu inda aka had’a wani taron walima da d’alibansa suka shirya masa, sun samu k’yak’yk’yawar tarba daga dangin Sheikh Aliy gadanga k’usar yak’i, yayinda Uncle yahya yatsaya da Jiddah har k’ofar Maimunatu, saida tafito ta durk’usa har k’asa ta gaisheshi sannan ya dank’a Mata hannun Jiddah yana jaddada musu Kalmar hak’uri da tsoron ALLAH wajen kwatanta nagartaccen zama da ALLAH bazai k’onasu akansaba wajen cutar da juna takowace siga.
Maimunatu ta amsa da insha ALLAH Abba tana hawaye itama, dan ita duk zatonta Uncle Yahya mahaifin Jiddah ne.
Maimunatu itace taima Jiddah rakkiya har cikin d’aya daga d’akunan barcinta, saida ta zaunar da ita a bakin gado sannan tace, *_“Amincin ALLAH ya tabbata a gareki k’anwata kuma Y’ar uwata, ina miki marhaban da shigowa wannan gida, ina rok’on Ubangiji ya kad’e dukkan wata fitina dazata shiga tsakaninmu, ALLAH yabamu zaman lafiya ya dasa mana k’aunar juna mai tsafta a zukata, yabamu ikon yima mijinmu biyayya da k’yautata zaman takewa a tsakanimu har ranar da mai rabawa mutuwa zata raba”._*
Kasa magana Jiddah tayi, sai hannun Maimuna data kuma matsewa a Nata tana kuma sakin kuka, rungumeta Maimunatu tayi itama tana Nata hawayen.
Wannan lamari ya burge jama’a, wasuma sunaji inama sune da wad’annan k’yawawan zukatan masu sauk’i da d’aukar rayuwa ba komaiba.
Munafukai masu burin kunna wuta kam sai jikinsu yay sanyi k’alau, a fili kuma sukaita ta6e bakuna.
Dangin Jiddah sunyi farin ciki da sauyin alkairi da d’iyarsu ta samu, dan haka suka juya cikeda farin ciki. Dan Uncle yahya yace babu mai kwana.
Tunda kowa yafita sai Jiddah tazame a gadon ta kwanta, dan kanta wani irin ciwo yake mata, har wani jiri-niri take gani. Zuwa 12:30 gidan yay tsit alamar kowa yatafi, har lokacin Jiddah Na kwance takasa barci, saima hawaye datake zirarwa har yanzu……………✍????
*_Harda sauran Na jiya Na had’a muku????, kai gaskiya harma dana gobe, irin wannan dogon page haka????????????????_*⛹♀
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*