NOVELSUncategorized
MUTUM DA DUNIYARSA 5

*_????HASKE WRITER’S ASSO…._*
*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_[5……]_*
…………..Gaba d’aya saisu Jiddah suka kasance cikin rashin sakewa, dan koda suka idar da salla basu fito tsakar gidaba, duk da zafin da ake zubawa yau. Itama Umma bata nemesu ba, dan tana idar da salla ta fito ta had’a abincin Abba takai falo, baiwar ALLAH harda kunna turaren wuta da maganin sauro. Tana kammalawa Ana kiran isha’i, dan haka bata nemesuba tawuce d’aki dan yin salla.
Ana idar da sallar isha’i Abba ya shigo gidan, babu batun sallama dama a tsarinsa sai gyaran murya, ada dasu Jiddah Na k’anana dasunji gyaran muryarsa suke guduwa su 6uya. (Humm ALLAH ya k’yauta????).
Babu kowa a tsakar gidan, dan haka ya wuce d’akin Umma, kulolin dake a tsakkiyar falon yake bi da kallo, kafin ya maida kallonsa ga Umma dake can wani d’an loko inda ta maida wajen ibadarta a tsakanin kujeru. Addu’a takeyi, dan haka baice komaiba ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu.
Su Jiddaha sunajin Abbansu na gyaran murya amma babu wanda yay koda gigin lek’owa waje.
Saima tagumi duk da suka rabga, kowa da irin kalar tunanin da yakeyi.
Jiddah ce tafara d’ago Kai ta kallesu, tausayin y’an uwan nata Yakuma kamata, cikin kauda tata damuwar ta zunguri walida dake kusa da ita. Kallonta Walidan tayi, Jiddah ta sakar Mata murmushi “Haba Autar Umma, irin wannan tagumi