MUTUM DA DUNIYARSA 55 – 56

Cikin dare saiga ɓarayi sunyi dirar mikiya a gidan Abba, tun Uncle yahya najin hayaniya sama-sama harya fara jiyo magiyar da Abba kema ɓarayi da roƙonsu.
Zuwa can kuma yajiyo suna dukan Abba yana kukan ihu, sai ihun hajia himdu da yara dayake jiyowa suma, gabannin asubahi saiyaji tsitt alamun ƴan fashin sun tafi, sai koke-koken yaran da hajia hindu.
Hindun yashiga ƙwalama kira yana buga ƙofar, kalifa yaje ya buɗe Uncle yahya.
Uncle yahya na fitowa yaci karo da Abba a yashe tamkar gawa, kallo ɗaya zakai masa kasan amatuƙar jigace yake da duka.
Kansa kawai Uncle yahya yayi yana kuka, itama Hajia Hindu da alama an daketa a ƙafa, dan zaune kawai take gaban Abba tana hawaye.
Ganin Abba ko motsi bayayi yasaka Uncle yahya barinsa yatashi ya fita neman motar kaisu asibiti….
★★★★★★★
Taimakon gaggawa aka shiga bama Abba, da ita kanta hajia hindu da aka jima ciwo a ƙafar haggu.
Hankalin Uncle yahya bai kwantaba saida akace masa Abba ya farfaɗo, amma anmasa Allurar barci. Itama hajia Hindu barci takeyi.
A lokacinne yasamu nutsuwar ɗaukar su Hassan yakai gidan Umma.
Duk da Uncle yahya bai sanar musu tushen matsalarba, Hankalinta yatashi daga ita harsu Zarah dajin abinda ya faru, kuka sukeyi sosai abin tausayi.
Umma da Uncle yahya ne kawai suka koma asibitin, akabar su kalifa anan gida taredasu Walida.
Batun tashin hankalidai ba’a maganarsa ga wanan family yau, dolene kagansu su baka matuƙar tausayi, ƴan adamawa ma duk an sanar dasu, hakama Aunty Zulai dake huntuwa.
Aunty Nafisace ma hartazo asibitin, Jiddah ce kawai Uncle yahya yaƙi sanar mata.
A ranar a asibitin Uncle yahya da Umma suka kwana wajensu Abba.
Su Kalifa kuwa acan wajensu zarah, sukaita zubama su Zarah rashin kunya akan bazasuci garau-garau da Walida ta dafa ba, wai sai dai aimusu miya, su Mom bata basu abinci da mai da yaji.
Daga Walida har Zarah watsar dasu sukayi suka cigaba da hidimarsu, idan yunwar ta rarakesu ai saci.
Ilai kuwa zuwa dare da sukaga babu mafita sai suka ɗauka sukacin.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Washe gari su aunty Hannatu dawasu a cikin dangi suka iso, Abba dai ya farko, sai dai ko magana baya iyayi saboda kumbura da fuskarsa tayi dam, tsakaninsa da mutane sai dai ido, ga karaya har biyu a ƙafarsa da ƙugunsa saboda duka sukai masa na fitar hankali.
Itama hajia hindu ta farko, kuma ita da sauƙi sosai, dan nata gocewar ƙashine.
Duk wanda yaga Umma da Uncle yahya a wanan lokacin saisun baka tausayi, dan dukkan lokacinsu yanakan Jinyar Abba da hajia hindu ne, hakama hidimar asibitinsu sai da kuɗinsa akeyi.
Zuwa dare su Aunty Sauda suka ƙarasa gida dansu huta. Dukda ba abin daɗi bane ya kawosu, kuma basu daɗe da tafiyaba daga bikin Jiddah hakan bai hanasu Zarah murnar zuwansuba.
Su kalifa kam sai suka hau kumbure-kumburen baki wai basason wanan gidan hayaniya tayi yawa da ƙauyawa.
Hakanne ya fusata Aunty Nafisa ta zubama kalifa mari har biyu ƙwarara, aiko ya zauna yana zaginta, Aunty Zulai tasa wayar caja ta zaneshi sosai, dama haushin yaran sukeji to????
Wanan duka da akaima kalifa yasaka su Hassan nutsuwa waje ɗaya suka haɗiye tasu rashin kunyar, shi dama Munner bashida matsala, kasancewarsa ƙarami baikai sauran wayoba.
Zarah ce ta sanar musu Jiddah fa bata san halin da ake cikiba, Uncle yahya ya hana a sanar mata.
Numfashi Aunty Sauda ta sauke tana faɗin, “Nidai a ganina yakamata ta sani, dan gaskiya Abba yanajin jiki, mubama Uncle shawarar ya sanarma koda mijintane koya kukace?”.
“Wanan shawarar taki tayi aunty Saudah wlhy”. Cewar aunty Nafisa dake bama yaron aunty hannatu akamu.
Sun yanke shawarar masa magana da safe idan sunje asibiti.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Yau Jiddah cikin ɗoki take Aliyu zai koma wajen Maimunatu. Dan kwanakinta goma sun cika harda kwana shidan da maimuna ta ƙara musu. Dukda ba takurata yakeba itadai sotake ya koma can.
Su kaɗaima sukai hirar dare yau, danshi tunda safe yay tafiya shida malam dawasu malaman yin wa’azi jihar katsina.
Har sukai sallama Jiddah tatafi sashenta bai shigoba.
Saida tagama shirin barci tana ƙoƙarin kwanciya taji bugun ƙofa da sassanyar muryarsa yana kiran sunanta.
Hijjab ta saka tazo ta buɗe masa ƙofar falon.
Taɗanyi mamakin ganinsa da jallabiya, kenanma harya dawo yay wanka, haka kawai saitaji wani iri a zuciyarta, ya dawo amma ba’a sanar mataba balle tafito masa sannu da zuw…….
Numfashi ta sauke saboda jinta a jikinsa, cikin kunnenta ya raɗa mata “Yadai Jiddatulkhair? Ko bakiyi kewata baneba?”.
“Humm nayi mana”.
“Shine kikaƙi zuwa tarbata?”.
Shiru tai bata bashi amsaba, hakan yasakashi ɗago kanta yana kallon fuskarta data canja alamar damuwa.
“Mike faruwa? Naga kamar ranki a ɓace”.
”Babu komai” tai maganar tanason janye jikinta daga nasa.
Rikota yayi daƙyau, yajata zuwa saman kujera, saida ya zauna sanan ya ɗorata a cinyarsa.
“Mike faruwa? Faɗamin kinji Habibty”.
“Nifa nace babu komai”.
“Uhm-uhm ban yardaba wlhy Jiddah, karkiga ban daɗe da saninkiba kiyi tunanin ban fara fahimtar halayyarkiba, wani abun akai miki”.
“Ba aimin komaibafa ni, Amma shine ka dawo bamsaniba har saida ka daɗe, bayan tun ɗazun muna dakon zaman jiran dawowarka tare da auntyn”.
Murmushine ya ƙwace masa babu shiri, wato duk yanda mace take baka rabata da kishi, wanan jinin jikinsune, rungumeta yay sosai yana faɗin “To amin Afuwa amarsu, nayi tunanin kar in takurakine, dan kina baro sashen auntynki babu daɗewa ina shigowa”.
Yinƙurawa tai zata tashi yay saurin maidota a cinyarsan, zatayi magana ya ɗora bakinsa kan nata…..????
Ajiyar zuciya taita saki bayan ya saketa, uffan bata iya cemasaba har ya kawota ɗaki ya kwantar, saida yay mata addu’a ya tofeta sanan yashiga mata tausa a hankali.
Luf tayi tamkar tayi barci, hakanne yasaka Aliyu barinta, ya kashe mata fitila sanan ya fita tareda ja mata ƙofar.
Yana fita hawayen da batasan dalilinsuba suka ziraro mata, itadai tasan tayi murna dazaije can ya kwana, dan itadai takura takeyi da kwanciyarsu a gado ɗaya, amma batasan dalilin dayasa wani sashen zuciyarta yakejin ɗaciba, komi hakan yake nufi oho?.
Ta daɗe batayi barciba tanata juye-juye, sai can tsakkiyar dare barci ɓarawo yay awon gaba da ita.
★★★★★★★
Da asuba lokacin daya leƙo tashinta salla harta tashi, tana zaune a bakin gado tana addu’ar tashi daga barci ya shigo. Kallo ɗaya taimasa tai ƙasa da idonta tana gyara wuyan rigarta take a buɗe sosai.
baice da ita komaiba ya juya ya fita, ta ɗanbi bayansa da kallo harya ɓacema ganinta. Ajiyar zuciya ta sauke tamiƙe zuwa bayi ɗauro alwala…………✍????
_Masoyan Abba zakari Amin afuwa fa, babu ruwana Alƙaline????⛹♀⛹♀⛹♀????_.
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
????????karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*????????????????????????
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????