MUTUM DA DUNIYARSA 4

*_????HASKE WRITER’S ASSO…._
*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_[4……]_*
…………..Kamar yanda suka saba a kowanne dare bayan sallar isha’i akwai karatun manya magidanta a masallacin k’ofar gidan malam. A da shikeyi, amma dawowar Aliyu sai abun ya rabu biyu, malam Na koyar da dattijai, shikuma Aliyu matasa. Kowacce rana akwai littafin da suke karantawa, yauma kamar kullum Qur’an ne a gabansu, yayinda Sheirk Aliyu Maina ke karanto ayoyi daga suratul An-nisa cikin zak’in muryarsa da sanyin irinna masu nutsuwa. da alama ma yau suka shiga Surar, dan fako yake karantowa cikin kwarewar larabci da taka tsantsan.
Masallacin yayi tsit kowa yana saurarensa, sai da ya maimaita ayoyin daya karanta sau uku kafin ya d’ago idanunsa yana kallon d’aliban nasa da zasu iya kaiwa 40+, fuskarsa d’auke da murmushi mai sanyi.
Cikin nutsuwa suka shiga maimaitawa suma, yayinda yake musu gyara a inda yaji kuskure.
Har k’arfe 9 suna karatu.
Sheirk Aliyu ya kalli agogon fatar dake d’aure a tsintsiyar hannunsa, ganin har tara da kusan kwata yay d’an gyaran murya alamar su dakata. duk kallonsa sukayi, yad’an murmusa yana fad’in “Masha ALLAH, Inaga yakamata mu dakata haka, domin kowa yaje ya k’arasa Uzirinsa”.
Duk sun amsa masa da to.
Addu’a yay musu kafin kowa yatashi ya fito bayan sunbashi hannu duk sunyi musabaha da bankwan