NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 53 – 54

      Tunda aka baro kasuwa da Abba ƙananun magana ke tashi, kowane baki da abinda yake faɗa akan wannan tafiya da ƴan sanda sukayi dashi.

★★★★★★★★★.

          Hajia hindu da yara tun suna tsumayen shigowar Abba har suka bari, gashi yau yamusu alƙawarin sayo musu kayan daɗi idan zai dawo kasuwa, hakanne ya saka  yaran zumuɗin dawowarsa, amma har goma na dare tsit kakeji babu amo babu labari.
     Ƙosawar dasu kalifa sukaice tasakasu fara tsaki, itako hajia hindu takaicinta da tunaninta yanakan cewa Abba yana gidan Ummane jarabarsa ta kaisa, hakanne yasakata ɗaukar masifaffen fushi, tacika tayi fam dan kumbura, sai kaɗa ƙafafu take na tsumuwar bala’i.
      Wasa-wasa dai har shabiyun dare, tuni ta kora yaran ɗaki sunje sun kwanta, itakam tana zaune tana shiryama Abba shika-shikan bala’in da zata ɓarar masa idan yadawo gidan. Dataga lokaci ya jane taje ta kwanta itama.

Hummm????????

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

          Iya tantance tsakanin aya da tsakuwa jiddah tayi a daren jiya kam, shikansa ya Sheikh yasan yabuɗe ƙwanji da yawa, kuka dai hajjaju jiddah an shasa har an godema ALLAH, sai taji ranar ashe wasan yara akayima, yau ɗinne ta tabbatar da menene daren farkon.
       Tana zaune bisa abin salla ya dawo masallaci, kanta a ƙasa ta amsa masa sallamar.
     Muskarsa shinfiɗe da murmushi ya zauna a bakin gadon yana kallonta, cikin rawar murya tace, “Ina kwana”.
      “Ba irin wannan gaisuwar akema mijiba ai kairunnisaa”.
     Batareda ta shiryaba taɗan ɗago ta kallesa tai saurin janye idonta gefe.
      “Ya kika fasa kallon nawa Hauwa-Jiddah?”.
    Shiru tayi takasa bashi amsa, tasowa yayi da kansa ya kamata ya miƙar tsaye, dukda tagaza kallonsa bai damuba, ya cire mata hijjabin tareda sumbatar goshinta da laɓɓanta, cikin kuma sanyaya muryarsa yace, “ALLAH yay miki albarka kinji, yabama su Ummi ladan tarbiyar da suka baku”.
    Hawayen da take maƙalewa suka silalo, a zuciyarta ta amsa da amin.
     “Kukandai bazai ƙareba Jiddatulkhair?”. Yay maganar yana share mata hawayen.
     Haɗiye sauran kukan tayi da ƙyar, cikin sinne kanta tace, “A’a na daina, bara naje kar aunty tace zatayi aiki da kanta, kaga jiya ta yini batajin daɗi ma”.
        Murmushi yay idonsa akan laɓɓanta dake motsawa a hankali, ya ɗora goshinta saman nasa yana kallonta, “Ai kema bakida lafiyar, kiyi kwanciyarki zanje na tayata ni, dan yau a gida zan yini”.
      Ba ya da ta iya dole tabi Umarninsa ta kwanta ɗin, shikuma ya fice sashen Maimuna.
      A kicin ya sameta tana ƙoƙarin kwaɓa filawar da zatai fankasu, ya sumbaci gefen kuncinta yana faɗin, “Jazakillahu bil jannah Ummudduniyah”.
       Murmushi tayi dukda kishinsa da takeji na taso mata, taɗan juyo itama ta sumbaci kuncinsa tana amsawa da, “Tare da kai Kalby”.
          “Ya babyna?”. Yay maganar yana zagayo da hannunsa a cikinta daya fito sosai.
      “Yana cikin ƙoshin lafiya Nurry, sai dai kewar Abbunsa da yakeyi sosai”.
     Numfashi ya sauke a cikin kunnenta, cikin raɗa yace, “Shima Abbu yana kewarsa matuƙa, ko zamuje yanzu mu gaisa”.
      Dariya Maimunatu ta sanya, “Yaya nikam rufamin asiri, ina ƙanwata?”.
        Murmusawa yay yana sakinta kafin ya shafa kansa, cikeda jin kunyarta yace, “nabarota tana azkar, mizan tayaki dashine?”.
         Maimuna tai murmushi kawai, dan tasan badai azkarba, da azkarne ai dabaizo tayata aikiba, a filikam sai tace, “A’a na hutashsheka”.
      “Nikuma ban hutar da kainaba madam”.
     Babu yanda ta iya dole ta barsa sukayi aikin tare, bayan sun kammala yakoma ɗakinsa.
    Wayam ya tarar babu kowa jiddah ta gudu, amma an gyara ɗakin tsaf yanata ƙamshi.
    Wanka yayi yashirya cikin ƙananun kaya, sosai yay ƙyau tamkar ba shiba.

         Jiddah data gudo tuni koda tadawo sashen natama ba kwanciyar tayiba, gyara ɗakinta zuwa falo taɗan kumayi, ta ɗaura ruwa ta dafa  takuma gasa jikinta sosai sannan tai wanka, tagama shirinta tsaf tana ƙoƙarin kunna wayarta Aliyu ya shigo.
    Kallo ɗaya tamasa ta ɗauke kanta tana amsa masa sallamar, sai dai yamata ƙyau sosai, yaune ranar farko data taɓa ganinsa da ƙananun kaya, ashe dama yana sakawa….?
    Har ya iso gabanta bata saniba, saida ya riƙo hannuntane tadawo hayyacinta. “Malama jiddah tunanin mi akeyine haka? Ko nawa?”.
       Murmushi tamasa kawai.
     Shima saiya murmusa yana faɗin “Kinyi ƙyau sosai tawan, irin wannan gayu haka mai hana ango fita?”.
      Sosai ta dara yanzukam tana rufe baki, shima dariyar yakeyi zuciyarsa namasa daɗi da sakin jikinta da takeyi dashi sosai yanzun.

       Saida ta saka gyale sanan suka nufi sashen Maimunatu, yauma dai kosau ɗaya Jiddah bata yarda sun haɗa ido da maimuna ba, sanan bata saka baki yau a hirarsu sosai kamar sauran ranakun, shi Aliyu yasan kunya da sauyin da jikinta ya matane ya kawo hakan, itakuma Maimuna sai takejin tsoro a ranta kar jiddah ta fara sauyawa saboda daɗin miji data fara ji.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

            Da safe koda su Kalifa suka wuce makaranta sai hajia hindu tai shirin zuwa gidan Umma da nufin mata barka da tashin baƙi wai, amma kuma abinda ke a ranta shine son ganin idon Abba.

      Ta iso Umma ce kaɗai a gidan, Walida da Zarah duk sun wuce makaranta, zarah wata islamiyya ta shiga anan anguwarsu ta matan aure, ana zuwa tara a taso sha ɗaya, gani tagama ssce exam ɗinta da zaman banza sai Umma tace tashiga islamiyyar kafin ALLAH ya kawo mafita, idan auren ne kokuma saɓanin hakan.
     Umma na jan ruwa a rijiya Hajia hindu tayi sallama ta shigo.
    Ɗagowa Umma tayi tana amsa mata sallamar da mata sannu da zuwa, sai dai ƙasan ranta tayi mamakin ganinta, dan ranar tariyar jiddah ma sai yamma liƙis tazo gidan, kuma bata daɗeba ta tafi.
          Amma sai Umma ta tareta da ƙyaƙyƙyawar fuska, bayan tace mata tashiga falo itakuma ta ɗiba ruwa ta bita.
      Kafin Umma ta shigo hajia Hindu tai saurin leƙa bedroom ɗinta wai ko Abba yana ciki, wayam ta gani, hakanne ya sakata saurin komawa ta zauna saboda jin motsin tahowar Umma.
        Ruwan Umma ta ajiye mata sanan ta zauna suka gaisa suna tambayar juna yara. Kafin cikin kissa hajia hindu tace, “Ai zuwa nai dama Zarah ta rakani nagano gidan ƴata Jiddah”.
     Umma tace, “ALLAH sarki, gashi kuma kunyi saɓani tanama islamiyya”.
      “Kai amma banso hakanba wlhy, shiyyasa naita roƙon Abbansu ya jirani mufito tare tunda yace nan zaizo”.
     Murmushi Umma tayi batace komaiba, hakanne yasakasu yin ɗan shiru na wasu mintuna……
       Sallamar Uncle yahya ne yasaka Umma miƙewa tafito tana amsawa, yanda ta gansa kamar a rikicene ya sata tambayar “lafiya kuwa Uncle ɗinsu?”.
       “Wlhu Maman Nafisa babu lafiyarnan, dan yaya aka kama tun jiya, sai da safenan naje kasuwa nakeji, naje station ɗin da aka kaisan kuma sunƙi bani belinsa, yanzu dai haka zancen danake mikima sunce kotu za’a shiga gobe idan ALLAH ya kaimu”.
      Cikin dafe ƙirji Umma tace, “Akanmi ni Yagana?”.
    Cikin tsantsar damuwa Uncle yahya yace, “maganar kuɗin Alhaji Garbane”.
     Hajia hindu tafito  itama a rikice tana sallallami, mamaki sosai Uncle yahya yayi da ganinta, amma dayake a ruɗe yake sai baibi takantaba suka shiga maganar mafita kawai………….✍????

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button