MUTUM DA DUNIYARSA 61 – 62

*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_[61➖62]_*
…………Koda su Ashir suka amso kuɗi a kotu ƙiri da muzu suka hana Alhaji Garba, hasalima shi baisan wainar da
suke toyawa ba, dan yakoma sashen amaryarsa ya tare, kwata-kwata baya barin rana ta gansa, musamman ma da yanzu yasan yanada laifi a wajen ƴaƴansa akan abinda yayma mahaifiyarsu, toshi babban ma abinda yakeji a ransa gameda ita shine tsananin tsanarta, ko kaɗan baya sha’awar koda tunata ma.
A yau yay nufin kiran Abba ya tuna masa zancen kuɗinsa, amma sai wayar taƙi shiga, hakanne yasakashi maida akalar kiran ga yaransa na kasuwa akan su bincika masa Alhaji Zakari a shagonsa.
Mamaki ya kama Labaran, yace, “Alhaji wane kuma Alhaji Zakari za’a gani a kasuwa bayan shagon nasama yadawo naka?”.
Zaune sosai Alhaji garba ya tashi, dama kwance yake amarya namasa tausa, ”Labaran ban fahimci zancen nakaba ai nima, bani a warware”.
Labaran dai baiyi jayayya ba ya ɗakko labari tundaga tushe ya zayyanema Alhaji Garba, babu shiri kuwa ya rikito a gado, amarya na tambayarsa mike faruwa bai kulataba.
Sashen Hajia Deluwa ya nufa, wadda zuwa yanzu ka ganta dole tabaka matuƙar tausayi, dukta kuma ficewa hayyacinta, ƴan kuɗin da su Ashir suka amso miliyan goma suka bata, sukuma suka rabe sauran harda ƙanwarsu dake karatu. Shagon kuma yazama na yayansu saboda shine ya saya. Amma sai sam kuɗin basu gusar mata da damuwarta ba, itadai tafi buƙatar mijinta a gareta, babban tashin hankalinta na gaba kuma warin da takeyi, wanda hatta ƴaƴanta saisun toshe hanci suke iya zuwa inda take, jiya wata ƴar uwarta tazo gidan, amma sam kasa zama tayi tanata faman toshe hanci, ita kuma ko kaɗan batajin warin saima ƙamshinta na gayu datake zubawa a kullum……..
Banko ƙofar da Alhaji garba yayine da ƙarfi yay matuƙar firgitata ta miƙe zumbur tana kallonsa,
“Alhaji lafiya kuwa?”.
Hannunsa toshe da hanci yace, “Ban kuɗina”.
Cikin sanyaya murya tace, “wane kuɗi Alhaji?”.
“O bama ki saniba ko? To wanda ƴaƴanki sukaje suka amsa a kotu”.
Baki ta taɓe cikin ƙarfin hali, “Yanzu dan ƴaƴanka sunci waɗannan ƴan kuɗin daga cikin abinda yake haƙinsu shine zakazo kanamin hayaƙi, idan ka mutu sukeda gadon su ai”.
Galala yay yana kallonta tamkar wani soko, yace, “Aiyyyy dama maganar danakeji a gari gaskiyane? Bakida buri saina mutu kuci gado keda ƴaƴanki, to aiko yau ɗinnan basai gobeba zaki kama gabanki, saidai kisa a biyo dare yau a kasheni, kosu su Ashirun suzo su karni gobe a raba muku gado, bankuma yadda keɗin jahila baceba sai yau wlhy, dama da ALLAH yayma namiji arziƙi to kullum burin mace ya mutu suci gado itada ƴaƴanta, shiyyasa kikaita korar min mata kina musu asiri ko?, to ai dama tuni bokan naki yazo ya sanarminin kafin ya mutu, dan har kasuwa yazo ya sameni ya faɗan duk tsiyatakun da kuka aikata, harda haukata yarinyar Alhaji zakari, wanan ne yasani burin barmasa kuɗin, dama ina masa barazana ya banine domin hakan yazama izinina a garesa ya kiyayi halayyar cin bashi, shine ku ƙwararru kukaje kuka amshi kuɗin, kisani wanan karon bazakuci a banzaba kamar yanda kuka sabaci, insha ALLAHU kuma saikin rigani mutuwa, kije na sakeki saki Uku, kuma a yau nakeson ki barmin gidana”.
Wani gigitaccen ihu hajia deluwa ta kwala ta yanke jiki ta faɗi a wajen babu rai.
Alhaji garba baibi takantaba yay fitowarsa.
A wanan mummunan yanayin autarta data dawo daga makaranta yau cikin ɗokin ganinta ta isketa, bata sanarma kowa zatazoba saboda ta basu mamaki, sai ita ta tarar da abin mamakin.
Itace takira baban yayansu a waya.
Ankai hajia deluwa asibiti a sanƙame, bakuma a samu farfaɗowarta ba sai washe gari, wanda har zuwa lokacin babu alhaji garba babu dalilinsa, ama ranar suka cane dubai yawon amarci shida amaryarsa.
Hajia deluwa dai sai yamma lis ta farfaɗo, saidai kuma tasamu mummunan ciwon ɓarin jiki, ɓarinta na dama baya aiki gaba ɗaya har ido ɗaya, saida ɗaya take gani shima bishi-bishi, baki kuwa ya karkace yana zirar da yawu.
Ƴaƴanta sun shiga tashin hankali matuƙa, sunyi kuka sosai dan suna ƙaunar uwar tasu, sai dai basuda yanda zasuyi.
Haka suka cigaba da jiyyarta, tun sunayin abun da marmari har suka koma biyan likitoci su kula da ita, suko suka koma kan harkokinsu, sai dai suzo su dubata. A kwana a tashi kuma sai dubiyarma ta fara gagararsu zuwa, dan saisu haɗa kwanaki biyu basu leƙata a asibitiba.
Likitoci suma suka fara ƙosawa da ƙazantarta, aiko suka kira su Ashir suzo su kwashi abarsu.
Wannan ne silar dawowarta gidan jiyya, har kuma sanan Alhaji garba bai dawoba, dan sunacan suna hutawarsu da amarya dake fama da ƙaton ciki, haihuwa yau ko gobe.
Tunda aka maido hajia deluwa gida fa babu mai mata kallon arziƙi, dan bilki mai aikima tuni ta gudu abinta, haka hajia deluwa zatayi kashinta da fitdari babu mai gyarawa, ga tsoro da ake bata kullum, taita ganin halittu masu ban tsoro, haka zataita kuka babu damar ihu, wanima lokacin dariya za’aita ɓaɓɓakawa, amma tarasa a inane, kokuma aita kuka, ko kukan dabbobi kala-kala, gaba ɗaya ta susuce, itaba mahaukaciyaba ita ba gawaba. Mai kula da itanma saita gadama take bata abinci tana toshe hanci, data zirara mata take baro sashen.
autarta kuwa ƙiri-ƙiri tabar zaman sashen, takoma sashen babanta, saitayi satima bata kalli sashen hajia deluwaba.
Ruwa a jallo hajia deluwa ke fatan ganin koda ɗaya daga cikinsu Jiddah ne ta nemi gafara, tasan dai bama kowane zai yafe mataba, dan ita kanta batasan iya adadin matan data salwantar ba akan kar’a zauna mata da miji, wasu jini ta sakar musu, wasu warin jaɓa, wasu hauka, wasu kuwa taita ɓarar da cikin da suka samu dan karsu haihu a gidan, watama muguntar data saka bokanta yayi ta manta kalarta, gashi a yau tana girban abinda ta shuka.
ALLAH ka shiryemu, ka tsaremu daga son zuciyoyinmu????????????
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Yau dai kam a gida Jiddah ta yini abunta, sosai takema Abba hidima tamkar sauran ƴan uwanta, komai yace yanaso kafinma ya rufe baki an masa, yau kuma ƴan adamawa ma sukazo suka dubashi, amma basu kwanaba suka juya gida, kowa ya gansa saiya tausaya masa, dan sosai yanajin jiki.
Hajia Hindu ce dai da sauƙi sosai, dan harta fara ɗan takawa, ita babban tashin hankalinta yanzu kuɗin dake hannun ƙaninta, kwata-kwata takasa samun Number sa, takuma rasa wazata kira ya haɗata dashi, itama dai ƴan uwanta na zuwa jefi-jefi dubata, dan ba kowaba, acewarsu batada mutunci, mutum ko zuwa gidanta yayi tata masa yatsine-yatsine kenan, ko ta saka ƴaƴanta suyita maka rashin kunya.
★★★
Tun daga ranar duk bayan kwana biyu Jiddah sai tazo gida ta yini, kullum dare kuwa Aliyu sai yazo duba Abba, haka mijin aunty Nafisa ma, mazan su Aunty Hannatu ma duk sunzo, kasancewar ba’a kusa sukeba basa gajiyawa da kiran waya kullum safe da yamma.
Malam ma da tawagarsa yazo har gida ya duba Abba, yadai sha addu’oi kam.
Hakama dangin Umma duk sunzo dubashi.
Haka aka cigaba da jiyyar Abba dake matuƙar shan baƙar wahala karayar ƙugunsa, dan na ƙafar Alhamdllh harma an kwance, dukya rame yayi baƙi. Dolene ya baka tausayi saboda jigatuwa da yakeyi, zuwa yanzun kam yafara laushi.
Dan matar son nasa Hajia hindu ko ruwa wanan bata taɓa damuwa da zaman bashiba balle sannu da jiki, kullum cikin sakar masa habaici take da takalar su Umma fitina, idan anyi abinci sai tace bazasu ciba, yaranma harda kuka wai basu iya ciba, abinda yakuma birkitata kuma shine koro su kalifa da akayi daga makaranta, dan an kasa biya musu kuɗi, ta kafa tijara sai a siyar da motocin Abba biyu data kai yaran makaranta a biya musu su koma, Uncle yahya kuma yace bata isaba, tunda ba haƙinsu bane su kaɗai, kuma motocima ko an sayar jiyyar Abba za’a cigaba dayi da kuɗin, idan zata bari a maidasu ta gwamnati ta bari, dan kalifa ssce zaiyi, su Hussain kuma kwalfayin.
Amma sam saitace ƴaƴanta sunfi ƙarfin makarantar gwamnati, shiko Uncle yahya yace suyita zama babu karatu, dama ba islamiyya suke zuwa ba, danshi yagaji da iskancinta hakanan, tabarsu suji da jiyyar Abba amma taƙi, kullum cikin tadama mutane hankali takeyi a gidan, ga rashin kunyar su kalifa da basa ragama kowa harshi Abban.
Dan jiya da daddare zafi yasa akama Abba shinfiɗa a waje aka fiddoshi yasha iska, to babu wuta, Umma kuma tashiga da fitilar ɗaki zata ɗakko maganin sauro ta kunna, dan yanzu duk su Aunty Sauda sun koma gidajensu, sai dai suna ƙoƙarin kiran waya, sanan duk bayan sati biyu suna zuwa suyi kwana biyu su koma, Zarah kuwa an kirata hira tana gidan Uncle yahya, tare kuma suka fita da Walida tai mata rakkiya. Ihun Abba kawai Umma taji, aiko tafito a guje, kuka sosai da ihu yakeyi yana faɗin Hussain ya kasheshi.
Umma ta riƙe ƙafar daya riƙe yana ihu da tambayarsa miya faru?.
“Yagana Hussain ne ya takani, amma ko juyowa ya kalleni yaronan baiyiba ya fice abinsa”.
“Hussain kuma? To baya ganine kokuwa?….”
“To inda yana gani zai takashine baƙar annamimiya”. ‘Hajia hindu ta faɗa tana fitowa daga ɗakinta’.
Uffan Umma bataceba, saima hawayen tausayin Abba daya cika mata idanu, waya ta ɗauka takira Uncle yahya, babu jimawa yazo. Shikam kasa haƙuri yayi saida ya zane Hussain daya dawo.
Wanan duka kuwa shine yasaka hajia hindu zama taita tata ruwan bala’i a gidan har dare ya raba. Babu kuma wanda ya kulata sai Zarah data yaɓa mata baƙar maganar data kuma tunzurata, Umma kuwa tahau kan Zarah da faɗa tamkar zata daketa.
Anyi haka da kwana biyu Hajia Hindu tai shirin tafiya legas. Babu wanda maganar bata bashi mamakiba, Abba yace, “Maman kalifa legas kuma? Keko mizakiyi a legas dan ALLAH?”.
“kajimun musakin mutuminnan fa da wani zance, ina ruwanka da abunda zanjeyi acan? Kana kwance rigif tamkar wani tsohon ƙarfen Mota talauci yabi ya cinyeka kace zakamin iyayi, to wajen Harisu ƙanina zanje, shiyyace naje na amso kuɗi na maida ƴaƴana makaranta nasayi gida mu koma mubar wanan gayyar ƴaƴa da jikokin”.
“Humm Hindu kenan, yaushe shi Harisun yay hankalin nutsuwa waje ɗayan da har kikasan inda zaki sameshi balle yabaki waɗanan kuɗin da kika lissafo?”.
“Tofa, tanan kuma ka ɓillo, to ta ALLAH ba takaba, kana aibanta min ƙani ne, to saidai kagani akan ƴaƴanka da insha ALLAH saisun haifa maka ƴaƴan tsakar gida”. ‘Ta ƙare maganar tana nuna Walida dake bakin rijiya’.
Murmushi kawai Umma tayi tacigaba da fifita wutar gawayinta dazata ɗora abincin rana, walida ma da zatayi magana saita harareta damata nuni datai shiru.
Abba kam kasa cemata uffan yayi, saima ya maida kallonsa gasu kalifa dake leƙensu ta window suna kwasar dariya, kai kace wani Comedy film suka samu suke kalla. Cikin haɗiye wani Abu daya tsaya masa a makoshi ya ɗauke kansa kawai.
Hajia hindu taja dogon tsaki tabar wajen tana faɗin, “da kayi magana mana”
Daga jikin Window kalifa yace, “Mom aike boss ce, babu ubanda ya isa tanka miki idan kinyi magana. Shida Dady yama zama gurgu inashi ina faɗa damai ƙafa irinki, kema ba cazakiyi suyi cikiba, kin manta baya sonsu, cazakiyi ALLAH yasa a guntule ƙafafunsa”. Ya ƙare maganar da kwashewa da dariya su Hassan na tayashi.
Ba Abba kaɗaiba hatta da Umma saida maganar kalifa ta girgizata, walida kam kaɗan yarage ta afka rijiya saboda tsorata, Jiddah dake ƙoƙarin shigowa kam jakkar hannunta ta saki ƙasa sata hawaye da kallon su kalifa dake dariyarsu har yanzu.
“Lafiya kika tsaya nan?”.
Maganar Aliyu ta dawo da Jiddah hayyacinta, saurin duƙawa tayi ta ɗauki handbag ɗinta tana goge hawaye, taji daɗi da Aliyu baiji rashin tarbiyyar da ƙannen nasu ke zubama mahaifinsu ba.
Cikin murmushi ta ɗago ta kallesa, “Babu komaifa “Kalby, tuntuɓe nayi”.
Cikin raɗa dan kar ajisu saboda suna soro kuma gabda shiga cikin gidan, amma su Umma basa hangosu, itama taga su kalifa ne saboda window ɗin ɗakin da Hindu ke ciki yana saitin ƙofar sorone, “Kifa kula hajjaju ban gama amarciba”.
Gaba tai abinta tana murmushi, amma bata tankaba. Shima saiya biyota yana murmushin.
Ita tafara sallama ta shiga, kafin tace, “Tare suke”.
Tashi Umma tai ta saka hijjab, Walida tazo ta rungumeta tana murnar ganinta, dukda kuwa jiyama Jiddah tazo gidan.
Har Aliyu yayi gaisuwarsa yagama hajia hindu bata fitoba, kuma sarai tana jiyosa, hakama su kalifa Aliyu na shigowa sukabar jikin window ɗin suka koma ciki.
Jiddah bata zaunaba, tare suka koma da Aliyu, dama zasuje gaishe da Aunty Ruƙayyane datai mura, to hanyar gidn ta anguwarsu jiddah ne, shine Aliyu yace su biyo suga Abban, dan zuwa dare da wuya ya samu zuwa sunada majalisin dare na ƙarshen wata da akeyi a masalaccin ƙofar gidan malam.
Umma ta ɗakko magani a leda tanabama Jiddah. “Jiddah gashi idan kunje a jiƙa, maganin zakine Yaruwaiya nasa ta amsoma Maimunatu, jiya da Bunami zaizo yazo dashi, dan yanada ƙyau sosai, saura kuje kuƙi jiƙawa saboda ƴar banzar shiriritarku, kuna komawa gida dan ALLAH ki jiƙa matashi, ALLAH ya raba lafiya, ki gaidamin ita, ki kuma cemata tacigaba dashan farin zoɓonnan shima, gobe idan ALLAH ya kaimu Zarah zata kawo mata wani”.
“To Umma ALLAH ya saka da alkairi, yabama Abba lafiya”.
“Amin ku gaida gida”.
Aliyu dake jiyosu yay murmushi, shiyyasa yake ƙaunar Umma, baiwar ALLAHr tayi, akwai dattako, tunda cikin Maimuna ya tsufa bata gazaba wajen bata maganin zaƙi da duk wanda zai taimaketa ta haihu lafiya, yanda yasan zata iya taimakon ƴarta Jiddah ta cikinta haka takema Maimuna, har zuwa tai ta dubota sau biyu dayake Maimunan ta kwanta a asibiti har sau biyu, tundama cikin ya tsufa tace tabar zuwa duba Abba hakanan sai ALLAH ya sauketa lafiya, sanan duk wasu dabaru na mai ciki Umma faɗama Maimuna takeyi tamkar mahaifiyarta. Hakanne ya saka iyayen Maimuna suma jin daɗi, suka ƙara ɗaukar Jiddah da muhimmanci da janta a jikinsu, koda yaushe suna ƙoƙarin zuwa duba Abba, dan zuminci mai ƙarfi ya ƙullu.
Jiddah na fitowa Aliyu yay yunkurin rungumeta sai Walida ta fito dan musu rakkiya, hakanne ya sakashi matsawa baya yana susar gefen wuyansa da key ɗin mota.
Walida ta gimtse dariyarta dan ta fahimci abinda da za’ayi ganinta yasa aka fasa.
Sai da ta rakasu har mota. Aliyu ya kalleta bayan yama motar key, “Auta wai yaushe zaki dawo mana kwana ne? Daga zuwa sau ɗaya baki sakeba, ko gidanmu babu daɗi? Inama Zarah ban gantaba”.
“Yaya Zarah taje gidan aunty Nafisa ne”. Wlhy malam akwai daɗi sosai, hidimar gidace kawai kemana yawa, ga makaranta kuma, amma insha ALLAH weekend ɗinnan zanzo na sake muku kamar wancan, ALLAH yasama Aunty Maimuna ta haihu ina nan”.
Sheikh Aliyu yace, “Amin auta, ki gaida Zarah idan ta dawo, mu munyi hanyar ƙauyenmu”.
Jiddah ma ta amsa da amin.
Dariya Walida tayi tana ɗaga musu hannu har suka ɓacema gsninta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Cike yauma massalacin yake da jama’a, tsit kakeji babu wata hayaniya, sai sautin muryar Sheikh Aliyu data karaɗe micrephone ɗin massalacin, bayani yake dalla-dalla bisaga abinda ke rage kuzarin namiji da wanda ke ƙara masa ƙarfi.
“Waɗan nan abubuwan dazan lissafo suna taka rawar gani wajen ragema namiji ƙarfinsa ƙwarai da gaske, ga wasu kaɗan daga ciki, sun haɗa da. Hawan jini, Maleria, Ciwon ƙoda, Ciwon sanyi, Ciwon hanta, Wasa da azzakari da hannu, Shan lemon tsami, Sammu (sihiri), Aljanar dare, Ciwon Sukari, Basir, Rashin samun ishashan Hutu, Yawan Bacin Rai, Yunwa (Qaranci Cin Abinci ). Indai kana tare da waɗan nan matsalolin dolene kazama ka kasa gamsar da iyalinka, na lissafo kaɗanne a ciki dan akwai abubuwa da yawa baya waɗan nan ɗin. Saikuma waɗannan magungunan dana ɗan tsakuro muku, Shi maganin ƙarin kuzarin Namiji, ya bambanta ne daga wani mutumin zuwa wani. Misali maganin da wani yasha yaji daɗinsa, ba lallai ne kai idan kasha yayi maka aiki ba. Amma dai ga wasu abubuwan da zanyi bayaninsu anan, kuma mutane da dama sunce sunyi amfani dasu kuma sunji daɗi”.
*_“1 MAN HABBATUS SAUDA_* : Ka samu shayin Na’a-Na’a wanda aka sanya Na’a-Na’a ɗin sosai. Ka zuba masa Man Habbatus Sauda cokali 1, sannan kasha. Safe da dare kafin kwanciya. Ko kuma ka samu ƙwan Tantabara ko ƙwan Kazar gida guda biyu ko uku, Ka zuba garin habbatus Sauda cokali 1 a ciki. Agauraya a soyashi da Man Habbatus Sauda ko Zaitun, sannan kaci”.
*_“SAIWAR GINSENG_*: Wani itace ne ingantacce wanda ake kawoshi daga ƙasar China. Idan Namiji ya yawaita amfani dashi zai samu ƙarin Kuzari da girma”.
*_“KANKANA_* : Kankana tana kunshe da irin sinadarin dake cikin ƙwayoyin Viagra. Don haka tana ƙara ƙarfin Namiji sosai, kuma ƴaƴanta suna ƙara ma Namiji girma ba tare da wata illa ga jikinsa ba. Ka samu ƙatuwar Kankana ka yanka bayan Magriba ko Isha’i ka shanyeta gaba daya. Kuma ka riƙa taunewa ƙwallon. In sha ALLAH U zaka ji bambanci mai yawa”.
*_“RUWAN CITTA_*: Ka samu Madarar Peak ko Luna, ka tsiyaya ruwan chitta ko kuma garinta daidai misali. Sannan ka samu garin Kustul Hindi cokali guda ka zuba aciki, sannan ka sanya zuma daidai Misali ka shanye, Minti 30 kafin kwanciya”.
*_“MAN JIRJEER_* : Yawancin Maza masu fama da raunin Mazakuta, Basur ne ke damunsu ko kuma Majinar Kwankwaso (Waist). Shi Man Jirjeer yana ƙone irin wannan Majinar ne, har majinar ƙirji. Don haka yana ƙara ma Namiji ƙarfi. Waɗanda suke zaune a ƙasashen Larabawa kamar Saudia ko Misra zasu iya samun ganyensa cikin sauki. Domin shi suke sanyawa a saman abincinsu kamar yadda muke amfani da Lettuce anan”.
*_6 ZOGALE_* : Ɓawon jikin itacen Zogale idan aka shanyashi aka dakashi, ana hadawa da Madara ko Zuma ana sha. Shima yana Qara kuzarin Namiji sosai”.
“Abin lura anan, yawancin waɗannan Magungunan ba wai daga yin amfani dasu sau daya ko sau biyu zaka ga canji gaba daya ba. Dole sai ka juri amfani dasu yau da kullum kana hadawa da Motsa jiki, kuma ka rage amfani da abincin zamani waɗanda suke kunshe da sinadarai masu ƙarfi. Irin su Lemon kwalba, Biscuits, Chocolate, Alawa, Succarine, Farin Magi, etc. Ka koma amfani da kayan sha irin na gargajiya kamar irin su Kunun aya, Mazarkwaila, ƴaƴan itace irin su gwanda, ayaba, Lemo, Karas etc”.
“Sai kuma za’a iya asamun tafarnuwa cokali biyar 5, Kurtafalu cokali uku 3, Citta cokali biyu 2, Fijil cokali biyar 5, Zuma kwalba daya 1. Sai a haɗasu wuri ɗaya a cakuɗa su da zumar kullum asha cokali biyu a yini kawai insha Allahu za’a samu da cewa da izini ALLAH . ALLAH yasa mu dace”………..✍????
Zamu cigaba a page na gaba????????????
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*????????????????????????