NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 45 – 46

 *_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
             _(ya dace ya gyara kansa)_
                 *_Bilyn Abdull ce????????_*
                   *_[45➖46]_* 
…………..Hira suka cigaba dayi a sashen Maimunatu har kusan sha biyun rana,
itadai Jiddah bama saka baki takeba, sai idan sun sako sunantane take d’an murmushi, Sheikh Aliy ne yafara tashi ya fita saboda kiran da Malam Mustafa yaymasa akan gashi da bak’i a k’ofar gida.
    Bayan fitarsane Maimunatu ma ta mik’e tana fad’in “Kinga Jiddah bara nashiga kicin rana tayi, ga hotuna ki kalla karki zauna shiru”.
     “A’a aunty bar hotunan, daga baya saina kalla, muje kicin d’in”.
      Cikin waro idanu waje Maimuna tace, “Wai inani ina saka amarya aiki, wlhy Na yafe miki zauna ki huta abinki”.
    Duk yanda Maimuna taso Jiddah ta zauna k’i tayi, tabita kicin d’in suka fara aiki tare, sunayi Maimuna nad’an janta da hira, mafi yawan hirar itama duk akan abinda yashafi gasar da Jiddan taje Saudia ne, hakanne yasaka Jiddah d’an sakin jikinta da ita tana bata labari.
      Har suka gama girkin da kimtsa kicin d’in Aliyu bai shigoba, time d’inma anata shirin shiga sallar zuhur, dan haka Jiddah tanufi sashenta cikeda jin Maimuna ta kwanta mata a rai, itadai koda ake cewa kishiya bata maka Abu dan ALLAH saidan kissa ta aminta da Maimuna da zuciya d’aya, kuma insha ALLAH zata bata had’inkai su zauna lafiya, dan tunda suke da Ummansu ba’a ta6a jinta tana hayaniya da kishiyaba, to ita mizaisa tayi da tata.
     Da wannan tunanin takoma sashenta, tsaf ta iske komai yanda ta barsa, tashiga bayi ta d’aura alwala tafito domin gabatar da salla. Bayan ta idar kayan jikinta ta cire ta sauya da doguwar riga ta material rowan ganye mai haske, sunmata k’yau dan d’inkin yamata d’as, tad’an gyara fuskarta sannan ta saka turare. Batayi yunk’urin komawa sashen Maimuna ba, saima laluben wayarta data shigayi dan san kiran su Umma, ta gama zazzage handbag d’inta amma babu wayar, shiru tad’anyi tana tunani, saikuma zuwa can ta dafe kanta dan ta tuna wayar na a hannun walida, tasan itama mantawa tayi bata bataba, saikuma duk taji tadamu, ga kewarsu dake cin ranta, kwanciya tayi a gefen gadon, zuciyarta Na karyewa da tunanin rayuwa mai sauyawa a kowacce safiya.

          Saida aka idar da salla Aliyu ya shigo gidan, kai tsaye sashen Maimuna ya nufa, babu kowa a falo dan haka yanufi d’akin barcinta.
     Zaune ya isketa tana karatun Qur’ani, ya jawo stool d’in madubi ya zauna yana sauraren zazzak’ar muryarta. Dukda taga shigowarsa bata tsayaba saida takai inda ya kamata ta tsaya sannan ta rufe tana ajiyewa da kallonsa.
      “Sannu da shigowa”.
 “Yauwa Maimoon, bak’uwar takifa? Tad’an sake dake ko?”.
    Murmushi Maimuna tayi tana mik’ewa tsaye da cire hijjabinta, “Ai tanada sauk’in kai Yaya, tarema mukayi girki, duk macen da za’ama kishiya takan Shiga matsananciyar damuwa saboda batasan wa za’a kawo mataba, dan y’ammatan yanzu burinsu dasun shigo su Kora ta ciki waje, watama tun a y’an kawota zasusaka jikin Uwargida kuma sanyi, saboda gugar zana da habaici, amma Alhamdllh ni sai Ubangiji yaymin k’yauta da samun baiwarsa kamila mai addini da tarbiyya, wlhy da ace amarya zata kasance irin Jiddah da babu wata Uwargida da zata Gaza kwantar da hankalinta a zauna lafiya, dukda har yanzu banida tabbaci akan Yaya zata kaya nan gaba amma ina kyautata Mata zato da fatan tabbatuwar nagartarta”.
       Murmushi Aliyu yayi yana kamo hannun Maimuna cikin nasa, ya matso da ita gabansa idonsa akan fuskarta, “Maimuna bake kad’ai kika dace da samun Jiddah matsayin abokiyar zamaba, har itama tadace da samunki, sai nikuma Na dace da samunku baki d’aya, kinyi abinda Mata da yawa suka kasa a wannan zamanin, dan inhar akace miji zai k’ara aure to shikenan zaman lafiya ya k’auracema gidansa, tsakaninsa da matarsa sai Y’ar harara da ya6a magana, amma ke sai kika Nuna kin cika Y’ar halak mai aiki da ilimi da tarbiyya bisa addinin islama, duk wandda yazama mai k’yak’yk’yawar zuciya ALLAH bazai ta6ar dashiba Maimoon, inhar kayi k’yak’yk’yawa saikaga k’yak’yk’yawa, da sauran Mata zasuyi koyi dake da dayawa sunzama taurari a zukatan mazansu kamar yanda kika zama a tawa zuciyar, ALLAH yay miki albarka kinji, nasan kinajin kishin amma kike dannewa saboda k’yak’yk’yawar zuciyarki”. ‘ya k’are maganar da rungumeta a jikinsa’.
        Itama rungumeshin tayi tanajin k’arin k’aunarsa.
     Sun jima a haka sannan ya saketa,
      “Hayaty bara na sauya kayanan nad’an kwanta Na huta”.
      “Kwanciya kuma Nurry, abincinfa?”.
      Cikinsa yad’an shafa yana yamutsa fuska, “Mikuka dafa mana a gidan?”.
        Cikin tsokana tace, “Taliya da mai da yaji”.
       “Taliya kuma?”. ’Yay maganar cikin had’e fuska’.
     Maimuna ta sanya dariya tana shafa k’irjinsa, “maida wuk’ar Alhaji wasafa nakeyi, kus-kus ne da miyar kayan lambu”.
      ‘Dan hararta yayi, “Zan kamakine ai, dama kinsan d’azun kinada laifi”.
         “Ni munari, baka mantuwa Yaya?”.
      “Aiba tsufa nayiba balle nafara mantuwar, zoki bani abinci naci naje  nad’an huta”.
   
          Koda tazo bashi abincin zata Kira Jiddah cayay “Kinga barta, kinga d’azun batawani ci abun kirkiba saboda bata saba damuba, mubata lokaci koda na kwana biyu haka, bani naci idan Zan wuce saina tafi Mata dashi”.
       “Okay Yaya hakanma yayi gaskiya, dama inata tunani tun d’azun akan hakan wlhy”.
       Tare ta zuba musu sukaci, bayan sun kammala sukai hamdala ga Ubangiji.
         Kulolin tasaka a karamin basket duka tace ya tafima Jiddahn dasu, “Yazakice a kai duka, yamata yawa ai, k’ila kuma wani yazo”.. 
       “A’a kakai Mata Yaya, dan yanzu hakama saikaga ita tayi bak’in ni banyiba ai”.
     Baice komaiba ya amsa ya fita.

            Kwance ya isketa tana barci, da alama daga tunaninta barcin ya saceta, abincin ya ajiye gefe ya gyara Mata kwanciya dan tana a bakin gadone sosai.
      Shima fita yay zuwa sashensa danya d’an kwanta kafin la’asar.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

          A katafaren falon bak’i Na gidan sanata Sammani aka sauke Abba, dan danan aka cika gabansa da kayan motsa baki.
     Bayan kamar awanni biyu da shigar Alhaji Sammani saigashi ya shigo falon da Abba yake, zama yay suka gaisa cikin fara’a da tambayar iyalai. Daganan suka d’ora da hira.
      Sai da Abba yabari hirar tayi nisa sosai sannan ya sakkoma Alhaji Sammani buk’atarsa ta rancen kud’i miliyan hamsin.
       Wani kallon K’asan ido Alhaji Sammani yakema Abba, tuni kuwa fara’ar fuskarsa ta gushe, ya gyara zamansa yana fad’in,
      “Kaiko Alhaji Zakari duk mizakayi da wad’annan kud’in zunzurutu haka?”.
      Cikin nisawa Abba yace, “Wlhy Alhaji Sammani wani business yazomin babu shiri, gashi kuma zamuyi had’akane da wani, nikuma kud’in hannuna narigada na zuba kaya dasu”.
      Alhaji Sammani yay murmushin takaici yana kallon Abba sosai. “Lallai Alhaji zakari Kai lafiya lauma kake, yo dole nace nafiya lau kake mana, Kai kud’in Business kake nema yanzu, bayan kuma kanayin wani, niko yanzu maganar nan danake maka tunanin yaya zan shirya kamfen a shekara mai zuwa nake, maganar gaskiya bara namaka gwari-gwari, banida wad’annan ruwan kud’in da kake buk’ata, idan kace nabaka rance ina kaga kud’in biyanama? So karka kawo abinda zai ruguza mana zuminci please ”.
     Tunda Alhaji Sammani ya fara magana Abba ke kallonsa baki hangame kawai, harshine zai buk’aci abu wajen Alhaji Sammani ya hanashi? Yamanta wahalar Campaign da sukai masa? Ya manta kud’ad’ensu da suka zuba danya samu mulki?….
     Afili saiya kuma kwantar da murya ga Alhaji Sammani, “Haba abokina, nasandai wad’annan kud’in bazasu gagarekaba, yazan kawo maka matsalata ka kalleta a k’amar matsala, dan ALLAH ka duba mana”.
    Mik’ewa Sanata Sammani yayi tsaye yana ta6e baki, ya Ciro dubu Hamsin a aljihunsa yana ajiyewa gaban Abba, “Alhaji Zakari ga wannan kasha mai, ka gaida iyalan naka da k’yau”.
    Sakatata Abba yabi Alhaji Sammani da kallo harya bar falon, ya maida kallonsa ga kud’in daya ajiye masa zuciyarsa Na tafasa, waishi wannan mutumin zaima haka saboda sunriga sun tura motar ta tashi? A lallai lamarin y’an siyasa abin tsorone, wato lokacin da suke buk’atar mulkime muke mutane a wajensu? Cikin cizon yatsa Abba yamik’e yana harar kud’in.
    Harya Kai k’ofar fita kuma yadawo yana kwafa ya kwashe kud’in ya zuba a aljihu yana fad’in “Garama Na d’auka narage asarar danayi”. (????????ho Abbanmu).
        Nadai tak’aice muku bayani aranar Abba yabaro Abuja ya kamo hanyar kano, sai surutai yake a mota tamkar sabon kamu.????
   

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button