NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 51 – 52

 *_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
             _(ya dace ya gyara kansa)_
                *_Bilyn Abdull ce????????_*
                   *_[51➖52]_*   
…………Duk yanda yaso daurewa karta fahimci shine yakasa, maimakon ya
zuge mata zip ɗin tamkar yanda ta buƙata saiya ɓige da tura hannayensa cikin rigar ya zagayo dasu saman cikinta.
     Baƙaramar firgita Jiddah tayiba, tanemi juyowa a razane yay azamar ɗora kansa saman kafaɗarta yana faɗin, “Afuwa hajjaju nine ba Zarah ba”.
     Kasa motsin kirki Jiddah tayi, sai jikintane ke mazarin tsumar tsoro, muryarta na rawa tace, “Sannu da dawowa”.
     “Yauwa amarsun Aliy, yaya jikin dai?”.
     Shiru tai ta kasa amsawa, gaba ɗaya tagama takura, gefen zuciyarta kam addu’a take ALLAH yasa kar cikinsu Walida wani ya shigo, ita abindama bata fayimtaba inasu Aunty Nafisa suke? Harya shigo nan……. Firgita tayi tana Saurin dafe hannunsa dake neman canja salon yawo a rigarta, cikin sarƙewar murya da matuƙar in ina tace,
     “Su..su..s..u aunty Sau..dah sun.. zo fa”.
     Dariyar dake nemen kufce masa ya danne da ƙyar, dama yayi mata hakane dan tayi magana. Fuskarsa ɗauke da shinfiɗaɗɗen murmushi ya cire hannunsa yana juyo da ita. Kasa kallonsa tayi, hannunsa yasaka ya ɗago haɓarta yana faɗin, “Tun randa na fara ganin wannan fuskar na fahimci matsoraciya ce ke kam”.
      Murmushin da bata shirya yibane ya kufce mata, tasaka hannayenta ta rufe fuskarta. Yanzun kam saida ya dara, ya jawota jikinsa yasaka mata zip ɗin.
      Komawa yay ya zauna a bakin gadon yana kallonta tana ta wani sinne kai, aransa kam dariyar yanda taketa kare ƙirjinta yakeyi da faɗin mata kenan, hakafa Maimunatu taita masa, amma kwanaki naja tana kuma sakin jikinta dashi, yasan itama Jiddahn zata koma dai-dai ne, duk macen kirki dolene asameta da wannan kunyar, danshi baiga birgewaba ga ƴammatan yanzun da idanunsu ke a soye, watama ɗan kukannan idan za’a kaita gidan miji batayi, ƙagarama take atafi, suna ɗaukar hakan wayewane basusan zubar da kimarsu suke ta ɗiya maceba, koshi mijin sai dai yaƙi faɗa maki amma saiyaji baki birgeshiba kwata-kwata, duk son wayayyar mace da wasu mazan keyi sunason koyaya taɗan ringa kunyarnan a gabansu, domin kunya ita kanta jan ajine ga ɗiya mata, kuma alamune na kin kwankwaɗi tarbiyyane a gidanku, danshi abinda yake kallon mace mara kunya *BALLAGAZACE* kawai mara isashshiyar tarbiyya. Numfashi yaɗan sauke yana kallon jiddah dake tattare kayan data cire, amma koda wasa taƙi duban sashen da yake. “Juddatulkhair muje na gaida su auntyn namu naje naɗan kwanta na huta kafin lokacin sallah ko”.
      Kanta ta jinjina masa tana ajiye kayan hannunta, cikin sanyinta tace, “To”.
     Harta kama hanyar fita yace, “Zonan na tambayekima”.
    Dawowa tayi da baya, zata durƙusa ƙasa ya kamo hannunta yana faɗin, “Zauna anan”. Ya nuna mata bakin gado kusa dashi.
    Bata musaba ta zauna, kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
    “Kinsan mizan tambayeki?”.
     “A’a”.
Murmushi yayi mai sauti yana kuma maida hankalinsa gareta, “Wai kinsan sunanama kuwa?”.
      A mugun bazata tambayar tasa tazo mata, dan haka ta ɗago kai tana kallonsa cikin waro idanu.
     Babu shiri shima dariya ta kufce masa, miƙewa yay tsaye yana cewa, “Dama sonake naga idonki kuma nagani, tashi muje ki rakani”.
     Jitai tamkar zata nutse dan kunya, wlhy rayuwar bawan ALLAHn nan tana matuƙar burgeta, tarigada ta taso Abbansu banda jaraba babu abinda ya iyayima Umma, idan sunga fira tsakanin mata da miji cikin aminci to sai dai idan gidan Uncle yahya sukaje, amma a gidansu dai a’a, itafa zatama iya lissafa dariyar Abba data gani a rayuwarta, wannan yasaka duk abinda Aliyu yay mata sai take ganinshi tamkar wani mijin novels ko film????.
       
        Fita tafarayi falon ta barsa a ɗakin, su aunty Hannatu na zaune sunacin abinci, yayinda su Balu ke ɗaki suna salla sukuma.
     Yanda taketa wani nuƙu-nuƙu da sissinkuyar dakai ne yasakasu zuba mata idanu.
      “Lafiya kuwa Jiddodo?” ‘Aunty Zulai tai maganar’.
       Kuma ƙasa tayi da kanta kafin tace, “Aunty wai dama shine zaku gaisa”.
    Harsun fara dariya saikuma kowacce ta rufe bakinta da hannu saboda harar da Aunty Saudah ta zuba musu dukda itama danne tata dariyar take, yanda Jiddah tayi maganarne dole tabaka dariya.
       “Wlhy Jiddah yanda kikasan ƴar da haka kike, bakisan sunansa baneba?”.
       Murmushi tayi kanta a ƙasa,  “toni aunty bansan yanda zance muku ku ganeba”.
      Cikin tsokana Aunty Nafisa tace, “Sai kice auntys Hubbiy zaizo ku gaisa”.
      Ido jiddah ta zaro saikuma ta narke fuska, “kai Aunty Nafi wlhy nidai babu ruwana”.
     Yanzukam kasa daurewa sukayi, saida sukaɗan dara kaɗan.
      Yaruwaiya tace, “To ɗan nawa yana ina?”.
     Da hannu jiddah ta nuna ɗakin data fito.
    “K jiddah wai kina nufin yana ciki?”.
    Kai ta ɗagama aunty hannatu mai maganar.
      Hannu sukasa suna dafe bakuna, Aunty Sauda tace, “Wai kina nufin dama tun ɗazun yana nan?”.
     Cikin son tsokanarsu Jiddah tace, “eh mana”.
     Babu wanda bai rikiceba dukansu, Maman Sadiq ta zubama Jiddah daƙƙuwa tana faɗin, “Jiddah kinci gidanku, shine dan iya shege kika barmu muketa zuba da sakin magana”.
      Dariya jiddah keyi, saikuma tarufe bakinta da hannu tace, “Wasafa nakeyi, wlhy yanzu yashigo kuna ɗaki kuna sallah, su Zarah kuma suna kicin”.
     Babu wanda bai sauke ajiyar zuciyaba a cikinsu, yayinda aunty Nafisa ke faɗin, “ALLAH kafin nabar gidanan saikinci gidanku jiddah”.
      Nanma dariyar Jiddah tayi tanama aunty Nafisa gwalo.

       Shiekh Aliyu dake ɗaki duk yana jiyosu, murmushi yay yana mamakin dama tana magana haka, da sai yaga kamar tafishi shiru-shiru, amma yaukam dayaji bakinta saiya kuma tabbatar da kunyace kawai da rashin sabo dasu.
      Ɗakin ta shigo da sallama, ya ɗago idanu yana kallonta da amsa mata.
        “Na faɗa musu zakaje ku gaisa”.
     ”Wakikace musu zaizo?”.
      “Kai mana”.
 “Niwa?”.
       Shiru tayi dan an ƙureta kuma.
       “Shiyyasa nace bakisan sunanaba ai madam, muje kirakani to”.
       Kafinma yakai ƙarshen maganar harta kai ƙofa, dan batason yazo yacim mata.

        Tunkan su fito dama sun kimtsa, Aliyu ya zauna saman kujerar farko idan kafito daga bedroom ɗinsu, fuskarsa shimfiɗe da murmushi yana musu sannu da zuwa.
       Duk suka amsa masa cikeda girmamawa, yau gasu ga babban malamin da sukeji a redio da tv a gabansu, matsayin mijin ƴar uwarsu.
       Sun gaisa cikin mutunta juna, sunata kuma mamakin sauƙin kai irinna Aliyu, har yana tsokanar yaron Aunty Hannatu wanda dashi kaɗai akazo dan ƙaramine sosai.
      Suma su Zarah sun fito suka gaisa dashi, yace, “Walida kece ƴar zaman ɗaki ko?”.
     Dariya tayi tana faɗin “A’a malam, ai Umma bazata yardaba”.
      “Aini sainaje na roƙeta tabamu ke auta. Idan kuma auta batason nesa da Umma sai a bamu Zarah”.
      Dariys sukayi, Zarah na faɗin, “Ai sai arasa gane matar gidan da ƴar zaman ɗakin”.
      Miƙewa yay yana murmushin maganar Zarahn, yaɗan saci kallon jiddah dake gefe kanta a ƙasa ya fita abinsa.
       Sosai suka shiga yaba masa dajin ƙarin ƙaunarsa a ransu, tareda kuma taya ƴar uwarsu murna.
      
     Sai la’asar lis suka bar gidan, bayan sun kammala kimtsa komai, kayan gara kuwa sashen Maimunatu suka kaisu tareda kayan cin-cin daduk suka ɗiba mata, itama Jiddah aka ajiye mata nata.
      Har gate suka rakosu Jiddah na hawaye, duk sai tausayinta yakama Maimunatu, dan da gaske duk amarya saitaji wannan damuwar a farkon aurenta, kaitajin tamkar ka koma gidanku.
      Itace taita lallashinta bayan tafiyarsu, harma jiddahn taɗan saki jikinta.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

          Abba baibi takan hajia hindu ba yagama shirinsa ya fice, yau koma yaran bai sauraraba, danshifa haushinma kowa yakeji, shikaɗai yasan tanajin kalar rashin mutuncin daya shirya zuwa ya saukema Uncle yahya da Umma. 
       Koda ya fito gidan Alhaji garba ya nufa. Da ƙyar Amarya tabarsa ya fito, shima danya mata bayanin cewar kuɗi ƙila Abba ya kawo masa, har tsakar gida tamasa rakkiya, saima tasamu wajen zama tana jiran su gama taja abinta su koma. Hajia deluwa batasan hidimar da akeba, tanacan zaune jigum a falonta abin duniya yagama addabarta.
   
      Fitowa abba yayi daga cikin mota yabama Alhaji garba hannu suka gaisa, kokaɗan fuskar Alhaji garba babu fara’a, sai wani ciccijewa yakeyi, shidai Abba ya danne tashi zuciyar dan masalaha yake nema yau.
        “Alhaji idan ban takurakaba dan ALLAH magana nakeson muyi dakai”.
        “Magana kuma Alhaji Zakari, to aini babu sauran wata magana a tsakaninmu yanzu saita kuɗina”.
      “dukda haka dai ka daure ka saurareni, nasan zakayi farin ciki da hakan”.
      Umarni Alhaji Garba yabama direba yakawo musu kujeru, hakan da hajia amarya taganine yasata komawa sashenta takawo musu lemo, Abba dai sai kallonta yake da mamaki, dan yasha ganinta tazo shagon Alhaji garba, har mutane kansha dangantata da karuwarsa ce, to yanzu kuma mitakeyi a gidansa?. Bashida mai bashi amsa dan haka ya maida hankalinsa kan Alhaji garban.
     Sabuwar gaisuwa suka sake kafin Abba ya ɗora dayima Alhaji garba bayanin abinda ya faru akan auren Jiddah, Alhaji garba dai baice uffanba. Ganin haka sai Abba yakuma gyara zamansa yana faɗin, “To ni yanzun nayanke wata shawarar danasan zatai maka daɗi insha ALLAHU, tunda dai hakan ta kasance mizai hana nabaka ƙanwar ita Jiddah ɗin Zarah, itama yarinyace mai hankali, kuma tana kama da Jiddahn ma sosai wlhy”.
        Wani banzan kallo Alhaji garba ya zubama Abba, “Alhaji Zakari nakula dai kama maidani wani sha katafi kawai, to bara namaka gwari-gwari dai kawai, bana buƙatar auren kowace yarinya ma ni yanzun, dan na auro wadda take tsaremin komai dake sakani aure-aure, yanzu hakama dai zancen danake maka gobenan zakaga sammaci, dan nariga na shigar dakai kotu akan kuɗina. Naji tausayin haɗaka da Ashir ne kawai wlhy, dan kaɗan daga aikinsa yasaka fitsari a tsaye, nabarka lafiya, saimun haɗu a kotu”.
      Gaba ɗaya abba yagama ruɗewa, duk maganar da yakema Alhaji garba yaƙi saurarensa, saima yunƙurin shigewa sashen amaryarsa da yakeyi. Akuma dai-dai wanann lokacinne hajia deluwa ta fito saboda jin ƴar hayaniyar maganar da abba kema Alhaji garba.
     Ai tanayin ido huɗu da Alhaji garba itama saitayi kansa da gudu. Saurin shan gabanta Amarya tayi.
       “K ballagazar mace nutsu mana, minene kikeyi haka tamkar sabon kamu?”.
      Takaicine ya cika Hajia deluwa, ta ɗaga hannu da nufin marin Hajia Bariki sai caraf aka riƙe hannun nata, Alhaji garbane yariƙe, yayinda ɗayan hannunsa ya toshe hancinsa dan wani irin mugun warin dayafi na jiddah yaji tana masa”.
     “k shashasha, karki sake ƙazamin hannunki ya hau kan matata”. Ya ƙare maganar tareda hankaɗe hajia deluwa yakama amarya suka shige abinsu.
       Tibiran Hajia deluwa tashiga hauka a cikin gidan, ta koma sashenta ta ɗakko taɓarya tazo taita dukan ƙofar, su balki mai aiki da mai gadi da Abba dabai tafiba sunyi cirko-cirko suna kallon ikon ALLAH. Daga ƙofa hajia deluwa saita koma winduna taita fasa gilasan.
    Dolefa Alhaji Garba ya sake fitowa, ƙyaƙyƙyawan mari ya zubama Hajia deluwa.
      hannunta dafe da hancinta. Cikin jin azabar shigar marin ta cakumi wuyan rigarsa, tunifa kokawa ta hargitse a tsakaninsu, ƙarfi ba ɗayaba yahau jibgarta ganin zata zubar masa da mutunci gaban ma’aikatan gidan. Saida yay mata lilis tana kuka da zaginsa da jan ALLAH ya isa ya turata cikin sashenta ya kulle. 
     Su Ashir duk basa gida, shiyyasa Alhaji garba yasamu wannan damar.
       Mota Abba ya shiga yafita yana sheƙa dariyar mugunta, aganinsa wannan tashin hankalin kaɗai ya ishi Alhaji garba mantawa da maganar kuɗinsa, indai hakane kam zaisa hindu taita tunzura Hajia deluwa dan ta ɗauke hankalin Alhaji garba.


????????maga yanda za’a kwashe to⛹‍♀????.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

         Su Umma na zazzaune a tsakar gida tanashan labarin gidansu jiddah da su aunty hannatu ke basu Abba ya shigo fagan-fagan tamkar an jehoshi.
     Saikuma yayi turus ganin duk ƴaƴansa gasu Yaruwaiya kuma, gashi duksun watso masa idanu tamkar wani ojuju.
       Ɗauke kai Umma tayi tamkarma bata gansaba, sai yaranne suka shiga gaidashi, cikin sarƙewar harshe ya amsa musu da tambayarsu ya yara. Abin yabasu matuƙar mamaki.
    Umma data fahimci tsorata yayi da ganinsu sai abin yabata dariya, dan alamunsa duk sun sunana bada arziƙi yazoba, ita dama tasan arziƙin bazai kawoshi a irin wannan lokacinba, ballema Jiddah ta tare bai saniba.
    Gani kawai sukai yajuya yafita batareda yashiga cikiba, hakanne yasasu tunanin anya lafiya kuwa?, Yaruwaiya tayi murmushi dan itama ta fahimci ba arziƙi ya kawoshiba, ganinsune yasakashi tsorata shine yafita..
   
       Daga nan gidan Abba gidan Uncle yahya yaje ya aika a kira masashi, danya kira wayarsa a kashe.
    Amma koda ɗan aiken ya fito saiyace ai Uncle yahya bayanan ma, ance yaje Adamawa.
     “Adamawa kuma?” Abba yafaɗa a fili cikin mamaki da al’ajabin uwarmi akeyi a adamawar kuma?.
    Bashida mai bashi amsa, danhaka yabar anguwar da ƙudirin ai gobema ranace ko, zai dawone.

????????Abba kana ruwa gaskiya????.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

       *BAYAN KWANAKI UKU* 

     Abubuwa dayawa sun faru takowanne ɓangare, dan hajia deluwa tana cikin jin azabar jin jiki su Ashir suka dawo suka sameta, hankalinsu tashe sukahau tambayarta miya faru, cikeda magagin azaba tafaɗa musu abinda ya faru, takumace Alhaji Zakari ne da Amarya suka saka Alhaji garba dukanta.
     Sosai Ashir da bala suka hasala, suka kuma kira babban wansu suka sanar masa abinda ya faru.
    Ransa a matuƙar ɓace shima yazo gidan, sai dai kuma Alhaji garba yaƙi fitowa, wannan ne yasaka su sakawa amusu bincike akan Abba.
    Ita kuma suka kaita asibiti, kwananta uku cif tana jinya acan, yau da safe aka sallamosu, suna direta a gida kuma suka nufi gidan Abba da akai musu kwatance.


????????????⛹‍♀Abba maza bisa kanka.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

         A gidan Sheikh Aliyu dai sai muce Alhmdllh, dan suna cikin aminci gwargwadon iko, bandama dai Maimuna dake fama da lalurar laulayi, wadda kuma Alhamdllh tana samun kulawa ga mijinta da Jiddah ma, dan ƙiri-ƙiri Jiddah ke ƙoƙarin hanata wasu ayyukan, dukda itama Maimuna na hana jiddah, acewarta amaryace saita gama amarci sannan.
     Amma sam Sai Jiddah taƙi bari. Hakanne yasaka Aliyu kuma samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya, a gefe kuma yana addu’ar ALLAH yasa su ɗore hakan.
      Shida Jiddah dai kam tun ranar bai kuma takurata ba, dan soyake takuma sakin jikinta tamkar yanda yaga ta fara, ƴan wasanni dai kam yakanyi da ita, dan har yanzu a sashenta yake kwana saboda kwanakin da Maimuna ta ƙara musu, da safe Jiddah taita ɓoye fuska batason su haɗa ido, shikam yata tsokanarta kenan yana dariya.

       Yaukam tunda suka gama fira a sashen maimunatu ta dawo nata sashen, tana gama shirin barci saiga Aliyu ya shigo shima cikin nasa shirin.
      Kallonsa taɗanyi tana amsa sallamar a saman laɓɓanta, mamaki yabata, takula tunda yasha kunun kwakwar ɗanzun yakoma wani shiru, firarma daina saka musu baki yayi, yabarta itada Maimuna kawai.
    Cikin sauke numfashi tace, “Kobaka jin daɗine?”.
     Murmushi yay mata danya kula batasan dawan garinba, amma harga ALLAH tausayintama yakeji shi, dan yasan yau kam bazai iya juriyar binta a hankaliba tunda yasha kunun kwakwarnan…………????✍????


*_Ya Sheikh masoyan jiddah fa sunce kabi a sannu dan ALLAH????????⛹‍♀_*

_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

????????karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*????????????????????????



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button