MUTUM DA DUNIYARSA 45 – 46

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sai gabannin la’asar Aliyu ya tashi, wanka yayi danyaji k’arfin jikinsa, barcin dayayi yasaka jikinsa nauyi sosai.
Jiddah kam barcinta bai wuce Na awa d’aya ba ta farka, Tasha mamakin yanda akai takoma tsakkiyar gadon, tana sakkowa taci Karo da kayan abincin da Aliyu ya ajiye, tashitai taje ta duba ganin abincine saita rufe tafara shiga bayi, bayan wasu mintuna tafito, zama tayi taci abincin, dan dama yunwa takeji.
Bayan ta kammala d’akkowa tai tadawo falo, tana zama Ana maido wuta, taji dad’i sosai, saidai kuma matsalar ma ba’a had’a Mata kayan kallonta ba, koma fiddasu a Kwali su Yaruwaiya basuyiba, komawa tayi cikin kujera ta kwanta tafad’a duniyar tunani. Har aka Kira sallar la’asar tana falon, daga bisani takoma d’aki domin yin sallah.
Bayan an idarne Aliyu ya shigo, sanye yake da yadi mara nauyi kalar shanshanbale mai duhu, kansa da hula kamar ko yaushe.
Kan Jiddah a k’asa tace, “Sannu da dawowa”.
“Yauwa amarya, ya bak’unta?”.
Murmushi kawai Jiddah tayi amma batace komaiba.
Shima saiya zauna a bakin gadon yana fad’in, “Naga kin kirani d’azu a waya, nasakata a silent na kwanta barci, sai dana tashi nagani, mike faruwa?”.
Kallonsa tayi da mamaki, “Aini wayarma bata wajena, na mantata a gida”.
“Tofa, to kosu Zarah ne dai?”. ‘yay maganar yana Ciro wayar a aljihun gaban rigarsa’.
Jiddah tace, “K’ila sune to”.
Baice komaiba yashiga k’ok’arin kiran Number tata, amma kuma a kashe yanzu, kallonta yayi yace, “wayarkuma a kashe ai”.
“k’ila babu cajine, ni nazatama zasuzo yau amma babu Wanda yazo saikace basa sonama”. ‘Tak’are maganar Idonta na cika da k’walla’.
Fuskarsa d’auke da murmushi yace, “Malama waya fad’a miki dama ana zuwa gidan amarya irin wannan ranar?”.
Matso hawayen tayi sannan ta saka gefen hijjab ta share.
Shi dariyama tabashi, yacire hularsa yana ajiyewa gefen gadon, “Kincika shagwa6a da sonyin kuka, kuka yana miki matuk’ar sauk’i hajiyata, toyi hak’uri insha ALLAH nasan zasuzo kinji”.
Kanta ta jinjina masa, shikuma yay murmushi yana mik’ewa, “Bara naje gadon k’aya na gaida malam dasu hajia, inaga sai dare zan dawo insha ALLAH”.
“Adawo lafiya, ALLAH ya tsare hanya”.
“Amin ya rabbi Khairunnisaa”.
Harzai fita yadawo ya manna Mata Sumba a kumatu sannan ya fice.
Ajiyar zuciya Jiddah ta sauke, harma tad’an fara sabawa da halayyarsa itakam.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Ihuntane yasaka Bala da Ashir shigowa aguje suna fad’in “Mami lafiya? Mi akayi mikine?”.
“Ashir bazaku ganeba, zuciyata neman tarwatsewa takeyi, yanzunan har akwai ranarda dama kishiya zata fad’amin son ranta akan mijina? Ni ni Deluwa? Wlhy sai matarnan tabar gidannan koda zanyi yawo tsirarane kuwa, har abada dagani sai y’ay’ana zan rayu a gidannan”.
Cikin fusata Ashir yace, “Mami ki kwantar da hankalinki, wlhy idan kika bamu dama bazata cika satiba a gidannan zata Kama gabanta, narasa mike damun kan Dady, yarasa wadda zai kwaso mana sai wannan tsohuwar karuwar, ALLAH garama yarinyar nan Jiddah, dama ita kika hak’ura muka zauna da Dady bai kwaso mana wannan motar hayarba ai”.
Hararsa hajia deluwa tayi, “Kai dan Ubanka waya fad’a maka kishiya duk k’ank’antarta tanada sauk’i, dalla kuficemin anan kafin najuye muku takaicin dake kaina yanzunnan”.
Kallon juna sukayi shi da bala suna ta6e baki, suka fice suka barta tana cigaba da borinta da zagi kwando-kwando ga Alhaji garba da amaryarsa.????????
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sai 10:30pm Aliyu ya dawo gida, tunda magriba ya dawo anguwar amma bai shigoba yana massalaci, bayan sungama karatun dare yakuma barin anguwar, sai dai baiwani dad’eba yadawo, Kai tsaye gida ya shigo, tsitt kakeji tamkar babu mutane, leda d’aya ya d’auka yanufi sashen Maimuna, kwance ya isketa harma tayi barci, ganin magani a durowar gefen gado yabashi tabbacin batada lafiya, zama yay kusa da ita yajanye bargon datake ciki yana ta6a wuyanta zuwa goshi, jikinta ringim da zazza6i, tausayintane ya kamashi, bai tadata ba ya tofeta da addu’a ya maida mata bargon sannan yafito.
Kicin d’inta ya shiga yasaka Mata abin cikin ledar a firij sannan yadawo falo, tea d’insa da kayan fruits data gyara ya d’auka yafita yaja Mata k’ofar.
Saida Yakoma mota ya d’auki d’ayar ledar sannan yanufi sashen Jiddah itama.
Bai isketa a faloba, dan haka yawuce bedroom. Zaune take tana duba littafin Umdatul Ahkam, kanta ta d’ago tana amsa masa sallamar, ganinsa da kaya saita ajiye littafin tamik’e ta amshesa tana masa sannu.
“Yauwa Juddatulkhair, ya zaman shiru? Amin afuwa kinsan nid’in sai a hankaline”.
Fusakarta d’auke da murmushi amma batace komaiba.
Zama yay kan k’aramin kafet d’in gaban gadon ysna kallonta, itakam takasa kallon nashi, tana k’ok’arin aje kayan gefe tace, “Aunty fa batada lafiya, amma tasha magani tun d’azu ta kwanta, zan kiraka amma ta hana”.
“Eh naje wajenta kafin nashigo nan, Mata kuna k’ok’ari, tunda tasamu cikinan haka taketa fama, nikaina bansan adadin ledar ruwan data shaba ma”.
Cikin tausayawa Jiddah tace, ”ALLAH Sarki, ALLAH ya k’ara Mata lafiya, wlhy Na tausaya mata, dan d’azun daga cin abincin sai amai”.
Shima duk fuskarsa ta Nuna alamun damuwa yana tausayama Maimunatu matuk’a.
★★★★
Bayan sunsha fruits d’inda saida yasha fama da ita sannan yasa ta had’a masa Shayin, koda yace taci naman daya kawo catai ta k’oshi, bai takurataba ya kammala shan tea d’insa yamik’e yana fad’in tayi alwala kafin ya dawo”.
Bai jira amsartaba ya fice, kwashe kayan tayi cike da tsarguwa tafito, tabud’e abinda tasan zai iya lalacewa dan batada firij.
Umarninsa tabi, bayan tayi shirin barci ta d’auro alwala, duk yanda su Yaruwaiya suka koyar da ita wajen saka k’amshi da tsaftace bakinta saida tayi, kafin tasaka hijjab ta zauna zaman jiransa.
Bai wani jimaba can sosai ya dawo cikin jallabiya ruwan k’asa.
Kallonta yay damata alamar ta tashi, itadai duk jikinta yayi sanyi, addu’a kawai takeyi a k’asan ranta ALLAH yasa ba zargin datake baneba.
Sheikh Aliy ya jasu salla raka biyu kafin suyi zaman addu’ar, yaja addu’a mai tsayo tafatan zaman lafiya a tsakaninsu da sauran al’umar musulmi kafin su shafa ya juyo gareta.
Cikin tsareta da idanu ya jeho Mata tambaya…………..✍????
*_Zan d’anyi jan hankalo anan please, wasu suna ganin maganar da Maimunatu tafad’a akan mutumin da ya turo sak’o tamkar da Aliyu take, a’a badashi takeba, sak’one aka turo masa kamar yanda ta fad’a, mun ta6o wannan ga6arne kuma saboda girmanta da yawautarta acikin al’umma, sannan masu gani shi Aliyu kamar baya iya Mata komai ba haka baneba, itadai tace yakan had’ama kwanaki hud’u bai nemetaba, sannan baya dogon zango tare da ita, (abinda nakeso mu fahinma anan shine yanada k’yau muringa kwatanta rayuwarmu ta zahiri a cikin novels, babu wani namiji da azahiri zaikai tsawon awoyi hud’u ko sama da haka tare dake, inkuwa hakane to lallai munshiga uku????????????, idan kuwa har za’a samu irin wannan to basuda yawa gaskiya, nata6ajin wani likita Na fad’in yawan jima’i kullum-kullum yana ragema ma’aurata sha’awa da jindad’i harma suji abun yana fita Kansu basa wani shauk’in yinsa, sai dai suyi domin sabo kawai, sannan yana ragema mace d’and’ano awajen miji, abinda kuma zamu kalla bakowane namiji baneba a zahirima zai kasance dake a kullum, dan wani yaje aiki ya gaji, wani kuma damuwa tamasa yawa da sauransu, kuma ke kankima wlhy saikinji lamarin da takura dukda dai halittarmu kala-kala ce, akwai masu yawan buk’ata a mazan da matan, a dalilin karatun novels Mata da yawa sunama mazajensu kallon ragwaye, a buk akan saka namiji yayi awa uku tare da matarsa, maybe ma bai ishesaba, sannan da safe zai k’ara, idan yadawo aikima haka, tayaya ke a zahiri da ba’aima haka bazakiga gazawar naki mijinba?, wannan yasa lokuta da dama ake kalubalantarmu mu marubuta, dan mungaza fahimtar tasirin da alkalumanmu kedashi ga al’umma, badan nishad’i kawai ake rubutu ba, yakamata y’an uwana marubuta muringa saka hakan a ranmu, dan yanda zaki rubuta Abu Mara k’yau ALLAH ya tambayeki haka idan kika rubuta k’yak’yk’yawa zai baki lada, balle idan wani ya amfanu dashi Yasamu amfani kuma, idan awannan littafi kin saka yawan bukatar ma’aurata to Ya kamata acan kisaka k’asa-k’asa, awanima kisaka rauni sosai domin wasu su sami mafita daga matsalarsu Na gidajen aure, hakanne yasakani a farkon buk d’inann Na nuna Aliyu yanama da Matsala gaba d’aya, wadda kuma a sanadinta harya rasa matarsa da yake matuk’ar so da k’auna. Ina fatan kun fahimceni, nayi wannan maganarne domin murunga tafiya akan abinda ya dace, dan idan mun kauce kuke Fara k’alubalantar mu, alhalin kuke tunzura marubuta da yawa rubuta abinda zai burgeku a buks nasu, kuma koda ya kasance Mara tsari ga al’umma)_*.
_ALLAH yasa mudace_.????????????