MUTUM DA DUNIYARSA 43 – 44

Abba tun yana zama Abuja da shauk’i harta fita aransa, gashi sai cinye y’an kud’insa yake wajen biyan hotel da abinci, kullum ya zagaya gidan Alhaji Sammani sai mai gadi yace ai bai dawoba.
Yauma dai yana tsaye a bakin gate sai hucin 6acin rai yake saboda abinda mai gadin yamasa Na wulak’anci da jifansa da Kalmar maula, da girmansa da mutuncinsa a kirasa d’an maula?, horn d’in mota ya sakashi saurin d’agowa, dad’i ya kamasa domin ganin Alhaji Sammani, ajiyar zuciya ya sauke tareda ambaton Alhamdullahi.
Har driver zai shige Alhaji Sammani ya dakatar dashi saboda ganin Abba dake jingine a jikin motarsa, ya sauke gilas lokacin da suka tsaya dai-dai saitin Abban.
“Wanake gani haka kamar Alhaji Zakari yaro?”.
Abba yay dariya mai cike da tsantsar farin ciki yana matsawa jikin motar Alhaji Sammani, “Wlhy nine kuwa abokina, inata zaryar ganinka amma hakan yaci tura”.
“Ashsha Alhaji zakari, wlhy banda wannan labarin, gashi kuma kullum ina gari, yanzu dai shigo muje ciki”.
Jikin Abba Na tsuma ya bud’e motar ya shiga kusada Alhaji Sammani, sai wani dad’i yakeji dajinsa a sama, jiyake yagama da matsalar Alhaji garba ma kawai.
????????????Abba????
Koda Alhaji garba yadawo gida baiko dubi sashen Hajia deluwa ba balle tasan da dawowarsa, itako tanacan tana cika da bunk’asa har yanzu, yayinda Bala da Ashir keta kuma tunzurata da tsinema amaryar Uban nasu, har suna fad’in tabasu dama su lakad’a mata duka yanda gobe zata tattara da k’afarta tabar musu gidansu.
Kumbura Hajia deluwa ta sakeyi, dan ita tafison Alhaji yadawo sufara cashewa kafin tabi takan waccan banzar, dan bak’aramin iskanci k’awayen Amaryar suka 6ararba yau a gidan, gud’a da habaici babu irin Wanda deluwa batajiba, gashi sun fita yawa, tanajin tsoron ta fita su lakad’a Mata duka. Hakanne yasata mak’alewa akan cewa da Alhaji zatayi badasuba.
Shikam baimasan tanayiba, yanacan yasamu tarba ta musamman ga amarya, tunima ya manta dawata banza hajia deluwa, Amaryarsa kawai yakeji da gani, yayinda ta gama kasheshi da dabaibayeshi da soyayya itakuma.
Har kusan 11 babu Alhaji babu labarinsa, hakanne yasaka su Ashir fitowa zasu sashensu, mamakine ya kamasu ganin motar Abbansu, Bala yakasa hak’uri yaje yana tambayar mai gadi ko Alhaji ya shigo. Mai gadi yace, “Ah tun kusan takwas da rabi ai Alhaji ya shigo gidan ai”.
Idanu bala ya zaro, sannan cikin sassarfa yanufi sashen Hajia deluwa ya shaida mata.
Wata uwar ashar ta lailayo ta dire, kafin ta fisgi waya tahau kiran Alhaji, amma harta k’araci ringing ta katse bai d’agaba, saida tayi Kira kusan goma sannan aka d’aga.
Cikin masifa tace, ”Sannu munafiki, to ALLAH ya tona asirinka kadaw……”
A wata irin muryar kwarkwasa Hajia bariki ta katseta, “O madam kekuma haka naki salon yake babu tarbiyya da girmama miji? Please kid’an jinkirta yana sunnah ne, zuwa safiya zaki iya ganinsa bye”.
Bata tsaya jin zagin da Hajia deluwa ta antayo mataba ta yanke wayar tana dariya.
Zubewa kawai a k’asa hajia dealuwa tayi ta daddage ta kwad’a ihu????????????………….????
*_Gobe idan ALLAH ya kaimu bazanyi typing ba sisters, amma inada page daban k’arasaba Zan k’arasashi anjima kad’an insha ALLAH, Na turo muku anjiman kokuwa abari sai gobe?_*
_Wanda naga ra’ayinsu yafi yawa to shi za’abi????????????_
_Barkanmu da Juma’a_????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????